Chapter 2

293 20 0
                                    

Washe gari  da rana inna zulai tana daki tana tinanin abinyi dan ta gaji da halin gwaggo Takayuki ace suna zaune suna kallon ta tana abinda taga dama suma ai in magani ne suma sun iya shi dan dai suna tsoron Allah ne shiyasa suka yi mata shiru amma yau sai nayi maganin ki kwanon zogalin da ta dafa ta janyu tana hadawa sai da ta gama hadawa sannan ta kasa a faranti ta diba ma yara nasu akwano san nan ta kasa na farantan kashi uku kashi daya tai mishi sarkullen ta na fulani tana gamawa ta fita da farantin a hannun ta fuskanta ba yabo ba fallasa sai da ta dauki nata a hannuta sannan ta mikama inna farantin ta dau na gaban ta sannan ta kaima gwaggo talatu nata sai yatsine takeyi kaman Ba zata karba ba ta hannu ta dauka tayi daki tana ce tana kunkunai ita kakai ta san me take cewa inna zulai tace kya dai jida shi da shagen kwadayin tsiya.
Gabda magariba malan ya shiga dakin inna zulai ya shiga yace ta bashi buta zaiyi alwala zai je mashallace yana fitowa ya tarar da gwaggo talatu bakin kofa sai huci takeyi ko ta kanta beyi ba yayi alwala ya fita, har zaka shiga dakin inna zulain sai ta fasa tayi dakin ta bayan sallah magariba kowa na dakin sa sai hayaniya suka ji da malan da gwaggo talatu  inna na fitowa taji malan na cewa gwaggo talatu ban son shirman nan naki mene in na karbi buta nayi alwala a wajan ta itama ai matata ce kin ga talatu ki fita idon na  inna na nan tsaye malan ya fito ran shi a bace gwaggo talatu ta biyu shi a guje tana cewa dakin nata zaka koma kuma a gaban shi ta tsaya ta rike mishi kwalal riga tana baka isaba wallahi yausha kayi baki ina fada kana fada
Jiyayi wani abi ya taho tin daga kafan shi zuwa kan shi ya bude baki zaiyi magana ya kasa magana ba ma san me zai ce bata ba sabi da mamaki maganan ta hannun shi ya kai yana kokarin ya cire hannun ta daga rigan shi kin saki tayi sai ma kara rikawa datayi
Ahankali yace talatu sakain min riga ban zan saki ba me ka isa kayi ka fad.... marin da taji ne yasata yain shiru ba shiri ta saki rigan shi tayi baya hannu yasa ya janyota ya kara mata wani marin sanna yace na baki kan in dawo daga masallaci karna sameki a gidan nan juyawa yayi zai fita inna ta dakatar da shi da cewa haba malan yazaka yank....... dakatar da ita yayi ta hanyar daga mata hannu ya wuce ta ya fita
Gwaggo talatu daki tayi tana cewa sai me in na bar maka gida zaka zo da kafan ka kace na dawo ranan zaka gane kuran ka inna ce ta biyo ta tana ce mata tayi shiru abi abun a hankali ban zanyi shirun ba abun da kike so kenan ai ya koru ni toh ya koran kun ji dadi dan haka ki fitan min a daki inna zata yi magana ta hana ta sai masifa takeyi da zage zage wani uban zagi da tayi ma inna ba shiri ta bar mata dakin
Inna zulai dama da malan ya fita tayi nata daki tana jin dadi sai dai bata so malan yace ta tafi gida ba nayine don malan ya daina tsoron ta amma gadarin ta ya ja mata
Sallaman inna ne ta katsa mata tinani
Sai da ta zauna san nan ta tambaye ta ko ta zan meya hada malan da gwaggo talatu
Ban san meya hada suba amma ina ga dan taga ya shigo daki na ya karbi buta yace min ya makara butance a hannuna zani alwala nima na mika masa ya fita na dauko wata zan fito kenan na hangeta ta labule sai huci takeyi tsayawa nayi ina kallon ta na dauka ma shigowa zatayi sai naga ta jiya ta tafi
Inna tace to ina ga dan malan ya shigo ne shiyasa kin san ta tsani taga yana shiga daku nan mu ran girkin ta
Inna zulai tace haka ne ma shegen kishin tsiya muma ai muna da kishi muba duwatsu bane dan bamu nunawa ne da muna nunawa gidan nan tsagewa zaiyi
Allah ya kyau ta inna tace amma dai ya yanke hukunci a cikin fushi
Ai har da laifin ta inna da batayi masa gadara da rashin kunya da hakan bata faru ba ni dama ba nay.... shiru tayi, girgiza kanta tayi tace hmmm Allah dai ya kyau ta inna
Ameen amma me kike so kice min, me kikayi? ba dai da sa hannun ki a ciki ba? Babu inna kawai dai sai kuma tayi shiru
Kawai dai me inna tace
Hajjo ce inna bata yi min bayani ba tace dai malan zai dai na tsoron ta
Me kike cewane ne zulai me hajjo ta baki
Wallahi ban san haka zai fa ruba inna hajjo ce ta taba ni sirkulle ta ce malan zai dai na tsoron ta in kika duba lama rin zakiga ya dai na tsoron nata sabida da in tana fadan ta baya iyya yin komai sai bata hakuri hajjo ta ce in dai ta ci sirkullan ranan ta wuce ba ta tsokani fada ba za a zauna lafiya sai yan da malan din yayi da ita sabida yanda da ta zauna lafiya haka za a zauna sai dai ma ita take tsoron malan din tace amma in dai tayi fada dashi sai yan da Allah yayi wallahi inna abin nan yadade da tabani na santa da fada shiyasa banyi ba sai yanzu abin da tayi min shekaran jiya shiya sa nayi mata na san laifina ne amma nata yafiyawa
Allah dai ya yafe min inna
Ameen tace kin san da bakiyi ba, hakan ba zai faru ba da kin barta Allah yayi mana maganin ta
Na sani inna amma zuceya sai addu'a zan je na bama malan hakuri in ya shigo na fada masa yanda akayi
Inna ta ce karki soma fada mishi in ba so kike ki bar gidan ba a yau dan a cikin fushi yake ke dai kiyi ta addu'a kina istigifari
Toh inna Allah ya yafe mana bakidaya ameen
Bari naje nayi sallah tin
dazu a kake kira
Inna na fita taga gwaggo talatu dakaya zata tafi sai jan danta sa'idu takeyi shi kuma yana nokewa yana ganin inna ya kwata hannun sa yayi bayan inna yana cewa inna ni ba zan bita ba kice tayi tafiyan ta
Inna tace Ai dama malan be ce ta tafida kai ka bata gama magana ba gwaggo talatu tace koya ce ko bace ba dashi zan tafi ka zo ka wuce ko na zo nan na ci mutin cin ka
Hawayan da ya ke makelewa ya zibo a kumatun shi inna tace kayi hakuri ka bita nasan malan zai je ya dawo da kai kaji
Kanma yayi hakuri mana yaga yan da zanyi da shi
Inna dai bata kulata ba ta share mishi hawayan fuskan shi san nan ta ce ya je su tafi kar dare yayi mushi
Toh yace a hankali ya karasa gaban ta yace kawo jakan na rike
Ta bashi jakan kayan shi ai kuwa tana ba shi ya falla a guje yana cewa ni ba zan biki ba na tafi gan malan
binshi ita ma da gudu tana fadin sai ka bini ban uban ka shi kuma yana fadin ba zan biki ba wuyan rigan shi take kokarin kamuwa ta dan kama ya subuce mata shi kuma kara gudu yake dayaga ta kusa kamo shi ya yarda kayan hannu shi yana ganin shine ya hana shi gudu sosai a soro ya yar ya falle gwaggo talatu a kofan soro ta ci barki ta durkushe tana ta haki ta dade batayi gudu ba sai da ta maida nunfashin ta san na ta hau masufa wai an shiga an fita an rabata da dan ta inna ko abin dariya ya bata.
Tin da gwaggo talatu ta tafi gidan yayi shiru ba hayaniyan fada, yau wata guda kenan ta sha zuwa gun malan kan ya mai da ta tin da dai ba sakin tayayi ba amma duk san data je gun shi ko a kasuwa ko a gona to da fada suke rabuwa ko a hanya suka hadu in ta shigo garin wajan kanwan ta da fada suke rubuwa.
Yau ma hake ce ta faru suna shiryawa zasu silhu gun malan din, innan tace ke tambayan ta anya talatu abin nan ba sa hannu a ciki kuwa ko abinda muke ma kishiyoyin ki ne ya dawo mana dan fa matan nan ta taba fada mana muyi a hankali dan a duban da tayi mana ta ga wataran komai zai lalace, kai inna bokan nan ya ce karya takeyi nidai yau ko me za ayi sai na koma gidan nan boka yace yana gani na sai maida ni in dai na shafa faran kasan nan.
Haka ta shafa faran kasan da boka ya bata a fuska ta sa mayafinta tace inna mu tafi, a bakin kofa ta ci karo da mahaifinta wanda ya gama jin me suke cewa baya tayi da sauri ta tsugun na tace na gama shiryawa kallon tayayi yace a haka zaki tafi fuska furufuru inna tayi saurin fitowa tana cewa faran fauda ta shafa tashi mu tafi inna ya kalla yace taje ta goge faran kasan da ta shafa inna tayi kicin kicin da fuska zatayi masifa ya daga mata hannu muje kawai kugani in faran kasa zatayi muku magani gaba yayi ya bar su a nan.
Da suka je gidan su malan din dan sulhu sai fada ya kaura tsanin malan da gwaggo talatu fada sukayi sosai har ya sake ta haka suka dawo jiki ba kwari tana zauna dakin innan ta tana kuka tana fadin inna nayi alkawarin sai na lalata zuri'an gidan Malan Ali zanyi anfani da abinda ke ciki na.
Wannan kenan...

***********************************
********************************

Comment and vote
Salam Alaiku
Kuyi hakuri da dadewan nayi ban yi muku update ba labarin ne ya goge dan harna gama ya goge sai dana sake ayi min afuwa.
Thank you.

KhadijaTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon