Duk sun yi na'am da maganarsa don haka gabaɗaya suka ɗauki mota don zuwa gidan motoci uku suka nufi gidan Aneesa rungume da Miemie kamar wani ya ce zai raba su.

Can ɓangaren kuwa ba su tashi farga babu Miemie ba sai da suka ga ta yi kusan awa bata shigo ba, nan fa hankalinsu ya tashi duk gidan an duba babu Miemie sun tambayi maigadi ya ce babu wanda ya shigo, domin Najeeb ya ba shi kuɗi masu yawa ya ce kar ya faɗawa Alhaji Mansur ya shigo, ai ko ya ce babu wanda ya shigo, ya sanya su mugu su ɗaure shi ke nan aka fara horn, da sauri ya je ya buɗe don a tunaninsa Najeeb ne ya dawo, su mugu sun yi tunanin 'yan sanda ne don haka da gudu suka ɓuya. Mamaki matuƙa ya kama su gabaɗaya, Alhaji Taheer cikin fara'a ya fito yana faɗin "A'a Alhaji har kun riga mu isowa ke nan? Lallai na yarda da soyayyar ka a gare ni." Ya ƙara maganar cikin jin daɗi.
Daburcewa Alhaji Mansur ya yi zai fara kame-kame Najeeb ya yi saurin cewa

"Ina mai baƙincikin sanar maku da mahaifina Alhaji Mansur ya sanya a ɗauke Miemie domin kwaɗayin abin duniya." Doguwar Salati jama'ar wajen suka ɗauka "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un."
"Kai Najeeb bana son shashanci yanzu ka rasa wanda za ka yi wa sharri sai mahaifinka?? Wannan wacce irin rayuwa ce Allah Ya kawo mu da 'ya'ya basa ƙaunar iyayensu? ABBA ya yi maganar cikin tashin hankali.
"Sam Alhaji a zamanin yanzu kafin ka samu yaro mai biyayya wa iyayensa kamar Najeeb da wahala wallahi duk abin da ya faɗa maka gaskiya ne, wannan kaɗan kenan daga cikin halin Mansur inda har baka ji tsoro ba wallahi shi ya sanya wasu marasa imani suka bige Ameesha lokacin da ta samu wannan lalurar." Wannan karon har kusan faɗuwa Abba ya yi don firgici, mutumin da ka yarda da shi, shi ke ha'intar ka? Lallai mutum ba abin yarda ba ne, kallon Alhaji Mansur ya yi wanda ya yi tsiru-tsiru kunyar duniya ta rufe shi bai taɓa tunanin yana da kunya irin ta yau ba, ji ya yi uwa kasa ta nitse ya faɗa ciki ko ya huta da kunya da nadama, yau kaɗai na ya ji ya tsani irin halinsa.

"Babu komai Alhaji duk abin da ka yi ka yi wa kanka, Allah Ya sani da zuciya ɗaya na ɗaukeka amma tun da haka ne babu komai, har cikin zuciyata na yafe ma duk abin da ka yi mini, kuma ina roƙonku da ku yafe masa kun ji?
"Tun da nake da zuciya ɗaya nake abota da shi, don haka na yafe masa kuma na san duk wanda na isa da shi ma ya yafe wannan magana, amma abin da zan iya faɗa masa shi ne daga yau babu ni babu kai, kuma kar ka yarda wani abu ya kuma haɗa mu, ba dai a kan kuɗi ka yi haka ba? To ka sha.kuruminka kai Jaheed ɗauko jakar kuɗin nan ka bashi miliyan biyar a ciki." Cikin sauri Jaheed ya cika umurnin Abba nusiha sosai Abba ya yi wa Najeeb wanda ya sanyaya masa jiki sannan suka juya, su ma su Najeeb motarsu suka shiga sai dai ya kasa jan motar sai Rufaida ta ja.

Su Abba na fita su mugu suka fito, Alhaji Mansur har zai fara kaso suka kwace kuɗin babu tausayi babu tsoro yana kallo suka wuce da shi, kuka sosai ya yi ya rasa aboki mai taimakonsa sannan kuɗin da aka ba shi sun kwace wayyo tarin nadama da dana sani suka masa yawa take kansa ya fara wani irin sarawa. Da ƙyar ya iya jan motarsa zuwa gida, kwana biyu ciwo ya kwantar da shi, da ƙyar da lallashi Mummy ta samu Najeeb ya kai shi asbiti. Gwajin farko aka ce ciwon zuciya da hawan jini wanda suka masa mummunan kama, domin zuciyarsa kumbura ta yi haka jikinsa ya fara kumburi.

