BABI NA ASHIRIN DA BIYU

1.1K 99 0
                                    

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

               
                   {~74~}

    "Bayan likitan ya tabbatar maku da ciki ne ta zubar sai kuma me ya faru?" Barr. Sa'eed ya jefo masu tambaya yana kallon Sister Fatima da nufin ita zata amsa masa.

   "Gaskiya munyi mamaki sosai, bamuyi tunanin d'alibar wannan jami'ar zatayi wannan ta'asar ba,  ganin munyi mamaki yasa Dr. Khalid ya tabbatar mana da wannan ba shine zubar da cikinta na farko ba, saboda yaga alamomin haka da dama a tattare da ita".

    Kallonshi ya miyar ga alk'ali yace
    "Ina so kotu ta bani dama domin gabatar da Dr. Khalid idan yana kusa".

   "Kotu ta baka dama" alk'alin ya fad'a yana kallon ta inda likitan zai fito.

       Dr. Khalid ne ya taso a hankali ya tsaya kusa da sisters d'in,
   Qur'ani aka bashi yayi rantsuwa  da zai fad'i gaskiya sannan Barr. Sa'eed yace
    "Ko zaka fad'a mana cikakkrn sunanka da kuma abunda  kayi karatunka a kanshi?".

    "Ehh zan fad'a" Dr. Khalid ya bashi amsa.

    "To myna saurarenka",
     "Sunana Khalid Muhammad Khalid, ni d'an asalin garin Katsina ne amma iyayena suna zama a Jalingo nima d'in acan nake zama,
    Ni cikakken likita ne ta fannin abunda  ya shafi mata, yanzu haka inada asibiti tawa ta kaina wadda duk fannin mata ne kawai a cikinta",
    "Good" Barr. Sa'eed ya fad'a,
    "Ko akwai gyara akan bayanan da sisters d'in nan sukayi? Ko kuma wani abu wanda ba gaskiya ba?".

   Shiru yayi kafin yace
    "Tabbas babu k'ari ko d'aya a bayanansu,
   Bayan sun kato Aishatu na dubata sosai na kuma gane irin k'wayar data sha wadda ta nemi illaya rayuwarta,
    Data farfad'o ne nake mata fad'a akan dalilinta nayin haka,
   Shine ta cemin wai tana kunyar a ganta da cikin ne, savoda ita duk iskancinta da bin mazan da takeyi a gidansu ba'a san tana yinshi ba,
   Kuma ta tabbatar min da wannan cikin shine na biyu kuma wancan d'inma zubar dashi tayi,
   Na mata nasiha akan ta daina bin maza amma tace sam bata san wannan ba, ta rigada ta saba da maza dan haka dole sai ta bi...." bai k'arisa maganar da yakeyi ba Barr. Sultana ta mik'e cikin hawaye tace
    "Objection my lord! Bai kamata suna fad'in magana irin haka ba, saboda wannan tamkar cin fuska ne".

    Kallonta alk'ali yayi yace
    "k'orafi bai karb'u ba Barr. Sultana,
    Dr. Khalid ci gaba".

  Wani wawan murmushi Barr. Sa'eed yama Sultana sannan yace
    "Muna jinka Dr."

    Ci gaba da zuba k'arairayi Dr. Khalid yayi, ita dai Ummimah mutuwar zaune ma tayi, ta rasa avunda zata fad'a sai tsabar mamakin hali irin na mutanen yanzu take, lallai kam yanzu kowa ba abun a yarda dashi bane.

       Bayan ya gama duka suka koma suka zauna,
  Alk'ali ya gyara zaman gilashinshi yace
    "Ko akwai mai sauran hujjar da zai gabatar kafin a yanke hukunci?".

   Kai kawai Umar da Sultana suka kad'a cike da takaici, sun san dole ba zasuci wannan shari'ar ba, saboda duk wasu hujjoji nasu anbi an b'atasu, wanda suke da hope akanshi shiru baizo ba, idon Sultana har ya kumbura tsabar kukan da tasha a kotun, Umar kuwa tagumi kawai yayi yama rasa avunda ke masa dad'i.

   Kallonsu suka miyar ga Sultana da Mama da suma hankalin nasu a tashe yake, jin alk'ali ya fara magana yasa suka miyar da hankalinsu a gareshi.

