Cike da tashin hankali nace "Salmah! Kenan da saninki kika shiga motar nan ake aikata alfasha dake?",
   K'are min kallo tayi ta tabbatar da nice sannan cikin halin ko in kula tace
    "Ehh da sanina ne sai kuma me? Ke Aisha bari kiji in fad'a miki, tun wuri ki fita daga sabgata idan ba haka ba kuma wallahi ni kad'ai nasan matakinda zan d'aukar miki".

   Kallonta nayi cikin ido saboda an kunna security light na cikin makarantar,
    "Kiji tsoron Allah Salmah, ki sani iyayenki da suka kawoki makarantar nan fa sun damk'a miki amanar kanki, idan kikaci amana kuwa sai amana ta kamaki, zina Salmah? Wal'iyadhu billah! Da idona na ganki kina aikatata, sam banyi tsammanin halin naki har yakai haka ba" na fashe da kuka sosai ina k'ara mamakin Salmah.

    Cike da izgili namijin da suke masha'ar tare yace
    "To wai ita wannan wacece ne Gentle?  Taya zaki baru tana fad'a miki magana anyhow?",
    Ban ko kalleshi ba saboda banga abunda zan kalla ga mazinaci ba,
   Dan haka na koma gareta,
   "Kin cuci iyayenki kin kuma cuci kanki, kiyi gaggawar tuba ga Allah saboda Allahu gafurur-raheem ne, idan kika bi sharud'd'an tuba mai yiwuwa ne ya yafe miki".

   "Ke wai ina ruwanki danine? Idan ma abunda yafi zina nayi ina ruwanki? Kija k'azamin jikinki ki k'ara gaba" Gentle ta fad'a cike da masifa.

     "Ke har kinada bakin kiran jikina da k'azami? Ai babu babban k'azamin jiki bayan na mazinata, ko kun manta Allah mad'aukakin sarki yace "wala taqrabuz-zinah",
    Karma mu kusanci zinar barin har mu aikatata, dan haka dan Allah kiyi hak'uri ki rabu da wannan yaran, Salmah  ki koma halayyarki ta baya wadda kika baro gidanku da ita" na k'ara fashewa da kuka ina k'ara tuno k'awancenmu da ita tun ss1.

    "Aisha Kibar wurin nan tun kafin in d'aukar miki mataki" ta sake fad'a tana kallona cikin ido.

    "Bazan tafi in bar wurin nan ba Salmah sai idan tare dakene, ki d'auki duk matakinda saki d'auka dan bazan iya tafiya in barki ke kad'ai ba saboda  zaku iya komawa kuci gaba da aikata mugun aikinda kuke kanyi".

      Kyakkyawan mari saurayin nata ya d'aukeni dashi,
   Take na ringa ganin bishi bishi kamar zan fad'i k'asa,
   Dakewa nayi na had'iye hawayen daya fito min, na k'udura a raina bazan tafi inbar Salmah a wannan halin ba.

   "Ka k'yaleta AK, nasan maganinta" ta fad'a tare da sake juyiwa ta fuskanceni,
    "Wallahi sai nasa anyi miki fyad'e matuk'ar baki bar wurin nan ba".

   A wasa na d'auki abun saboda wannan maganar ban tab'a zaton zata fito daga bakinta ba, kuma ni nayi zaton b'acin raine ya sakata fad'in haka,
   Dan haka naci gaba da tsayuwa ina jiranta tazo mu tafi.

    "Khalifx kuyi mata fyad'e kuma na rok'eku karku sassauta mata, nasan zaku iya ku jata kukai dajin can inda babu haske" Gentle ta fad'a tare da komawarta cikin mota itada saurayin nata wanda naji ta ambata da Ak.

    Kamar wasa wannan k'artin suka ringa jana da k'arfin tsiya suna k'ara turani cikin daji,
   Hankalina ya k'ara tashi sosai ganin da gaske suke abunda Gentle ta sakasu suyi min shid'in zasuyi.
   Ihu nake sosai ina fad'in "Ya Allah ka kareni daga sharrinsu, Baba, Mama kuzo zasu rabani da *martabata* (Ummi Aisha), amma shiru sabida wurin ihunka banzane saboda babu wanda zai iya jina.

     Samari takwas saida sukayi min fyad'e, idan wannan ya gama sai wannan yazo yayi babu sassauci,
   Gashi kuma cike da rashin imani sukeyin abun, sosai nake jin azaba, tun ina ihu har ihun ma ya daina fita sai sabbatu da nakeyi wanda bansan abunda nake fad'i ba,
    Bayan mutum takwas d'in sun gamane na k'arshen yace
    "Manu saura kai, kazo ka gama da ita mu kaita mu jefar, sabida babu alamar ma tanada rai".

   Sama sama nake jin maganganun nasu,
   Wanda suka kira da Manu yace "haba ai wannan rashin imanin naku yayi yawa, taya zakuyiwa yarinya fyad'e har ku takwas? Tunda nake a rayuwata ban tab'a jiba ko a labarai, dan wannan yarinyar ma bana tunanin tana numfashi, gaskiya ta mutu kuma doke zata mutu, gardawa takwas ba wasa ba",
     "Kai wawane matsalata dakai Sarki Manu, komai kai kace tausayi, an fad'a maka a iskanci akwaa tausayi ne?" Wabi daga cikinsu ya fad'a.

    "Aini kasan duk iskancina bana yiwa mace dole, sai idan ita ta amince tace taji ta gani sannan nake mu'amala da ita, sab'aninku da aikinku kenan yima yaran mutane fyad'e" wanda suka kira da Sarki Manu d'in ne yayi wannan maganar.

     Duk abunda akeyi na zama niba rayayyaba ba kuma matacciya ba, Allah dai ya bani ikon sauraren maganganunsu amma kuma ko idona bana iya bud'ewa.

    "Shikenan ai ku d'uketa ku jefar cikin dajin nan, saboda da alama dai ta mutu wannan gawace",
   Ina jin sun fad'i haka gabana ya tsananta bugawa,
    Sai jin muryar Manu naji yayi yace "a'a karku jefarta cikin daji dan Allah, ni ku barni in kaita daga can gefe, yanda za'a iya ganinta cikin sauk'i sai a sallaceta".

    D'aukata kuwa yayi yakai daga can gefen titinda zai zartar da mutum cikin humanities, a hankali ya ajiyeni tun daga nan baccin wahaka ya d'aukeni wanda ban kuma sanin inda kaina yake ba.

    _masu karatu dan Allah kuyi hak'uri da wannan, mura nake fama da ita duk ta kashe min jiki, da k'yar na samu nayi wannan ma._

_Jinjina maras adadi gareki 'yar uwa mai albarka my dear Xarah bb, tabbas kin zamo wani jigo a rayuwata wanda bazan iya misaltashi ba, a kullum burinki shine kiga kin faranta min rai, wannan dalilin yasa nima nake k'ara jaddada miki yanda kike a rayuwata, kinada muhimmanci sosai a gareni, na gaisheki sosai da duk wasu masoyana na nesa dana kusa, *Amrah luvs you much.*_


°•°AKA°•°Princess Amrah😘
              .    NWA

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now