12

10.4K 865 36
                                    

Thank you so very much habibtis coz gskia jiya naqara tabbatarda eznah nada masoya
Inasonku Ina qaunarku kamar yanda kuke yina😍😍

😂😂 Musamman yanda Nima kuka sakani dariyar Abu da Abba ajiyan Dan kuwa comments dinku yasa nasake karantawa Nima nayi dariya sosai ammafa karkuga laifinsu kowa wuya yake gudu yanxu a rayuwarnan sbd duniyar ta lalace... Allah ya karemu ya tsaremu...
Mamuh love you guys more😍

Aysha agamcy and faiza amg this one is for you guys 😍



Suna shigowa gidan zayyan ya bu'dewa Abba dake hada gumi still duk da ac motar ya fito riqeda babbar rigarsa ya miqawa saheeb jakar takardun hannunsa ya nufi Palo yashige direct sama ya haye yashige bedroom yasaka key tareda zubewa bakin gado Sai lokacin yakejin kansa safe..

Abu ma jiki na rawa ya fito motar ya nufi 'dakin jabiru Maigadi da sauri ya fa'da toilet dinsa Dan a buqace yake da bayin.

Kallon yaransa yayi fuska a 'daure yabasu umarnin tsaron lafiyar Abba daga yau din harsai yagama bincikensa.

Part dinsa suka nufa shida zayyan kowannensu da abinda zuciyarsa ke saqa masa..

Zama yayi akujera tareda rintse idanu kansa nason 'daukar zafi akan alamarin Dan kuwa ba tantama yasan dasaka hannun wannan ill mannered girl din....

Zayyan ma tunanin ananon yake sbd da saninta Dan kuwa Dole tasan da hakan zatafaru to Amma idan dasaka hannunta meyasa zata turasu Kuma in a indirect way kenan bazata iya fa'da musu Kai tsayeba wani Abu zai faru idan hakane then watake karewa kokuma 6oyewa....I have to find out komai akanta coz something is definitely fishy...

Kallon saheeb yayi yaga yanayin dayake ciki ya dafasa yace,

Don't stress your self man tunda Allah yasa ba abinda yafaru....

Wani mugun kallo ya watsa Masa yace,

Like seriously,,,wannan crazy yarinyar tayi magana Kan Abba thank God we arrived at the right time idan badan hakaba wat do you think will happen?.....
She has to explain her self coz koma meyene tana sa hannu da masaniya aciki..

Miqewa yayi ya nufi hanyar bedroom dinsa ya shige yabar zayyan din a zaune cikin dogon tunanin alamarin kafin daga baya shima ya miqe ya tafi.

Tunda su bullet suka Kira mum asee suka fa'da Mata abinda yafaru taji wani mummunan baqin ciki yarufeta sbd rashin samun nasara Amma ba komai zata canza salonda ba saheeb da shegun sojojinsaba ko uwarsa dake kabari tayi fatalwa bazata ku6utar dashiba.

Qarfe bakwai na dare suka shigo asibitin shida zayyan kallo 'daya zakai Masa ya burgeka sbd kwarjininsa da izzarsa saidai fuskarsa dake ha'de kamar ko yaushe.

Ita kadaice a 'dakin zaune bakin gadon Abdul daya gama rigima yayi  bacci
gwaggo taje gida ta 'dauko musu wasu abubuwan Dan itama anan zata kwana taredasu.

Sam ba'a cikin cikakkiyar nutsuwarta takeba Dan har lokacin Bata daina fargaba ba.

Tanajin anbude qofar 'dakin tayi zumbur ta miqe tsaye gabanta na fa'duwa musamman dayake shine agaba zayyan na bayansa.

Yawu ta ha'diye da qarfi tareda qura Masa fararen idanuwanta dake cike taf da tsoro da fargaba.

Wani mugun kallo ya watso Mata zaiyi magana zayyan yayi saurin Shan gabansa Yana kallonta cikin 'yar sakewar fuska yace,

Ya jikin Abdul?

Jijjiga Masa Kai tayi sbd bazata iya magana ba still idanuwanta nakan saheeb daya gama burkuta gaba 'daya nutsuwarta da hankalinta da kallonsa...

EZNAH 2016✅Where stories live. Discover now