Auran ba shiri

419 14 0
                                    

Don't forget to vote read comment
GODIYA ta musaman ga mahaifiya ta Hajiya Mariya Sada da mahaifina Alhaji Sani Sa'idu Bindawa my siblings Sister Rukyy Farida hafsy
And class 2014

Yarinya ce yar kimanin shekara goma dan dauriya a duniya. zaune take acikin kasuwa tana saida yar zururu  taliyar Hausa ta manja da yaji yasha farin magani, Yara mata da Maza sun zagaye ta suna siya, suna ci suna sharar majina hanci Sai tsiyaya yake faman yi.  Ba laifi wanna satin kasuwar tayi dadi sosai yar yarinyar Sai murna take yi. 
Bayan sallar magariba ne na hangi yar diyar tana hada kwanin kan tana son shiga cikin kasuwa siyan goro Wanda zata Kai ma kakar ta "Iya salmai" tsarabar kasuwa don wanna Al'adar tace duk kasuwa Sai tayi tsarabar kasuwa ko ba yawa.

Laure dai yarinya ce yar kimanin shekara goma da yan watan ni wacce yanzu ta gama makarantar primary anan charanchi dangin mahaifin ta sunyi uwa sunyi makarbiya Sai sun mata aure.
Laure irin yaranan ne masu son karatu tana da tsafta duk da halin babu da suke ciki yarinya ce wacce gaba daya ta tashi acikin hali na rashin gata babu Wanda ya damu da rayuwar su ita da kakar ta "Iya salmai " sun ci abinci basu ci ba ko Oho.
Laure bata kula samarin karkarar su "Iya salmai" tayi ta mata tsiya wai tsoron samari takeyi. Ita dai ko ajikin ta, ita burin ta aduniya tayi karatu tazama mallamar makaranta! Ta dunga siyan ma "Iya Salmai" kayan dadi  idan "Iya" bata da lahia ta Kaita asibiti birni .  Shine babban Burina Amma kash ga dukkan alamu bazai cika ba tunda magajin Mahaifi na Alhaji Lado yazo wajan "Iya" akan aurar dani zaiyi nan da mako daya.
  "Alhaji Lado " Wan Mahaifin na ne shi irin mutanan ne masu son abun duniya ga dadin baki Alhaji Lado yayi tunanin ba Mallm Sule auran Laure ba don komi ba Sai don Alkawarin da yamishi nace wa zai bashi kyautar Gona ta yamma da gari katuwar gona ce gari guda! jin haka yasa Alhaji Lado amincewa.shi ko Mallm Sule dadin duniya ya rufe shi jin za'a bashi yarinya Danya sharaf .
Shine dai Mallm Sule Dan caaca ne  kuma Dan kasuwa ne Yana cin kasuwanin kusa dasu irin su dankama, jibiya, Mai Adu'Wa, Batsari, Mashi da nan charachi.
Mallm Sule Yana da matan aure hudu Zulai, Barira, Mero,  kubra
Kubra duk tafi su Zafi ,Allah yayi ma zulai rasuwa Uwargidan Mallm Sule, wata Mai kamawa ne shekarar Zulai shida da rasuwa. Allah sarki zulai mace mai hakuri auran saurayi da budurwa sukayi  da Mallm

BAKIN WUTAWhere stories live. Discover now