BABI NA ASHIRIN DA TARA

En başından başla
                                    

      Ido bud'e Gentle ke kallonsu,
   Ko a mafarki bata tab'a tunanin wannan rana ba,
   Shikenan yau tasu ta k'are, asirinta zai tonu kenan,
    Gabanta sai dukan uku uku yake ta kasa rufe bakinta,
   Tunani take waima ya akayi hakan ta kasance?,
    D'an marin kanta take wai idan ma barci takeyi ta farka.

    A k'asa aka ajiye gadon kusa da Ummimah, Gentke kuwa tasha mamkin halin da taga YB ciki,
   K'yafta masa ido kawai take tare da d'an murmushin yak'e wanda da k'yar take fiddoshi.

     Gyaran murya Umar yayi yace
     "Sarki Manu kotu zata so jin cikakken sunanka, garin daka tashi, sannan kuam menene alak'arka da Salmah Gentle?".

    Tuni Gentle ciki ya d'uri ruwa, zawayi take ji amma babu halin tace zatayi,
    Sai raba ido take tana kallon mahaifinta sannan kuma ta juya ta kalli lawyer'nta.
  
    "Sunana Sulaiman Usman Saraki, zan iya cewa na d'an tab'a rashin ji a baya kafin Allah ya shiryeni yanzu, alak'ata da ita kuwa ita budurwar wani abokinmu ne Abdul K'adir amma duk da AK muke kiransa".
     "Ko zaka iya yima kotu bayanin yanayin tarayyar Gentle da saurayin nata AK?",
    "ehh zan iya mana, yana sonta tana sonshi sosai, harma son da take masa yafi wanda yake mata yawa, hakan yasa ya rainata sosai saboda yaji tana yawan fad'in ba zata iya rayuwa idan babushi ba,
     Babu abunda zai nema a wurinta ya rasa, zina kuwa sun miyar da ita tamkar abincinsu, sun zama kamar miji da mata, abun nasu har a cikin makaranta yinshi suke kuma kusan kowa ya san da hakan,
   Wata rana...." ya basu labarin avunda ya faru ranar da akayima Ummimah fyad'e.

   Salati duka mutanen dake cikin kotun suka d'auka,
   Alhaji Abu Abu kuwa sai cire hula yayi, dukda sanyin da akeyi amma shi zufa yakeyi tsabar kunya da yaji, gashi d'an siyasa sananne kuma a gaban jama'a wannan abun yana neman ya kasance.

    "K'arya kakeyi wallahi ni banma sanka ba? A gidan uwarwa ka sanni? Kaji min mutum da sharri, ko tab'a ganinka banyi ba amma kake fad'in haka, ya mai shari'ah karka yarda dashi wallahi k'arya yake".

   Daka mata tsawa alk'ali yayi had'e da buga teburinshi,
    "Karki manta nan kotu ce ba wurin shirme ba, ki nemi izinin magana idan kina son kiyi ba wai ki sakota haka ba".

   Shiru tayi gabanta sai fad'uwa yake,
   Ji take tamkar k'afarta ba sata iya d'aukar gangar jikinta ba.

       Ga YB umar ya koma yace
     "Me zaka iya fad'i game da maganganun da Sarki Manu yayi?"
      Cikin muryar ciwo YB yace
    "Babu k'ari ko kad'an a bayananshi,
    Ina d'aya daga cikin wanda sukama Aishatu fyad'e kuma Gentle ce ta sakamu,
   Duk sauran wanda mukayi abun tare babu wanda ya sake samun kwanciyar hankali tun daga ranar da muka mata fyad'en,
     Kwatsam kwanakin baya munyi shayr shayenmu muka had'u da tsautsayin accident, baki d'aya mutanen motar suka rasu nine kawai Allah ya kub'utar dani,
    Tun daga wannan lokacin nake rok'on Allah ya had'ani da koda kad'an ne daga mutanen dana zalunta in nemi yafiyarsu,
    Kuma case d'in Aishatu yana d'aya daga cikin abubuwan da nayi wanda suke yawan fad'o min a rai,
    Tun daga wannan lokacin nake fatan Allah ya gwada mib ranar da san had'u da ita dan neman gafararta amma Allah bayyi ba sai yanzu,
    Ko tantama babu Gentle itace ta saka muka mata fyad'e,
   Bayan nan kuma akwai abubuwa da dama wanda ta saka aka mata,
     Itace ta tura 'yan daba suka sace k'annen Aishatu 'yan biyu,
      Tasa an kashe d'aya daga cikinsu aka kai gawarta kan layinsu aka yar,
      Itace ta had'a baki da manyan makaranta aka kori Aishatu akan laifin wai ta zubar da cikin shege harda fad'in wai ba wannan ne na farko ba,
    Itace tasa aka k'ona gidansu Aishatu wanda da bakinta ta bamu labari saboda ni nayi zaton ma bata raye, dan yanda muka mata fyad'e mu kusan takwas sauk'inta ma duk bamu da wani k'arfi sosai a lokacin saboda yanda muka bugu,
   Ban tab'a zaton ma tana raye ba saida ita Gentle d'in ta bamu wannan labaran,
   Ina rok'on wannan kotu mai adalci datayi gaggawar yanke mana hukunci tare da k'watarwa Aishatu hakk'inta" ya k'arisa maganar cikin rawar murya had'e da fashewa da kuka.

    Duk mutanen kotun babu wanda bayyi mamaki ba,
     Hamdala kawai ke tashi a ciki banda b'angaren iyayen Gentle  da har yanzu suke ganin k'age ne aka mata.

     "Yanzu haka d'aya daga cikin k'annen Aishatu tana wurin Gentle a b'oye, banda azaba babu abunda ake mata" YB ya fad'a a hankali.

      Har Sarki Manu saida yayi mamaki sosai, saboda shi duk baima san da wannan mugayen abubuwan da Gentle tasa akama Ummimah ba.

   Kuka Gentle ta fasa da k'arfin gaske wanda duk fad'in kotun babu wanda baiji ba,
    "Na shiga uku ni Salmah, na cuci kaina, kai co na ni Salmah, dama hausawa sunce 'kwana dubu na b'arawo, rana d'aya tal ta mai kaya' yau gashi asirina ya tonu abunda ban tab'a zato ba, nasan tawa ta k'are saboda banida wata hujjar da zan kare kaina" a b'oye tayi maganar amma bata san a bayyane tayita ba,
    Baki d'aya kallo ya koma gareta saboda da k'arfi ne tayi maganar kowa ya ji.



_nagode k'warai da yanda kuke bada lokacinku wurin karanta wannan labarin musamman *Asma'u Umar,* kina d'aya daga cikin manyan fans d'ina ina godiya sosai. Amrah LYSM._



°•°AKA°•°Princess Amrah😘
                  NWA

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin