Da sauri na duba wayar ina kokarin bude sakon wani video na gani wanda ya girgiza ni har na kasa zama sai da na dangana da tashi tsaya
Matata ta tambaye ni me ke faruwa na nuna mata videon sai da ta zubar da hawaye tana tambaya in mata bayanin abin da idanun ta ke gani amma nima ta kaina nake yi ban amsa ta ba
Ta rude ta birkice min sosai sai muka kara jin kira ina daukawa aka ce min

"Da fatan ka ga yadda muka yi wa ƴar ka??
Toh muddin ka yi kokarin tona mu koh kin yin abin da muka saka ka yi consider her dead and that u'v never had a girl child in ur life

Na girgiza da batun su saboda haka na ce musu na amince su gaya min duk abin da suke so zan musu

"Correct cewar mutumin da ya kira ni""

Suka ce min zamu hadu a private hospital di na by 11am

Haka na fita na bar gida na na nufi asibitin mata na na tambaya na meke faruwa amma haka na tsalake ka ta fita na bar ta tana kuka abin sai ya bani tausayi saboda na san damuwar da nake ciki kashi 30 ne a cikin dari da take ciki

  Na isa asibitin da mintuna 10 sai ga kira ta landline din asibitin wai an zo wuri na na ce a bar su su shigo

  Zama suka yi bayan sun shigo suka min kallon tsaf kafin su dora da ce min ga manufar su

Na kalle su na ce "in haukata ta sannan in kai ta mental asylum??"

Da eh suka amsa min akan koh in yi koh su halaka min ƴata hade da family di na kafin su bata min suna har a kwace min license di na na aiki

Yanda na dau abin ya fi karfin tunanina saboda basu da digon imani koh da na miskala zarratin

"Zabi ya rage nake koh kayi koh ka fuskanci matsala mai gida ba abin da baya yi akan abin da ya ke buri ciki kuwa har da shafe tarihin ahalin ka in ka amince ga yarinyar chan a mota

Zufa na goge na roke su akan su min rangwami amma haka suka min banza

Karshe dai amincewa nayi da kudirin su

Wasu nurses biyu na sa suka biyo ni hade da mutanin muka dauko ta muka shigo da ita cikin asibitin,, bayan mun ajiye ta suka nemi da kar in kuskura in bari wannan maganar ya fita saboda har yanzu ba wai sun bar ni bane

    "Yanzu ina iya ganin autata?
Nai musu wannan tambayar sai suka tuntsire min da dariya

"A ganin ka kai din mai wayo ne koh me?? ai sai mun ga yanda aikin zai kasance we are not fools dr""


Da haka suka tursasa ni har na yi mata wasu aluran saboda ko lokacin da suka kawo ta nayi observing din ta kuma na gano cewa sun mata inhaling wani abin,,

"I made her unconscious for 12hours suna ganin hakan suka yi kira a gaba na

" *DON*,, we are good can we release the girl?

Ko me suka ce mishi oho sai suka kashe kiran

"Dr karfe shabiyu daidai na dare ka iske mu a bakin asibitin ku zamu kawo maka ƴar ka in ka kara ko da second daya ne,, yayi wani irin smirk kafin ya dora da kewa consider her dead... Ka fahimce mu?

Na girgiza musu kai da "eh na fahimta"

Sai da suka tabbatar da sun tsorata ni sosai kafin su bar hospital din

   Zama nayi na gama dukkan tunani na na ga iya mafitar da zan samowa wannan yarinya shine in kawota wannan asibitin in dau short video clip in tura musu su gani bayan na mata allurar da zata fita hayyacin ta hakan ya kasance saboda bayan sun wuce nikuma sai na daukota a mota na nayi asibitin da ita though ban bi hanyoyin da ya kamata ba since am only trying to plan for something

A daidai lokacin da na shigo a sannan na ga zaki fita kuma ni ina jin nauyin yi miki magana lokacin da kika fito

   "Toh fah hakan ta kasance hajiya bayan na shigo da ita na mata allurar na dau videon na yi savig"

  Bayan na kai gida nayiwa hajiya Hadiza bayanin kokomai ta tsorata wanda hakan ya sa ta bani wata shawara aka why not bayan na karbo khadi'atu daga hannu su mu bar kasar temporary har bayan komai ya lafa sai mu dawo""

Ban bata amsa ba nace zan yi tunani toh fah na kashe kusan daren ina tunanin mafita saboda ni gaskiya bana jin barin yarinyar nan a nan kuma idan ma bari suka sani tsaff zasu iya hallaka ta domi basu da alamun imani

11:40pm ya min a bakin asibitin 12am suka iso suka fito hade da hankado min ƴata waje a hujjajan ta zo ta rungume ni taba kuka nima ina tayata kada min warning Suka yi wanda nasan me suke nufi da hakan suka wuce

Da ɓari na ja motata na bar wurin muka iso gida a lokacin hajiya Hadiza ta kuma nanata min maganar da ta min dazu amma nace mata kar ta damu wani abin nake son karasawa
Da haka muka kwanta

A washe gari na kuma daukar video clip din na yi saving bayan kamar wasu lokuta na tura musu da na jiyan da na dauka suka min replying da "nice job dr""

Chan yamma na kuma tura musu wani suka gani haka shima suka yimin replying

Toh a kullum abin da nake yi kenan su kuma duk tsammanin su a mental asylum take not knowing tana nan ne

"Kin ji dalilin da yasa nace miki kar mu kai maganar zuwa higher authority kenan saboda ban gama shirye-shiryen da nake son yi ba again ganin sunnan yarinyar sai da yasa na ji wani irin tsoro ya kama ni coz in ban manta ba sunnan wani family name ne na wani shahararen architecture da ya rasu shekaru da dama amma ban san relationship dake tsakanin ta da shi ba seeing this made me more scared gashi tana da danyen jinjirin ciki just 2months shi yasa na kara neman yanda zan taimake ta batare da sun sani ba kuma ba tare da an yi involving family di na ba amma har yanzu na rasa yanda zan yi na kasa samo mafita""

  A nan ya dasa aya nikuma na numfasa saboda na kidime iya kidimuwa ƴata

Wani shawara na bashi......




  _Ko menene wannan shawaran readers oho amma domin jin shawaran zaku iya biyo ni sannu a hankali har zuwa next page din wannan littafi coz am also eager to know the advice_

_*🍒s, ibraheem🍒*_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now