Lokacin da Dr ya ya dawo Ameesha tana toilet, ido ya daura akan gadon ya ci karo da jarirai har biyu kwance akan gadon, matsawa ya yi fuska ɗauke da mamakin yadda Ameesha har ta haihu bai sani ba, karan buɗe kofar da ya ji ya sanya ya juya wayam ya ga cikinta baki buɗe yake kallonta, ita kam murmushi kawai take aika mas, doguwar a jiyar zuciya ya sauke yana faɗin "Cutie haihuwa kika yi shi ne ko ki sanar min in tari baby's ɗina da kaina?" "Sorry baby bayan fitarka babu jimawa sai nakuda, ni na hana Aneesa kiranka don can dinma aiki ka ke yi, kuma ka ga da sauki sosai tun da na sauka lafiya." "Madallah amma ban so yarana suka fito duniya bana kusa ba." Ya dire maganar yana isa bakin gadon. "Ai k'anwar ka ta amsheka domin ta yi aiki sosai Allah ya saka mata da Alhairi." "Amin.*" Dr ya amsa sosai ya cika da farin ciki kamar wannan ne karon farko da aka taba masa haihuwa, daukar yaran ya yi cikin zallar soyayyar su da kaunarsu, sai kiss yake masu take yama yaransa huduba da sunan Ummi da Abba.

Wannan abu ya yi wa Ameesha daɗi, mutane sai tururuwar zuwa barka suke har ranar suna, an yi lafiya an gama lafiya, yara suna amsa HIBBAN DA HIBBA, Ameesha zaune tana shayar da Hibba ya yin da Hibban ke kwance Miemie ta shigo da gudu ta k'arasa bakin gadon tare da kaima Hibban raruma a dole daukarsa za ta yi, da sauri Ameesha ta janye Hibban ɗin tare da kaima Miemie duka ba na wasa ba. Kuka ta saki aiko cikin sauri Aneesa ta shigo tana faɗin "Subhanallah Miemie me ya faru? Yar'uwa me ya sameta?" Harara Ameesha ta banka masu ta ce "Allah Yar'uwa ki faɗawa yarki ta kiyayi min yara yanzu fa Babana yana kwance shi ne ta zo zata daukar min shi bige mata hannu na yi."

"Sorry yarinyata kin ji rabu da Mami kawai don zata ɗauki Hibban mu tafi unguwa shi ne ki ta dokeki? Babu komai in kika kwantar da hankalin ki yanzu zamu bar maki gidan kuma ba bu inda zamu da Hibban ɗin." Ta karasa maganar tana daukar Miemie. "Hhh! Ku gaida su duk inda ku ka je za ku dawo ku samemu, Allah wannan yarinyar taki tana fama da sangarta." "Hmm! Yar'uwa yanzu duk SANGARTAR Miemie ta kai ki?" "Ta ma fini ki tambayi Ummi ki ji." "Umm ki faɗawa wasu amma mukam mun sa ni don haka sai mun dawo." "A dawo lafiya." Ameesha ta faɗa tana kwantar da Hibban ɗin.

Fitar su Aneesa gidan Nenne suka fara zuwa sun daɗe a can bayan la'asar suka fita dan zuwa gida, suna cikin mota Miemie ta ce "Mommana ice-cream." "Ok mu je gida akwai." "A'a Mommana ni dai ice-cream ki ciya min yanju." "Kai Miemie kin fiye rigima mu je." Kwana ta yi ta shiga wani super market ice-cream din ta saya mata robobi biyar sannan suka nufi wajen biyan kudi Aneesa tana biyan kudin Miemie ta fice ba tare da ta sa ni ba, ta gama biyan kudin ta duba bata ga yarinya ba cikin sauri ta fita wajen mota, sai dai me babu Miemie take hankalinta ya tashi ta koma ciki tana sanar da ma'aikatan wajen ba taga yarinya ba, su ma nan suka fara duba wa amma duban duniya babu Miemie babu alamar ta, tuni Aneesa ta barke da sabon kuka dama tuni ta fara, zaman dir shan ta yi a wajen ita sai an nemo mata yarta, duk lallashin da suka mata ta ki yadda.

Da kyar ta yadda ta nufi tafiya wanda sam ta kasa yin direban da kanta ga uban jiri idonta ya kumbura sun tun saboda kuka har bata iya buɗe su, babban tunaninta ta yadda zata tun kari Ameesha da Dr ita kuwa mai zata ce masu, sai sabon kuka a haka suka isa gidan da kyar ta shiga bangaren Ameesha hawaye na shatata, Ameesha tana jijjiga Hibba ta koma bacci sai ganin Aneesa ta yi sosai hankalinta ya tashi musamman yadda idonta suka koma, da sauri ta kwantar da Hibba ta nufi wajen Aneesa tana tambayarta menene.

"Yar'uwa Miemie! Miemie Yar'uwa." Shi ne kawai abin da take faɗa. " Miemie! Me ya sameta?" Wasu sabbin hawaye suka zubo daga idonta ta ce "a wajen sayan ice-cream ban ganta ba." "Baki ganta ba? Miemie ɗin?" A dan firgice ta yi maganar. " Eh, ta faɗa murya a dashe, Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un shi ne kalmar da Ameesha ke maimaitawa har ta ɗan samu nutsuwa waya ta dauko ta soma kiran layin Dr lokacin har ya shigo cikin gida, ɗauka ya yi ya ce "To gani nan har za a fara min waya." Cikin dariya ya gama maganar. Ba iya cewa komai ba sai kashe wayar ta yi har ya isa shigowa.

"What! Dr ya fada da ya gama jin labarin da Ameesha ke ba shi tashin hankali sosai Dr ya shiga da jin ba a ga Miemie ba, a fusace ya nufi Aneesa tare da shako wuyarta tare da sakar mata wasu lafiyayyun maruka biyu wanda suka yi sanadin daukewar numfashin ta ya daura da faɗin "wallahi matuk'ar baki nemo min yarinya ba duk abin da na yi maki ke kika ja, tun farko irin haka na guda amma Ameesha kika na ce sai an bata dama mata da ba imani ne da ita ba ta ya zata iya kula da yar wata, da kanki Ameesha kika zubar min da ciki sannan kika ci gaba da shan magunguna har kika yi wa kanki illa, wannan ba matsala ba ce domin ko yanzu Allah ya nuna maki ishara ni, ki fito min da yarinya tun ban yi maki lahani ba."

Da kyar Ameesha ta samu Dr ya saki Aneesa sai huci yake, Aneesa kam sam shakan da Dr ya yi mata bai dameta ba sai ciwon rashin Miemie, tana zaune a wajen hatta motsi kasawa ta yi sai kallinsu ita kadai ta san halin da take ciki, cikin lokaci kadan har maganar batan Miemie ya karede jama'a, Abba tuni ya kai sanarwa gidajen rediyo da talabijin har cikin jaridu, Dr kam sam ya rasa nutsuwa duk cikin su Ameesha ce kawai mai dauriya amma Aneesa kam bata da aiki sai kuka da sambatu, bata taɓa damuwa da bakaken maganganun Dr ba bata da wani buri sai na ganin Miemie kusa da ita, har aka kwana shiru babu labari. Nan fa hankula ya kara tashi aka duk'ufa addu'oi.

****
"Hahaha." Dariya Alhaji Mansur kenan lokacin da su mugu suka kawo masa Miemie, kallon yarinyar ya yi ya ce "tabbas wannan jinin Alhaji Taheer ne, don haka da ita zan yi amfani wajen cimma burina." "Kai Alhajina gaskiya kasan kan tsiya yanzu wannan yar yarinyar ka sanya aka dauko maka na san dole hankalinsu ya tashi, kuma ko nawa ake bukata za su kawo." "Sosai kuwa ai na yi bincike ne akan son da suke mata, kuma idan muka dauko Alhaji Taheer akwai matsala amma kaga wannan bata sammu ba mu dinma bamu santa ba. "Ka yi farar dabara" tafawa suka yi cikin jin dadi.

Number din Alhaji Taheer ya ba mugu ya ce maza ya kira shi ya faɗa masa ga jikarsa sun kama sai ya bada miliyan ashirin za su bada ita "yau kwanan ta nawa ma." "Eh Alheji kwanan ta uku, gaskiya a yi ayi domin gaba daya ta damemu da sangarta kuma ka ce mu rika bata komai, haka jiya ta ishemu da surutun tsiya sai da bobo ya kai ma bakinta duka." "Du me? Waye ya baku izinin duka? To kar ku kara." "An gama oga." Ya fadi maganar yana dan nawa Alhaji Taheer kira.

Lokacin yana zaune a cikin gida abin duniya ya dameshi sam ya rasa tunani daya sai jin kar'ar wayarsa ya yi, da sauri ya dauka ganin sabuwar Number Yana Addu'a Allah yasa sun ga Miemie ne, maganar da ya ji ya firgita shi amma cikin dakiya ya ce "Ku fadi in da za a kawo kuɗin nan da awa daya zan turo amma don Allah karku yi mata komai." Faɗa masa suka yi kafin ya yi wata maganar har sun katse layin. Dr ya kira yana faɗa masa yadda suka ce "Abba karka yi saurin tura masa kuɗin nan fa ka bari a yi bincike." "A'a zan tura Asmad zan iya kashe ko nawa in dai Fatima zata fito mu ci gaba da addu'a." Cikin kankanin lokaci har su Nenne da Bobbo sun isa gidan Asmad su Ummi da Abba ma haka har da Meena.

Kudi Alhaji Mansur ya mika ma su mugu ya sayo masu abin sha, aiko ya sayo har da kayan maye sun sha sun yi ta tutul, Miemie sai wasa take yi abin ta bata damu ba da ta gaji da zaman falon ta fita, suna kallonta don sun san babu mai shigowa gidan tunda akwai mai gadi kuma ba zai barta ta fita ba, kuma ma dai ai Miemie bata da wayan da zata gudu fitarta ya yi daidai da zuwan Najeeb tare da Littel Ameesha sun zo gaida Abbansa domin kwana uku kenan yana zuwa gidan baya samunsa shi ne ya yake shawarar zuwa nan gidan domin duba shi, ido hudu suka yi da Miemie duk da bai taɓa ganin yarinyar ba sai jiya a Arewa 24 ana cigiyar sa sunanta makale da sunan Dr Asmad ya shaidata, da sauri ya rikota yana dube-dube don kar wasu su ganshi a hankali ya ce "ke ce Miemie?" Kai ta gyaɗa ta ce "ka kaini wajen Mommana..."

*YAR MUTAN RANO*

SANGARTA COMPLETEWo Geschichten leben. Entdecke jetzt