Na yi wa kaina wannan tambayar

      Na rasa mai bani amsa daidai lokacin da zuciyata tayi na'am da amsar da kwakwalwata ta bata a lokacin ne kuma wannan matashiyar ta kuma birkicewa birkicewar da tun da na iso ban ga ta yi shi ba

Zuwa nayi nurses station din a hanzarce ina nuna musu gadon

Mikewa suka yi wanda yayi daidai da fitowar metron daga ofishin ta tana share kwalar da ke kan fuskar ta

"" nurse Ahmad get me my phone

Da sauri ta dauko mata wayar ta mika mata

  Kira tayi tana sauke ajiyar zuciya tana kokarin saisaita numfashin ta

""Baballe this is metron Zayyad,,ina buƙatar private vehicle din asibiti ne in the next 5minutes and be fast about it pls

   Dif ta kashe wayar tana mai kallon ta tareda Cewa

"it's all gonna get over dear hmm am so sorry for the delay i will protect u at any cost

    Few minutes sai ga baballe da private vehicle din asibitin yana kokarin kashewa

Juyawa nayi na kalli metron din nace mata

"Ma pls where are u taking her to i haven't source the information i came here for yet "

Ta min murmushi ta ce

""kar ki damu tare zamu tafi da ke saboda na dade ina neman wanda zai fallasa wannan muguwar makarkashiyar da aka dade da binne ta ko kowa ma ya huta'""

  Kallon ta nayi na ce ""but ma'am from all indication kamar kina nema ki taka dokar asibitin ne ai by getting the patient out of the hospital without the awareness and permission of the hospital management"

  Mursmusawa tayi ta kalle ni na dan wasu dakiku tace min

"No this isn't a patient"

tana mai girgiza min kai, ta cigaba da cewa 

"this is a mentally fit lady,she is not mentally unstable yanayin rayuwa ne ya mayar da ita haka"

Daga nan bata kara cewa komai ba ta juya zuwa offishin ta tana mai kiran nurse Ahmad
Ban san me suka tattauna akai ba amma naga yanayin nurse Ahmad ya canza sosai

Few minutes sai ga metron ta fito daga office din ta sanye da doguwar riga mai kalar ruwar bula

Ce ma baballe tayi ya kirawo wadannan hefty men din da suka danne patient din nan dazu su zo su rike mata ita

Suna zuwa suka daddane ta metron ta tsikara mata alura tana gamawa sai ta yi luu bacci yayi awon gaba da ita

  Daukan ta akayi aka saka a motar a inda metron ta fito da jakar ta ta shige motar bayan ta bani izinin shiga motar nima tana mai nanatawa nurse Ahmad cewa kar ta manta da maganar su

    Toh dama tun da ta fara birkicewa sauran nurses da students din suka matso kusa amma suka kasa tabuka komai saboda sun fara tsorata da yanayin ta

Toh koh da nurse Ahmad ta fito daga office din metron sai ta musu bayanin komai suma sai jikin su yayi sanyi kalau har lokacin da metron suka bar asibitin

  Muna kan tafiya a titin tayi kira tare da cewa

"'Islam ka same ni a daidai roundabout din ostrich da motar""
  Sai ta kashe wayar

  Ni dai wannan abin na daure min kai toh wai me hakan ke nufi ne ban da mai bani amsa haka dai nayi gum da bakina

Mun iso daidai roundabout din kenan muka hango wani dan saurayi yana matsowa kusa da mu
Dakatawa baballe yayi yana gyara parking din shi

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now