"I love you Meesha." Dr ya faɗa yana kara shigar ta jikinsa

"I love you too." Ameesha ta ba shi amsa, wani irin tashi zaune ya yi wannan shi ne karon farko da ya ji Ameesha ta furta tana sonsa ita ma.

"Kina so na yaushe kika fara so na?" Dr ya yi tambayarsa da mamaki.

Babu kunya ta ce

"Tun ranar farko da muka soma haɗuwa a sahad store na fara sonka Dr."

"Kina nufin a lokacin ɗaya muka yi *MUSAYAR ZUCIYA*? (Littafin Hajja).

"Kwarai kuwa sai zuciyoyinmu ta soma mana *BAHAGGON TUNANI* (littafin Badeeyar beauty queen).

"Ba shakka *SANGARTAR* ki ta taka muhimmiyar rawa wajen hanamu mallakar juna tun tuni." Ya yi maganar yana lakace mata hanci.

Turo baki ta yi ta ce

"To amma duk *LAIFIN WA?* (Littafin Khadija S Muhammad).

"Dukkan mu muna da laifi tunda mun kasa bayyana soyayyar mu a fili, sai faɗa da muke da juna sam bama jituwa, lallai Allah shi kadai yasan abinda ya ɓoye cikin tarayyar mu." Ya dire maganar yana manna mata kiss a kumatu.

"Allah ya bamu hak'urin zama da juna lafiya. Ameesha ta faɗa tana  kara shigewa jikinsa idonta lumshe kamar mai jin bacci.

"Amin." Ya amsa yana ci gaba da wasa da jikinta a haka bacci ya kwashe su, ba su farka ba sai bayan la'asar, Dr ya fara farkawa ya sauke idonsa kan agogon da ke manne a bangon falo, da sauri ya tashi zaune ganin lokacin sallah ya gota. Tashin Ameesha ya soma yi tana farkawa suka shige bedroom Dr niyyar wanka ya yi, don har ya ɗaura towel a kugunsa ya zubawa Ameesha ido ganin tana niyyar kwanciya

"Tashi mu yi wanka mana Cutie time na tafiya fa."

"No! A fito lafiya zan yi nawa."

"Ba ki yin wankan kenan?"

Kai ta gyaɗa tana gyara kwanciya, Dr bai ce komai ba ganin ta rufe ido, ai da sauri ya sureta bai zame da ita ko ina ba sai cikin toilet cikin kwamin wanka ya sakata, yana sanya ta ta mik'e zaune jinta cikin ruwa tsundum kallonsa ta yi a shagwaɓe ta ce

"Please Dr me haka?"

"Soyayya ce haka." Ya bata amsa yana shiga cikin kwamin shi ma. Shiru Ameesha ta yi masa tana jinsa ya gama cire mata kayan jikinta wanka ya mata tas yana yi yana love wanda Meesha ko kallonsa taki balle ta taimaka masa, a haka ma ya ji dadi yana gama mata ta daura alwala cikin towel ya nadeta da kaita bedroom, cikin sauri ya kammala wankan ya yo alwala ko da ya fito ya sameta har ta gama shafe jikinta da mai ɗaya daga cikin jallabiyar Dr Ameesha ta san ya suka gabatar da sallah.

Bayan sun idar Dr ya je ɗakinta kaya ya kwaso mata wanda zata saka, three kwatan wando da karamar top mai hannun bes, tana kwance Dr ya gama mata komai har shiya ta, ya feshe mata jiki da turaruka masu sanyin kamshi, woww gaskiya Ameesha ta yi kyau, Dr ma cikin kananan kaya ya shirya three kwata da singileti, sosai kayan suka amshi jikinsu, falo suka koma inda suka kunna tv suna kallon tashar Bollywood.

Karfe shida saura direban gidan Nenne ya kawo masu abinci, Dr da kan sa ya fita ya kwaso, a dining suka  shirya komai

Ba su zauna cin abincin ba sai da suka gabatar da sallar magriba.

"Cutie je kira Aneesa." Dr ya yi maganar yana kunna tv.

"To! Ameesha ta amsa tana fita, a bangaren Aneesa sai buga kofar take amma Aneesa ko tari taki yi, ran Ameesha ya yi mugun ɓaci domin ta tsani walak'anci a rayuwarta har ta juya zata tafi sai ta ji muryar Aneesa tana faɗin

"Lafiya ake ta buga min kofa?"

Murmushi ta kakalo ta kalleta ta ce

"Lafiya lau Hamman ke kiran ki ya ce ki zo ki ci abinci."

"Kirana in ci abinci? Ba shi da Number ɗina ne da zai sa a rika buga min kofa ina kwance, ko kuma dai an ce masa yunwa nake ji?"

"Wannan ne bani da labari." Cike da takaici Ameesha ta gama maganar ta juya abinta.

"Hee! Ki ce masa bazan zo ba."

Girgiza kai ta yi tana mamakin halinta, babu wanda zai ce ran Ameesha ya ɓaci yanzu, musamman yadda wani kyakkyawar murmushi ke kwance a fuskarta, zaune take akan daya daga cikin kujerar dining din.

"Wai Cutie kin ko sanar mata?"

"Eh! Baby amma ban san me ya hanata fitowa ba." Da ya ke Ameesha cewa Dr ta yi ta ce tana zuwa.

Don ba zata iya faɗa masa amsar da Aneesa ta bata ba.

"Ok bari na duba." Ya yi maganar yana tafiya.

Kwance ya sameta ta, da ya yi sallama watsa masa harara ta yi bata da alamar zata tashi

"Ke! Wai me kike ji da shi ne? Ya zaki maida ni wani sa'an ki tun ɗazun ina jiran ki amma kika shanyani?"

Mtsww ta ja tsaki, ta ce

"Cewa na yi bani zuwa ko kuma dole ne sai na ci abincin?"

Jinjina kai Dr ya yi ba tare ya furta komai ba

Yasa kai ya yi ficewarsa, cike da farin ciki suka kammala cin abincin sannan suka faɗa harkar love ɗin su, abin dai ba'a cewa komai sai son barka, haka kwanaki ke ta tafiya soyayya tsakanin Asmad da Ameesha gwanin burgewar.

***
Yau Dr zai koma dakin Aneesa, shi da Ameesha sun kasance cikin rashin walwala, domin sun saba da junansu fiye da tunani cikin kwanaki bakwai din nan shakuwar Ameesha da Dr ba'a cewa komai, bacci, cin abinci, wanka duk a tare suke abinsu, yau kam duk jikinsu ya yi sanyi har gara Dr ya yi karfin halin zuwa office don baya son yaga Ameesha cikin damuwa,

Ameesha ce zaune ta zuba tagumi ta yi zurfi cikin tunani, kallo ɗaya zaka mata kasan tabbas tana cikin damuwa, duba da har Dr ya yi sallama amma bata ji ba, cikin takunsa ya k'arasa har kusa da ita bai yi wata-wata ba rungumota jikinsa, hakan da ya yi shi ya dawo da ita daga tunanin wata ajiyar zuciya ta saki mai karfi ta ce

"Sannu da dawowa baby yaushe ka shigo?"

Da kallon mamaki Dr ya bi Ameesha ya ce

"Ai ba zaki ji ba ke kam tunanin mai kike yi haka da har na shigo baki ji ba?"

"Babu komai baby, mu je ka yi wanka sai ka ci abinci." Tana maganar tana kokarin tashi tsaye.

Gyara zama Dr ya kuma yi yana sha fa sumar kanta ya ce

"Ki fawwalawa Allah duk lamuran ki in sha Allah baki taɓewa Allah ya maki albarka." Maganar ya dire yana sassauta rikon da ya mata. Cikin kankanin lokaci har ya yi wanka ya ci abinci suka zauna suna hiransu mai ban sha'awa har karfe shida, taga Dr baya da alamar tashi don haka sai ta ce

"Baby kalli time fa?" Cikin shagwaɓa ta yi maganar."

Da rashin fahimta yake kallonta, yana son karin bayani

"Ka manta yau dakin Aneesa kake?"

Harara ya watsa mata cikin wasa ya ce "Oh korata kike yi ne?" Ya yi maganar yana mik'ewa.

"A'a baby bana son ka shiga hakkin Aneesa domin nima bani son a shiga nawa, ka tashi ka shirya please."

Bai ko gama sauraronta ba ya shige toilet, bata damu ba sai ma binsa toilet din ta yi, tun yana daure fuska har ya saki ta taimaka masa ya yi, ita ma sai da ta sake wankan kafin suka fito, taimaka masa ta yi ya shirya cikin wani yadi mai shegen kyau kalar milk, sosai kayan suka amshi jikinsa sai fitar da sansanyar kamshi turaren yake, zuciyar Ameesha cike da kishin Aneesa amma ta yi kokarin dannewa.

Haka ta raka Dr har kofar daki, tana binsa da addu'a, sosai yake alfahari da samun Ameesha matsayin mata tabbas yasan duk wani abu da take daurewa kawai take, domin yasan irin shakuwar su da juna shi kan sa yana tunanin yadda zai yi bacci ba tare da Ameesha a jikinsa ba. Da wannan tunanin ya nufi bangaren Aneesa.

Ameesha kam bayan ta rufe kofa, sai ta saki wani irin kuka mai cin rai

Ku yi hakuri Please kwana biyu ban yi typing ba Wallahi tsabar rashin comment ɗin ku yasa Ni kasala, idan kun ci gaba sai nima na ci gaba in Kuma ba ku so sai naji shiru

*YAR MUTAN RANO*

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now