     "A bisa hujjoji da suka gabata na wanda lauyoyi masu kare wadda take k'ara, da kuma na wanda yake kare wadda ake k'ara suka kawo,
   Kotu tayi zurfin tunaninta tare da yanke hukunci.
      Munji yanda kowa ya kawo nasa hujjar, dan haka kotu ta gamsu da kaf bayanan Barr. Sa'eed,
   Ta kuma wanke Salmah Abubakar a bisa k'ararta da Aishatu Abubajar data kawo akan ta saka an mata fyad'e,
    Ita kuma Aishar kotu zata d'aureta har na tsawon watanni bakwai a gidan mata (prison) a bisa b'atawa Salmah suna da tayi, sannan kuma zasu bata tarar naira dubu goma na wahalar zirga zirga data sha, ta baro karatunta ta dawo gida akan wannan shari'ar,
    Amma kuma Aisha da lauyoyinta sunada damar da zasu d'aukaka k'ara idan hukuncin bai masu ba.
    Kooootu!". Alk'ali ya mik'e.

    K'ara ta saki da k'arfi had'e da zubewa k'asa,
   Mama dake kusa da ita tayi saarin duk'awa tana kuka sosai mai tsuma zuciyar mai sauraro,
   Zarah da Rabiatu ma tuni suka fashe da kuka, suna bala'in tausayin k'awarsu,
   Lallai wannan rayuwar ta yanzu avun tsoro ce, dukda cutar Ummimah da akayi amma sai gashi wai ita aka bama rashin gaskiya,
   Koda yake bataga laifin alk'ali ba, saboda shikam yayi amfani da hujjojin da aka kawo masa ne sannan ya yanke hukunci.

    Sultana ma tuni ta fasa kukan mai k'ara fiye da wanda takeyi d'azu,
   Umar nata k'ok'arin rarrashinta dukda shima d'in k'arfin hali ne,
   Tunda yake a rayuwarsa tun fara aikinsa bai tab'a yin shari'ar maras dad'in wannan ba,
   Tsabar rashin gaskiya yayi yawa a cikinta,
    Duk wata hanya da zasubi an dod'e ta.

    Cikin rashin imani da rashin tausayi Barr. Sa'eed ya kalli Umar tare da mik'a masa hannu domin su gaisa,
    Sam Umar yak'i bashi hannun saboda cike yake da takaicinshi,
   Hakan yasa Barr. Sa'eed ya kwashe da dariya yace
    "Ka tuna shari'arma ta farko dani wacce ka kayar dani? Baka sani ba tun daga wannan lokacin nake jin haushinka, na kuma k'uduri aniyar ka gama kayar dani a shari'ah har abada,
    Na dad'e ina fatan *WATA SHARI'AH* ta had'ani dakai, sai gashi kuwa wannan shari'ar ta had'amu, na kuma gwada maka cewa nafi k'arfi n k'aramin lawyer kamarka".

    Cikin dakewa Umar ma ya mik'e tsaye,
    "Ido cikin ido ya kalleshi yace
    "Karka damu da wannan Barr. Sa'eed, ka shirya mu had'u dakai nan gaba kad'an idan munyi apeal (d'aukaka shari'ah), mu muna tare da gaskiyarmu kuma Allah ba zai tab'a barinmu muji kunya ba saboda yana tare da mai gaskiya, dan haka ka sake d'aure d'amararka tayin yak'i dani,
   Ba komai nayi ba a wannan shari'ar sai idan mun d'aukakata zaka tabbatar da k'aramin Barr. Irina yafi babban irinka a fanni da yawa" ya miyar masa da murmushin da bai kai zuci ba.

   Fuska d'aure Barr. Sa'eed yabar wurin,
   Har ga Allah bayyi zaton zasu d'aukaka k'ara ba.

     Gentle kuwa saa washe hak'ora take,
   Iyayenta ma haka, sai kallon banza suka watsawa su Sultana.

     Suna cikin haka ne ma'aikatan gidan yari mata sukazo sanye da uniforma d'insu kalar k'asa,
     Daidai inda Ummimah take suka isa da handcuff d'insu wai sunzo su tafi da ita.



    _kuyi hak'uri da wannan masoya labarin *wata shari'ah* nasan wannan shafin yayi gajerta akan yanda nakeyi, munata hidimar biki ne saisa ya zama kad'an, magode sosai da soyayyar da kuke nunawa wannan littafin musamman 'yan *RAZ NOVELLA 2*, kunfi kowa son labarin, dan haka Amrah loves youh much. #onelove#_




°•°AKA°•°Princess Amrah😘
                  NWA

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now