5

9.4K 939 44
                                    

Zaune baffa yake kan tabarma yayi zuru dawowarsa masallaci kenan
Jafar na gefensa zaune shima cikin rashin da'din Rai Sai aliyu dake tsaye gefe shima dai ran ba da'di
Hamma Yusuf  da Usman kuwa daga masallaci gidan mande direba suka nufa suka sanar dashi zasu bisa idan zai koma da safen sbd su dubo can din koza'a dace Dan Sam Babu Wanda ya rintsa a gidan tunda motar daliban ta iso aka nemi Anano ba'a gantaba Nan hankali yayi tsananin tashi gasu ubaidah da nusaiba Koda aka tambayesu Sai kuka suke su kansu basusan Ina Ina zasuce takeba mande direba kuwa kusan hankalinsa yafi na kowa tashi musamman dasu Yusuf sukace ga hukuma zasu miqasa matuqar ba'a gantaba ko Kuma wani Abu ya sameta.

Inna data fito 'daki sanye da hijabin datayi sallah dashi ta gaida baffan bai amsa mataba sbd takaicinta dayakeji na yanda take qoqarin nuna ko inkula kan 6atan na Anano Wai ita kawaici,
  kicin ta nufa tafara qoqarin hura wuta.

Harara baffa yabita da ita Rai a tsananin 6ace cikin hasala yakira sunanta ta qaraso gabansa daidai Nan idonta ya sauka kan Anano dake tsaye qofar shigowa.

Jafar ne yafara ganinta bayan inna yayi saurin miqewa cikin farin ciki tareda hamdala yakira sunanta da 'dan qarfi.

Da sauri baffa ya juya batareda ya balbale Inna da fadan da yayi niyya ba ya miqe Yana cewa,

Alhamdulillah ya Allah,,,,

Qarasa shigowa cikin tsakar gidan tayi ahankali qafafuwanta na hardewa kamar Wadda kwai ya fashewa aciki tazo gaban baffa ta tsaya tareda sunkuyar da kanta qasa sabbin hawayen fargaba da tsoro na gangaro Mata.

Cikin tsananin kulawa da farin ciki baffa ya riqo hannunta 'daya ya nufi tabarmar daya taso Yana cewa,

Ananon baffa me.....

Cak ya tsaya Jin Bata motsa daga inda takeba yayi saurin juyowa Sai alokacin ya lura da Inna da aliyu dasuka kasa motsi sun qurawa ananon Ido cikin wani irin yanayi
Maida kallonsa yayi ga ananon saiyaga tuni sautin kukanta yafara fita ahankali.

Sakin hannunta yayi tareda fuskantarta cikin  damuwa da kulawa zaiyi magana idonsa ya lurada  abinda ke hannunta dunqule cikin farin hijab 'dinta.

Kallonta yafarayi tun daga samanta zuwa qasa,
Gabaki 'daya jini ne a uniform dinta ga fuskarta datai jajir ta kumbura...

Daqyar ya tattaro yawu ya ha'diye suka wuce maqoshinsa daqyar kamar zasu yankesa yakalli ananon cikin son yaqar wani tunanin dakeson shigarsa idonsa qyar akan hannuwanta yace,

Ananon baffa meya sameki Kuma menene wannan a hannunki?

Inna da tuni tafara mantawa da kawaici cikin tsananin fargaba ta matso tareda Kai hannunta dake rawa zata bu'de baffa yayi saurin riqe hannunta still idanuwansa nakan Anano yace,

Anano meya sameki?
Kafadamin idan ba wanine yayi Miki mummunan illa ba....

Kuka tasake fashewa dashi Mai qarfi daidai shigowarsu Yusuf suka qaraso da sauri saidai suna qarewa kayan jikin Anano kallo gabansu yayi mummunan fa'duwa sbd sun saddaqarda fyade akayiwa 'yar qanwar tasu
Bango Yusuf ya dafe Yana karanto innalillahi cikin tsananin tashin hankali.

Usman ma cikin tashin hankalin ya sulale qasa zaune jafar dayake da tsananin sanyi da karyayiyar zuciya tuni yafara hawayen tausayin 'yar qanwarsu da aka 6atawa rayuwa aliyu kuwa baffa yayi saurin riqewa ganin zai iya zubewa qasa sbd halinda yashiga.

Cikin zafin nama da takaici inna ta fuzge hijabin Saida jaririn yakusa fa'duwa cikin wani mugun sauri Anano tayi saurin zubewa qasa ta taresa tareda qanqamesa da sauri jikinta na rawa shikuwa jaririn Sai alokacin yasaki wani irin kukan jarirai Wanda tunda yafado Sai alokacin yayi kuka.

Yusuf,Usman,aliyu da baffa kusan dukaninsu atare suka zabura sunakai kallonsu ga jaririn Dan sai alokacin suka sanda akwai wani Abu acikin hijabin Anano din.

EZNAH 2016✅Where stories live. Discover now