KASHI NA FARKO

426 22 1
                                    

Hassanaah Zakariyya Maidaru(Sanaah)
Fikhra Writers Association

KASHI NA FARKO

Gudu ta ke tun karfinta tana neman taimakon mutane muryarta ta dashe babu mai jin me take cewa, babu mai taimaka mata,  ta rasa wanda zai kawo mata d'auki.

Ta shiga daji cikin gudun ceton rai.
Ganin ba ta samu mai ceto ba karfinta ya kare kuma matar bata daina binta da wuqa a zare ba, ta fadi kasa cikin karaya tana daga hannu sama da alamun rokon Allah ta ke muryarta ta fita.
Matar mai rufafiyar fuska ta d'aga wukar dai-dai kirjinta da nufin da'ba mata ita kuma tana ja da baya daga kwancen, wani mutum ta gani kamar an cefo shi ya hankad'e matar ta fad'i ya sa hannu zai riko hannunta...

"Deejah! Deejah!! wannan wanne irin barci ne haka ki ke yi? Kin manta a aji ki ke?"

Firgigit Deejah ta tashi kwance ta ke kan banci ta dubi wadda ta ke tashinta, ta sa hannu ta goge gumin fuskarta tana ji wani yana tsiyaya a jikinta.

Ta yi karamin tsaki "Maganin mura na sha ganshi ban samu barcin kirki ba a dare karfe hudu kuma na tashi ban koma ba, shi yasa kai na ke ciwo barci yana fusgata, an dawo break ne?"

"Yanzun nan aka kada dawowa, Deejah ba ki daina tashin karfe hudun nan ba kin ga yanzu sanyi ya zo, mura ba za ta barki ba"

Deejah ta yi murmushi ta dafa kafad'arta "Nima ba haka na so ba Naana, dole na tashi, ranar da na makara ruwa zai tasheni, ina yiwa Baaba Hansatu wankin wake, da ni nake kai ni'ka sai da Abba ya dage akai na daina kai niqa amma kullum zan wanke wake, Sannan na share gida na dora dumame"

Naana ta kalleta cikin tausayawa ta ce "Ina tausayawa rayuwarki Deejah! Ji nake kamar ki dawo gidanmu da zama wallahi har zuciyata nake jinki"

Deejah ta yi murmushi "Nima ina jinki sosai a raina, mu bar maganar nan haka dan Allah, kin yi note din malam Izzu?"

"Na yi amma ba duka ba, gajiya na yi kin san shi da zuba note"

"Za ki ban na je gida sai na kwafe" Inji Deejah

Malamine ya shigo suka kowacce ta d'auko littafinta daga jaka.

  "Malam dan Allah inje na aro Biro?" Inji wata yarinya.

"Kun san dokata ai muddin na shigo babu wadda za ta fita kowanne excuse ne da ita" Malam ya ce yana gizago.

"Ga Biro Hassana"
Ta taso ta karba "Na gode Deejah" Hassana ta ce ta koma kujerarta ta zauna.

Naana kallonta kawai ta ke sai da ta ga malam ya fara rubutu ta yi 'kasa da murya ta ce "Ke da wanne za ki yi aiki to?"

Deejah sarkin murmushi ta zira hannu a Jakarta ta dauko wani tsohon Biro ta daga ta nuna mata tana d'aga mata gira.

  "Ke kam kullum ba kya rabo da extra pen, to ai da tsohon kika bayar"

  "Wai su waye suke min surutu ne? Wallahi I will send you out"

Naana ta rufe bakinta da hannu tana harar keyar malam, Deejah ta na mata dariya.

Yau ma kamar kullum da yunwa Deejah ta koma gida ga rana a gajiye ta shiga gida.

  Ba kowa a tsakar gidan kai tsaye dakinsu ta nufa, ta rataye hijabinta a kan kyaure ta fito ta dauki buta za ta shiga bayi.

Tsawa Habiba ta daka mata wadda ta sa Dijah jefar da butar hannunta ta ja da baya.

"Uban wa ya sa ki daukar min buta Dijah? Lallai yau za ki ci na jaki"

   "Dan Allah Umma ki yi hakuri ina sauri ne ban san butarki na d'auka ba, ki yafe min" Ta fara hawaye.

   Habiba ta nufo ta "Ni ba ummanki ba ce ki je can kin nemi Umma ko ki tono taki a kabari, shegiya mayya kawai" ta janyota ta duma mata dundu ta jefata cikin ruwan da yake taruwa a kofar band'iki.

GIDAN BUNUWhere stories live. Discover now