BABI NA ASHIRIN DA UKU

Start from the beginning
                                    

    Wani mutumi k'aton gaske kamar basamude ya k'yalk'yale da dariya kafin daga baya ya d'aure yace
     Kai ba taurin kai gareka ba? Saida muka gargad'eka akan kar kaje Katsina domin ka bada shaida amma ka nace sai kaje, gashi nan kai bakaje ka bayar da shaidar ba, kuma zaka rasa uwarka".

    "Ya salam!" Dr. Rafiq ya furta.

    "Wallahi na maku alk'awarin indai zasu k'ylemin mamana ba zakuyi mata komai ba to ba zanje kotu in bada shaida ba kunji na rantse,
   Ban had'a umma da kowa ba, bana fatan a dalilina ta rasa rayuwarta,
   Ina sonta fiye da yanda nake son kaina,
    Dan haka wallahi ba zanje ko Katsinan bama barin in bayar da shaida indai zaku k'yaleta".

     Wani d'aya ya tsuke fuska babu ko alamar annuri a tattare dashi yace
     "Zamu saketa, amma da sharad'in inhar wani abu ya faru tofa zakaga abunda baka so, saboda muna tare da kai, muna sane da duk wani motsinka".

   Bakin Dr. Rafiq har rawa yake yace
    "Wal...wallahi...wallahi na amince, na amince".

     "Da ka kyautawa kanka" wancan d'ayan basamuden ya fad'a yana k'ara zaro mugayen idanuwanshi da suke jajur kamar jan garwashi.

       Wani d'aki suka shiga wanda yake duhu dund'um ko tafin hannu ba za'a iya gani ba,
     Kwanceta sukayi da muguwar igiyar da suka nad'eta,
    Selotape suka kwance daga bakinta da suka nad'e dashi,
     Janta sukayi da k'arfin gaske suka fitar daga cikin d'akin,
    Aikuw ahakan ne ya bata damar fashewa da kuka tana k'ara ambatar sunan Allah.

     Daidai inda Dr. Rafiq yake sukayi jifa da ita,
   Saurin k'ank'ameta yayi cikin firgici saboda yanda ta koma cikin kwanakin da basu wuce biyu ba amma kamar zautacciya.

    Suna cikin hakane basamuden nan ya daka masu tsawa, ba arzik'i sukayi shiru sai rawa jikinsu yakeyi.

      "Gaza d'aure masu fuskokinsu mu fitar dasu daga nan".

     Wanda aka kira da Gaza d'in ya zaro ido cikin mamaki yace
    "Ance a k'yalesu hakanan ne?",
     "Banida lokacin amsarka" basamuden ya fad'a a k'ufule.

   Hakan ya tabbatarwa Gaza d'in cewa an amince a sakesu d'in ne, saboda wanda ya sakasu aikin bayada babban amini sama da basamude, ya yarda dashi sosai.

    Bak'in k'yalle ya nema ya d'aure masu fuskokinsu dashi, cikin motarsu mai tint suka sakasu sannan suka tayar da ita suka bar wajen.

       A daidai GRA suka fiddo Dr. Rafiq da Ummanshi sukayi jifa dasu tare da barin wurin a d'ari uku da hamsin.

     Da k'yar da wahala Dr. Rafiq ya samu ya warware avubda aka nad'e fuskarshi dashi,
    Babu wahaka kuwa ya kwance na ummanshi ma.

    K'ara rungumarshi tayi cike da so da k'aunar d'anta.
    "Me ka masu ne Rafiqu? Me ka masu suke neman su illatani?" Ta sake fashewa da kuka.

    "Ummah muje gida zan miki bayanin komai insha Allahu, karki damu babu abunda na masu" ya bata amsa cikin sigar rarrashi saboda halin da yaga ta shiga abun tausayi ce.

      Da k'yar duka mik'e suka tari napep, har k'ofar gida ya kaisu Dr. Rafiq ya rok'eshi da yayi hak'uri har ya shiga gida ya fito masa da kud'insa,
    Bayyi kusu ba kuwa hakance ta kasance.

     Bayan sun natsu sosai k'annen Dr. Rafiq mace da namiji hankalunsu a tashe suka tambayesu inda suka shiga,
     Hakan yasa ya labarta masu komai har case d'in Ummimah wanda shine silar kama Ummansu da akayi shima kuma suka tsareshi wurinsu kawai dan kar yaje ya bayar da shaida,
   Ya kuma fad'a masu alj'awarin daya d'auka akan ba zaije ko Katsinar bama.

   K'anwarshi mace mai suna Dijah ta share hawaye tace
    "Gaskiya yaya gwara da kace masu ba zakaje ba, saboda nikam ban goyi vayan zuwankan ba, komai zai iya faruwa idan har kaje ka bayar da shaidar, saboda rayuwar yanzu abar tsoro ce".

     "Hakane kam Dijah, hausawa sunce 'zaman lafiya dukiya' dan haka mu fita batunsu kawai, idanma shari'ar vata warware ba sai su barsu da Allah shi zai masu sakayya, amma kai kam ka zare hannunka kenan" k'aninshi Shureim ya fad'a yana kallonshi.

    Cike da jarumta ummansu tace
    "Na amince koda ace zan rasa rayuwata kaje ka bayar da shaidar duk abunda ka sani, a yanda ka bani labarin na fahimci yarinyar tanada buk'atar taimako, kuma idan har gaskiya bata fito ba to za'a iya yanke shari'ar duk yanda akaga dama saboda basuda wata hujja dakai kad'ai suka dogara, dan haka na amince ka tashi ka tafi Katsina yanzu!".

     Cikin mamaki ya kalli umman tashi yace
    "Ummah kin amince?",
    "Ehh na amince Rafiqu, idanma kaga baka yarda daka barni ba sai mu tafi tare, nima zan bada tawa shaidar akan d'aureni da sukayi kawai dan kar kaje ka bayar da shaida".

  Kallonta ya sakeyi yace
    "Amma kuma Ummah ai har an zauna shari'ar tun jiya wata k'ilama har an yanke hukunci",
    "Babu komai nidai muje, insha Allahu sai yarinyar tayi nasarah".




°•°AKA°•°Princess Amrah😘
                  NWA

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now