D'ayan Barrister'n yace
    "Sunana Barrister Sa'eed Bebeji, lauya mai kare wadda ake k'ara" yama Umar shu'umin murmushi sannan ya koma ya zauna.

       Alk'ali yace
    "Lauya mai kare wadda ake k'ara, ko kanada hujja?".

    Tashi Umar yayi ya fuskanci alk'ali yace
     "Ehh inada ita ya mai shari'ah",
     "Kotu tana son gani" ya fad'a bayan ya zare gilashinshi.

     "Zan iya ganin Salmah Abubakar?" Barr. Umar ya tambaya bayan ya miyar  da kallonshi ga sauran mutane.

    Cikin daburcewa Gentle ta mik'e a susuce take taku har ta iso inda aka tanadar domin tsayuwar wanda ake tuhuma.

    Kusa da ita Umar ya matsa ya kalleta cikin ido yace
     "Kotu zataso jin cikakken sunanki daga bakinki?",
     "Sunana Salmah Abubakar" ta bashi amsa a tak'aice.

    "Salmah kad'ai? Babu wani lak'ani da ake miki?".

    Cikin in-ina tace
    "Ana...ana cemin Gentle",
    "Good malama Gentle, ko zaki fad'awa kotu alak'arki da Aisha Abubkar? Ina nufin wadda tayi k'ararki",
    "Ehh Aisha k'awata ce sosai tun a Secondary School, mun shak'u sosai da ita hakab yasa har jami'a muka cik'e d'aya a JAMB d'inmu kuma course iri d'aya, tare muke karatu kwatsam naji ance wai an koreta daga makaranta saboda an kamata da case d'in ta zubar da ciki".

    Har cikin ran Ummimah taji wannan maganar, jin hawaye tayi suna zarya a kumatunta.

     "Wane irin yanayi kika sjiga a lokacin da kikaji wannan maganar? Ina nufin kin yarda da maganar ko kuwa kin musa?" Ya tambayeta.

     "Nayi mamaki sosai, amma kuma daga baya sai na cire mamakin saboda mutanen yanzu abun tsoro ne" Gentle ta bashi amsa.

     "To duk yanda kike k'awance da ita har baki san tana yawon banza ba? Kuna rabuwa kenan?",
    "Ehh a'a, da dai bamu rabuwa da ita, amma kuma lokaci d'aya ta canja halinta, batada aiki sai yawon banza, idan na mata magana tace babu ruwana da ita, kowa yaji da kansa".

     "kina nufin bakiji damuwa ko kad'an ba a lokacin da akace an koreta daga makaranta? Amma a yanda kuke da ita ya kamata ace ko yaya kinyi mamaki saboda ace babbar k'awarki wannan al'amarin ya faru da ita abun mamaki ne".

    Cike da gadara Gentle tace
    "Nikam banji komai ba gaskiya, saboda dama ta dad'e da canja halinta, kuma ta nuna tafi k'arfina",
      "malama Gentle kuma bakya tunanin ko wasu k'awayen ne ta canja yasa ta rabu dake? Saboda kinsan zaman da kuke zaku iya gundurar juna, sannan kuma kina nufin ke kullum kina zaune cikin d'aki daga can sai School area kawai kike zuwa? Kenan bakya zuwa wurin kowa?".

    "Objection my lord!" Barr. Sa'eed ya fad'a a fusace,
     "Wannan kuma rayuwarta ce bai shafi shari'armu ba, bai kamata barr. Umar yana yima Salmah irin wannan tambayar ba".

      "Barr. Umar a kiyaye" Alk'ali ya fad'a bayan yayi rubutu a takarda.

    "Malama Gentle ko kinsan wasu k'awayen Aishatu masu suna Zarah BB da Rabiatu Sk? Sannan kuma bakya tunanin ko wurinsu ne take zuwa wani lokacin saisa bakya ganinta?",
     "Ehh nasan tana dasu, amma ni bansan ko wurinsu take zuwa ba, saboda suma d'in wani lokaci suna zuwa wurina nemanta idan ta tafi yawon darenta",
      Murmushi kawai Umar yayi saboda a yanayin kalaman dake fita daga bakinta ma kad'ai ya isa ya tabbatarwa mutum da rashin gaskiyarta.

        "Zaki iya komawa ki zauna har sai na sake nemeki nan gaba" Umar ya fad'a tare da komawa mazauninsa ya zauna.

      "Kafin ta koma ta zauna, ko Barr. Sa'eed yanada tambayar da zayyima Salmah Abubkar wacce yake karewa a wannan shari'ar?" Alk'ali ya tambaya.

    Bayan ya sunkuya k'asa yace
     "Ehh inada ita ya mai shari'ah" ya matso inda take yace
     "Salmah inaso ki fad'a mana yanayin alak'arki da Aishatu a tak'aice",
     "Alak'ata da ita mai k'arfi ce, saboda gidansu talakawa ne ni kuma gidanmu munada hali sosai,
   So wani lokacinma ni nake taimaka masu da abunda zasuci  a gidama barin a School idan tayi broke, komai nata nice kuma tana nuna min jin dad'in hakan,
      Amma kuma lokacin data fara canja hali na fahimci har abinci idan na dafa bata ci, bama ta zama barin taci, wani lokaci idan tayi dare zatazo da abincin restaurant mai rai da lafiya taci ko kallon inda nake batayi" Gentle ta sharara k'arya hankalinta kwance.

     "Barin d'an miyar dake baya, naji kincema Barr. Umar suma k'awayen nata wani lokaci suna zuwa nemanta, hakan ya tabbatar da cewa ba kowane lokaci take tare dasu ba kenan, to kina nufin bataje wurinsu ba kenan suma?",
     "Ehh lallai bataje wurinsu ba kam, tunda inda ace taje wurinsu ai ba zasu zo nemanta inda nake ba".

     "Objection my lord!" Barr. Sultana ta fad'a bayan ta buga teburi,
     "Yanayin yanda suke magana bai kamata ace suna yinta ba ya mai shari'ah! Wannan zai iya zama cin fuska ga wadda take k'ara".

     Jinjina kanshi alk'alin yayi yace
     "Barr. Sa'eed ka tausasa kalamanka".

     "Iyakacin tambayar da zan mata kenan ya mai shari'ah, ina neman kotu ta bani dama domin kiran Aishatu Abubakar, wato wadda take k'ara domin akwai tambayoyin da nake so na mata" Barr. Sa'eed ya fad'a had'e da sunkuyawa k'asa yana kallon alk'ali.

    "Kotu tana son ganin Aishatu Abubakar" alk'alin ya fad'a yana kallon ta inda zata fito.

   A hankali cike da natsuwa ta taso kanta sadde a k'asa ta tsaya inda Gentle ta fita.




°•°AKA°•°Princess Amrah😘
                NWA

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now