TALATIN DA TARA

Magsimula sa umpisa
                                    

Liyafa sosai aka hada, an ci kuma an sha, an dauki hotuna domin tarihi kai abin dai gwanin sha'awa cikin lafiya da salama aka gudanar da taron, karfe biyar Abba da kansa ya kai Ameesha gida Dr bayan tarin nasihar da tasha a wajen Ummi da Abba, kuka sosai ta yi har idonta ya yi jawur.

Ko time da Abba yasata cikin ɗakinta sai da ya kuma mata nasiha, mai sanyaya zuciya, kafin ya yi mata sallama, shiru ta yi zaune cikin dakin ita ɗaya hawaye suna zubowa daga cikin idonta, maganar Abba ta karshe ita ta kuma sanyaya mata jiki

*"Uwata ki sani ni da kaina na kawoki gidan aurenki, duk ranar da kika fita daga gidan nan da sunan ya ji karki kuskura ki nufo gidana, domin nan shi ne gidanki marufar asirin ki, mutuwa kaɗai nake fatan ta rabaki da gidan nan, Allah ya maki albarka."* Cikin murya mai kamar ta kuka ya gama maganar, don taga lokacin da yasa hannu ya share hawaye.

A fili ta furta "In sha Allah Abba zan yi maka biyayya." Ta yi maganar tana share wasu hawaye da suka zubo.  Sai kuma ta tuno nasihar Ummi, kamar yanzu take mata maganar

"Ameesha ki kula da jinsa, ganinsa, da kuma  dandanon  mijinki,

*1 karki bari ya ji wani abu da daga hankalinsa, ko ta  tsaftar jikinki, jikinki ya  kasance ko yaushe cikin kamshi na turaruka, haka falonki da ɗakunan baccinku, bakinki da duk wani lungu da sako na jikinki*

*2 ma'ana karki bari yaga wani abu da zai bata ransa akanki, musamman ta bangaren gidanki ko jikinki*

*1 karki kasance kullum cikin girka masa abinci kala ɗaya, a'a ko wacce rana ki yi masa kaloli  daban-daban kuma ba guda ɗaya ya ba ki yi hakuri da biyayya, karki kuskura ki bijirewa umarninsa domin aljannarki tana karkashin kafarsa, duk maganar da zaki yi masa ta zama cikin tsusasa murya da nutsuwa, in sha Allah matukar kika lazumci yin haka zaki ci ribar zaman aure.*

Tana cikin wannan tunanin ne ta jiyo motsin mutane kamar a falo, ko kafin ta yi wani kwaukwarar motsi har sun shigo bedroom din, muryar Aunty Saude k'anwar Ummi ta ji, ai da sauri ta daga gyalen ta sauka a gadon tana faɗin

"Sannu Aunty dama yanzu nake tunanin ni kadai a gidan har tsoro ya fara kamani."

"Nima Aunty Halima ta sanyamu zuwa, don ta ce bata son abarki ke ɗaya, nan da wasu awanni idan zaku je dinner zamu koma."

"Ai kam na gode wa Ummina." Hira suka shiga yi da Aunty Saude har lokacin da Dr ya bugo mata waya akan ta shirya, mai mata kwalliya zata shigo don yi mata

"To." Ta amsa tana gyara kwanciya.

Mintina ƙalilan ta ji sallama, lokacin Meena da wasu daga cikin kawayenta sun iso gidan, wanka Meesha ta sake sannan tare da dauro alwala, tana cikin sallah mai mata kwalliya ta iso, bayan ta isar  Aunty Teena ta tsantsara mata kwalliya sosai Meesha ta yi kyau, gama kwalliyar babu dadewa motocin su Dr ya iso, cikin rakiyar Meena ta isa wajen motar da Dr ke ciki, cikin sanyin murya ta yi sallama tare da shiga, amsawa ya yi cikin kasalalliyar murya yana lumshe ido, domin kamashin turaren ta ya kashe masa jiki, Meesha kam kasa ta yi da kanta don ji ta yi a takure take.

A haka suka isa wajen, lokacin wajen ya cika sosai da dan adam, suna zuwa aka soma gudanar da shagalin.

Sosai dinner ta yi kyau, anci an sha, Aneesa ma an halarci wajen dinner, sosai ta yi kokarin danne kishinta har aka tashi, karfe goma aka tashi gida Dr da Ameesha kawai suka nufi gidan

Rike da hannunta Dr yake har cikin bedroom ɗinta, akan gadon ta ya yi mata masauki, yana faɗin

"Heartbeat ki zauna ki huta ina zuwa." Ya yi maganar yana buɗe gyalen ta.

Saurin rintse ido ta yi, domin yadda yake mata wani irin kallo, da kyar ta iya daga kai  ta amsa, domin gaba daya jinta take kamar a daure, murmushi ya saki sannan ya bar dakin.

Mota ya dauka bai dade da fita ba ya dawo, hannunsa dauke da manyan ledoji, falon Ameesha ya shiga ya aje, sannan ya nufi bangaren Aneesa, a falo ya iskota ta zuba uban tagumi, zama ya yi kusa da ita yana faɗin

"My Anne baki kwanta ba?"

"Yanzu nake son kwanciyar." Ta bashi amsa tana mik'ewa.

"Ok ga wannan bari." Ya yi maganar yana mik'a mata."

Ko kallonsa bata tsaya yi ba, ta yi shigewarta idonta taf da hawaye, tsaye Dr ya yi cikin mamaki halin Aneesa, sai kuma ya nufi bedroom ɗinta tunawa da ya yi da Ameesha ita ɗaya.

A kan gado ya ga ta zube tana aikin kuka, da kyar ya lallasheta ya nufi bangaren Ameesha, tana ganin ya fita ta kuma sakin wani kukan, Dr kam ko da ya koma bed din Ameesha a kwance ya sameta.

"Heartbeat ba dai har kin yi bacci ba?"

"Zan yi dai." Ta bashi amsa.

"Oya tashi ba zaki kwanta da yunwa ba."

"Dr nifa na koshi."

"No! Maryam tashi ki ci."

Tashi ta yi tana turo baki, falo ya koma ya dauko plet, juye masu lafiyayyen kasashen kaji ya yi, ya tsiyaya masu fresh milk a glass cup,  lallaɓata ya yi ta ci kadan ta ce ta koshi

"Je ki yi brosh sai ki kwanta nasan kin gaji da yawa."

"To." Ta amsa tana mik'ewa, bata jima ba ta fito kwanciya ta yi tana addu'ar bacci, bata daɗe da kwanciya ba bacci ya kwashe ta.

Murmushi Dr ya yi ganin har bacci ya kwashe Ameesha, lallai bata da wuyar bacci, sai a lokacin ya soma ci, sai da ya koshi sannan ya tattara kayan ya kai kicin, dawowa ya yi yana tofe ta da addu'a ya rufe ta da bargo tare da kara mata gudun AC sannan ya fita.

       *YAR MUTAN RANO*

SANGARTA COMPLETETahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon