Ta dago ta kalle ni tace min "kin san menene wai diagnosis din ta""?

Na girgiza kai na
"Hmmmm wai Obsessive compulsive neurosis +long time history of Munchausen syndrome and type 2 bipolar disorder

Na kalle ta nace toh wai duk ita kadai sai nake ganin kamar fah lafiyar ta kalau

Kallo na tayi tace min "

""eh lafiyar ta kalau aka kawo ta bayan an dai kawota din ne aka fara juya mata tunanin ta"

Na ce toh su wadannan disorders din da aka ce tana da su menene su?

Gyara zamanta tayi ta ce
   _*"Obsessive compulsive neurosis is a mental disorder in wic an individual present with different symptoms of intrinsic thoughts which are caused by drugs and a purposeless act performed by an individual at a particular tym in wic if not performed can cause aggression and tantrum, and these include excessive thought about contamination, need to have a particular thing at a particular time the desire to have,repeated doubt about something, euphoria and sexual imagery*_

  Akwai wasu abubuwa dayawa amma wadannan sun ishe ki

Shi kuma
_*munchausen syndrome  is a disorder that occurs as a result of illness or psychological trauma in order to draw attention, sympathy or reassurance This disorder result to prolonged hospitalization and unnecessary operation*_

Sai kuma _*type 2 bipolar disorder which is a mental disorder in which an individual experience mood swings with an intervening period of normalcy from depression to extreme euphoria and it is accompanied by delusion or hallucination*_ (zaku iya nema na domin neman karin bayani in kuna so akan mental disorders din da nayi summarizing briefly)

Hmmmm ma'am ina jin ki

Ta cigaba da cewa
""Koh bayan da na karanta wadannan history din and her diagnosis nasan karya ne duba da irin social history dinta hade da age din ta da kuma sunnan familyn da ta fito''

  Ban yarda ba amma na tsaya jiran Dr Ladan ya zo ya min bayani

  Bayan kamar 1hour da zuwa na sai gashi ya shigo ya dudubata ya zo yana tambayar inda folder din ta yake aka ce mishi yana tare da metron
  Amsawa yayi ya shigo office din
  Bayan gaisuwa da wasa da dariyar da muka saba yi sai yayi shiru yana kallo na wearing a serious face

Ya ce min "Hajiya Rukayya my family is under a serious watch "

Nace mai watch?  kamar ya?
 
Ya furzar da iska yace min
"Wannan yarinya da na kawo ta nan a jiya mental asylum aka ce in kai ta in ba haka ba i and my family won't be spear out

A matukar razane na dago ina kallon shi na ce "Dr ka fa saka ni a cikin duhu kana min magana a shagube ban fahimta ba"

Sai da ya tabbatar da cewa babu wanda zai iya jin mu sannan ya kara rage murya ya fara magana kamar haka

"Tun watan da ya wuce ake bibiyata ni da iyalaina harta da auta ta da ke qabul a kasar Afghanistan ana mata barazana akan rayuwar ta,,, kullum sai an turo min sakonnin tsoratarwa da ban mamaki kuma aka hana ni kai kara zuwaga jami'an tsaro acewar su yin hakan daidai yake da halake min autata kasancewar ta ita kadai ce mace da Allah ya bani duk son duniya na dora shi a kan ta ne"
Ya numfasa ya cigaba
"Na yi kokarin sanin me suke bukata in yi musu saboda su rabu da ni ni duk a tunani na ma koh wasu ne masu patient a nan ke neman a sako musu koh kuma a yi transferring ashe ba haka abin yake  ba
Ce min suka yi kar in damu lokaci ya kusa da zasu fito min da manufar su

Tun daga lokacin na sami salama har sai ranar da abin ya faru wato 19/12/2018
Ya dan dakata yana jan numfashi kafin ya cigaba da cewa
 
  "Muna breakfast ni da iyalai na sai na ji karan sako ya shigo wayana a lokacin sai ban duba ba har kusan 1hour sai na ji kira ina dagawa aka ce min "doctor halan baka ga salon mu bane"?
Nace a'a sai suka min dariya suka kashe

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒जहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें