SARKI MA'AMUN 2

715 83 29
                                    


GIMBIYA YALUSA ÝAR SARKI MAI FADAR ZINARE...

Isma'il I. El-kanawy

Sarki Ma'amun ya juyo ya kalli Waziri Yahya da fuska me cike da kasaita sannan ya fara magana cikin girmamawa, " Ya kai amintaccen wazirin mahaifina; hakika ka gayamin duk abinda ya dace na sani, ka kuma nuna min duk abinda ya kamata na gani, sai wannan dakin kadai shine baka bude ka nunamin ba, ko meye dalilin hakan?.

Waziri ya kalleshi tare dayin murmushi irin na manya, sannan ya kada baki yace:

"tabbas kayi gaskiya ya babban sarki mai kwarjini da haiba, wannan daki da kake gani mahaifinka marigayi shiya bani umarni da kada na bude maka shi muddin kana son kwanciyar hankalinka ya dore. "

Kamar yaya fah? Wani abune a ciki wanda har kuke tsoron zai tafiyar min da kwanciyar hankalina idan na gani? Sarki Ma'amun ya tambaya cike da zargi.

"Babu komi a ciki sai tarin lu'ulu'u da marjani wanda lokacin bayyana maka su beyi ba" Waziri ya fada yana me kokarin mantar dashi maganar.

"kuma ina fata sarkin adalci baze kuma yimin magana akan wannan batu ba? Ya karasa maganar yana me risinawa.

Sarki Ma'amun ya gigiza kai tare da juyawa yayi hanyar da zata sadashi da cikin gida ba tare daya kuma cewa komai ba.

Dare ya tsala ta yadda babu abinda kakeji sai kadawar iskar damuna mai ratsa jiki da zuciya, tare da kukan tsuntsaye mai dadi da suke rerawa kamar ana busa sarewa, fadawa kuwa da sauran masu tsaron kofar fada tuni sunyi nisa a jan na rago, kai kace banju aka zuba musu a cikin funjalin inibi suka kwankwada. A tsakanin wannan daren ne Sarki Ma'amun ya fito yana tafiyar sanda tare da taka tsantsan, irin tafiyar da mahauniya takeyi akan itacen da bashi da kwari tsoron kada ya balle ta halaka, kai tsaye ya tunkari hanyar da zata sadashi da dakin daya kwallafa ran ganin abinda ke cikinsa, ko shakka babu be yarda da abinda babban wazirin ya gaya masa ba, cewa babu abinda yake cikin dakin sai tarin dukiya wacce lokacin bashi ita beyi ba.

Haka ya dinga sanda tare da boyewa a cikin dan bazawarin daren harya karaso inda kofar dakin take, wacce aka kerata da danyen zinare tare dayi mata ado da zanen dawisu, a wannan lokaci ne abubuwa biyu suka faru wadanda suka Sarki Ma'amun firgita tare da fadawa cikin tsananin mamaki, ganin waziri Yahya da yayi a wajen, zaune akan kujerar zabarjadu kirar birnin Dimishqa kamar bishiyar da aka dasa yana yi masa murmushi, sai kuma ganin dakarun da yayi sun kewaye shi kamar shazumamu cikin shigar yaki...

KOME YAKE SHIRIN FARUWA???

KUYI HAKURI DA WANNAN, DA FATAN BA KUYI FUSHI DANI DA YAWA BA😂😂😂

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 02, 2018 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

GIMBIYA YALUSA ÝAR SARKI MAI FAADAR ZENAREWhere stories live. Discover now