Allah Ka bamu ikon aikata kyakkyawa, ba irin halin Alhaji Mansur ba na zallar cin amana da baƙin ciki tare da hassada, ga dai yadda ya kare nan.

Ɓangaren su Ameesha ma AlhamduLillah komai ya wuce, ta ci gaba da shayar da su Hibban da Hibba yara masu kyau da wayau sun yi tula-tula gwanin sha'awa

BAYAN SHEKARA GOMA
AlhamduLillah! Gidan Dr arziki ya ci uban na da don yanzu ya zama katafaren mai kuɗi ƙaton gida ya gina masu, haka ya mallaki asbitoci har uku wanda ya sanya masu suna A'A specal hospital (Asmad Abubakar) duk a cikin garin Kano, duk inda ka zaga maganarsa ake Dr Asmad, ya yi suna fiye da tunani, yanzu yaransa biyar duk da su twins
Fatimah (Miemie), sai su Hibban da Hibba, sai mai sunan Meena wacce suke kira (Besty) sai yanzu da take goyon mai sunan Bobbo suna masa laƙabi da (Aryan) gabaɗaya yaran 'yan gata ta kowanne fanni ga tarbiyya da nutsuwa.

Miemie da Sahal yaron Meena suka shigo cikin falon bakinsu ɗauke da sallama, Ameesha da ke zaune ita da Dr tana shayar da Aryan ta amsa "Mami Daddy sannunku da hutawa." Suka haɗa baki wajen faɗa. "Yawwa Abbana da Nennena an dawo daga school ɗin?" Da yake school ɗaya suke da Sahal yau sai ya biyo direban Miemie wai zai gaida Ameesha "Eh Daddy Mommana bata da lafiya tana can sai juyi take yi." Miemie ta gama maganar tana hawaye. Kusan a tare suka tashi Ameesha saɓe da Aryan falon Aneesa suka shiga inda suka sameta kwance kamar yadda Miemie ta faɗa, da sauri Dr ya matsa kusa da Aneesa yana faɗin "Sannu Aneesa me yake damunki?"
"Cikina." Ta yi maganar da ƙyar. Cikin tausayi Ameesha ke mata sannu, shi kuma Dr ya ɗauko kayan aiki gwaje-gwaje ya soma mata cikin ƙwarewa, Yana gamawa ya saki murmushi ya ce "Ma Sha Allah! Miemie kin kusa yin ƙani Momma na da cikin wata biyu da kwanaki." Tsalle Miemie ta soma na jin daɗi, ita ma Meesha farinciki ne ya kamata har da hawaye ta riƙa godiya ga Allah, ya yin da Aneesa idonta ke fitar da hawaye duk na farinciki." Sai ku bar kuka shi yasa tun tuni ban faɗa maku ba gashi yanzu ya nuna da kansa a bar kuka a yi murna Allah Ya inganta. Aiko murna sosai suka yi daga lokacin Aneesa ta daina aikin komai sai da ta huta tattali da kula Dr na yi mata daidai gorgodo har Allah ya sauketa lafiya in da ta haifi santaleliyar budurwa mai kama da Dr kar kuso kuga farincikin da family ɗin Dr suka shiga, ranar suna yarinya ta ci sunan Maryerm Aneesa da kanta ta zaɓi sunan da aka sanyawa 'yarta suna kiranta da *(IFTIHAL)*.

DUK WANDA YA GA ZURI'AR DR ASMAD SAI SUN BURGESHI, DOMIN MATAN BIYU SUN HADA KAN YA'YANSU BAKA TAƁA CEWA YA'YAN KISHIYOYI NE, DON TUNI IFTIHAL TA KOMA ƁANGAREN AMEESHA, FARINCIKI KE WANZUWA A KOWACCE RANA A GIDAN DR ASMAD. To muma sai mu ce Allah Ya bamu farinciki da kwanciyar hankali.

TAMMAT ALHAMDULILLAH

Anan na kawo ƙarshen wannan littafi mai suna SANGARTA, Alhairin dake ciki Allah Ya sadamu da shi kuskuren da ke ciki Allah Ya yafe mana.

Godiya gare ku masoya abin tunkaho abin alfahari, Allah Ya barmu da ku har gaban abada Amin.🤩🤩

Tukuici ga my Besty Khadija S Muhammad, bana gajiya da yabon ki wallahi, domin karamcinki a gare ni ba ya faduwa sai dai na ce Allah Ya biya buƙatu na Alhairi.😘

SAI MUN HAƊU A WANI

*Ni ce ta ku har kullum*
*ZULAYHEART HARUNA RANO*
*ZULAYHEART RANO*
*UWAR FAWZAN*💞

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 31, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now