SARKI MA'AMUN 1

710 72 22
                                    

Bayan kwana biyu da yin wannan magana da sarki rashid yayi da waziri yahya mutanen birnin samaraqanda suka wayi gari da alhinin mutuwar gwarzon sarkinsu, wanda ya lullubesu da adalci, tausayi, da kuma kyautatawa, hakika a tarihin birnin ba a taba yin mutuwa irin wannan ba.

Bayan wata daya da mutuwar sarki rashid sai waziri ya fara tunanin cewa lokaci yayi daya kamata ya fara aiwatar da wasiyyar da sarki yayi masa, kai tsaye ya tashi ya nufi gidan sarki ya tambayi barori inda sarki ma'amun yake ( wanda aka nada a matsayin sabon sarki washegari da mutuwar sarki rashid ). suka nuna masa wani kayataccen lambu  mai cike da kayan marmari da furanni masu dadin kamshi dasa annashuwa a zuciya, wanda sarki ya saba zama a ciki a lokacin yana raye , yarima ma'amun saurayi ne dirarre wanda siffar mazantaka da jarumta suka fara bayyana a jikin shi, saurayi ne dan bana bakwai mai kyakkyawar halitta da kamala.

Waziri yahya yayi masa sallama tare da gaisuwa irinta sarakai, yarima ya dago fuskarsa ya kalli waziri tare da amsawa cikin kasaita da isa, bayan sun gama gaisawa ne sai waziri ya fara fadar abinda ya kawoshi, na irin maganganun da sukai da sarki da kuma alkawarin daya dauka na bashi kariya tare da sashi a hanya sahihiya wacce zata kaishi zuwaga rayuwa mai kyau da kuma shugabanci nagari. Kai tsaye sarki ma'amun ya tashi ya rungume waziri, tare da fashewa da wani tsimammen kuka mai raunana zuciya, "Bazan taba manta irin halaccinka a gareni da kuma mahaifina ba, hakika ka cika amintaccen waziri wanda kowani cikakken sarki zeyi burin samu, kuma in sha Allahu bazan taba tsallake umarninka ba matukar ina raye" sarki ma'amun ya fada idanuwansa na zubar da hawayen farin ciki.

   Waziri yahya yasa saurayin sarkin a gaba; sukayi hanyar komawa cikin gidan sarautar domin ya fara nuna masa irin dukiyar da mahaifinsa ya bari, kama daga dangin zinare da lu'ulu'u, zubardaju da kuma yaqutu, da sauran dangogin dabbobin ni'ima, irinsu shanu da jajayen rakuma, tare da dawisu sarkin ado da talotalo.

Daga nan sai suka rankaya izuwa bangaren dakunan dake zagaye da gidan, tare dayi masa bayanin kowanne daga cikin dakunan da kuma irin amfanin da akeyi dashi.

    Matashin sarkin ya lura da kyau cewa akwai daki guda daya da waziri baya son nuna masa, wanda shi kuma duk yafi daukar hankalinsa saboda irin adon da akai masa, wanda yasa ya fita daban da sauran dakunan, ya tabbata wani muhimmin abune a ciki wanda ake boye masa.

Yaya zata kaya???😁😁

GIMBIYA YALUSA ÝAR SARKI MAI FAADAR ZENAREWhere stories live. Discover now