"To! Shi ne abin da Dr ya iya faɗa, zuciyarsa cike da tunanin samun nasara ko akasinta, sun daɗe shi da Dr Ansar kafin suka nufi dakin da Ameesha take, tana kwance kamar tana bacci sai dai ba bacci take yi ba allurar da aka mata ne ke aiki a jikinta.

Wajenta Dr ya nufa zama ya yi tare da ɗaura hannunsa a kan fuskarta yana shafa wa a hankali

      "Kar ka damu fa Dr in sha Allah sauki zai zo." Maganar Dr Ansar kenan da ya yiwa Dr Asmad.

Murmushi ya yi ya ce

"Babu komai Dr a wannan shi ne burinmu, saboda zan yi kewarta ta ne daga yanzu har ranar da za'a fito da ita." A ɗan raunane ya dire maganar.

      "True love kenan kada ka damu da wannan, domin kana da matsayi a wajena zaka iya ganinta duk time da kaso."

        "Na gode da karamci, amma da gaske Dr ba zan dawo sai bayan an yi mata aiki, domin nasan zata samu kulawa yadda ya kamata." Ya kai karshen maganar yana mik'ewa tsaye.

      Sosai Dr Ansar ya ji dadin irin yabon da ya samu daga Dr Asmad, wata nuser yasa ta zauna da Ameesha su kuma suka fita, Dr Ansar da kansa ya kai Dr Asmad hotel ɗin da ya sauka, sai da ya ga shigarsa dakin kafin ya yi masa sallama.

Ko da ya shiga falon zubawa ya yi akan kujera yana sauke numfashi, ya yi farin ciki sosai da zuwan sa garin, domin yadda yake ta ganin nasara a kan komai, rigar jikinsa ya cire tare da dauko wayarsa sam ya manta da wata aba wai ita waya Number Bobbo ya Soma kira suka gaisa yana tambayarsa yadda jikin nata yake

        "Da sauki Bobbo na barta a asbiti."

         "To madallah! Allah ya kara lafiya."

        "Amin." Dr ya amsa sannan Bobbo ya mik'awa Nenne wayar, sun gaisa take tambayarsa jikin Ameesha.

       "Ai Nenne Alhamdulillah! Nasara ta samu har an gano matsalar a gabana akai komai, nan yaba Nenne labarin komai da ya faru. Sosai ta ji dadi sai addu'a take zuba masu shi da Dr Ansar.

       "Tun da ka ce gobe za'a mata aiki zuwa jibi zamu taho, ai bamu san abin haka yake ba."

       "Allah ya kawo lafiya, da karfe biyar zasu shiga, kila har ku iso kafin ta farka."

          "In sha Allah muna zuwa, yanzu dai ka sanar da mahaifin Ameesha domin ya samu kwanciyar hankali."

       "Yanzu zan sanar masa, ina Aneesa?"

      "Tana ɓangarena yanzu karfe biyu na dare ne, ka bari da asbah sai ka kirata, ko dama ba ku yi waya ba ne?" Cikin mintinan da ba su fi uku ba Nenne ta yi masa maganar.

     "A'a Nenne mun yi waya da ita ɗazun." Ya ba Nenne amsa.

     "To shi kenan Allah ya taimaka ya bada nasara."

      "Amin." Ya amsa sannan suka yi sallama.

Wayar Alhaji Taheer ya kira, bayan sun gaisa yake masa bayanin komai, sosai Abba ya ji dadin wannan bayani, suna gama wayar ya tashi ya dauro alwalarsa kamar yadda Nenne da Bobbo suka suka yi duk addu'ar tasu akan samun nasara aikin da za'a yi mata ne.

   Shi ma Dr toilet ya shiga sai da ya yi wanka ya dauro alwala jallabiya ya sa, kafin ya tayar da sallah, ya daɗe yana addu'a, sai kusan huɗu bacci ya kwashe shi.

Bacci sosai Dr ya yi  bai farka ba sai karfe tara na safe, da sauri cikin takaicin irin baccin da ya yi har ya rasa sallah aka lokaci yake, toilet ya shiga ya sake wanka tare da alwala, sallah ya gabatar kafin ya kira yan hotel ɗin ya sanar masu abin da yake buk'ata, wayarsa ya dauka ya danna Number Aneesa, lokacin tana kwance cike da tunaninsa sai ta ji karan wayarta dauka ta yi tare da karawa a kunne

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now