part 28

1.8K 48 1
                                    

💫 *Noorul Huda*💫

28.....

Tada motar yyi da sauri tunawa da Samantha da yayi, yasan in dai mujaheed yaga haza to fa xae iya cewa tana gidansu ma, cikin kankanin lokaci ya isa gidansu Mujaheed gabansa na faduwa, kusan a tare suka shiga compound din da kanwar Mujaheed Aysha ta dawo daga makaranta, ya amsa gaisuwarta yace "Kice ma bakuwar da ke ciki ina jiran ta pls hurry" tare samantha suka fito da Farida ta raka su har gun mota ya sosa kai yace "Kice Umma tayi hakuri ina nan xuwa gaida ta, kunya nake ji shi sa ban shigo ba" dariya kawae Farida tayi tace "Ya Jaheed fa?" Abuturrab yace "Ehh yana nan dawowa..." Daga haka ya sa samantha ta shiga mota shi ma ya shiga da sauri, farida ta d'aga masu hannu ya ja motar ya bar layin, yana fita layin motar sojoji na shiga, xaro ido yyi don bai san ko sun gansa ba ya kara gudun tukinsa, sae da suka dan yi nisa ya kalli samantha yaga idonta na waje, wani tausayinta yaji sosai ya kamo hannunta a hankali yace "Samha!" Kallonsa tayi bata ce komai ba, yace "Kin ci abinci?" Kai kawae ta gyada masa, cikin sanyayyen murya yace "Ki kwantar da hankalin ki kar ki sa ma kanki damuwa plss am with you now and forever..." Hawaye ya ga idonta, yayi parking da damuwa yace "Baki yarda da ni ba kenan Samha..." Ta fashe da kuka tace "My parent...." Ya rike hannayenta duk biyun yace "Ni ma na bijire masu duk sbda ke, kinsan irin neman da ake min yanxu? A guardroom Abba na yasa aka kulle ni da safen nan amma sae da nasan yanda na fito, na tura Mujaheed can gidan ya dauko mun Atm cards dina shima yana can nasan an kullesa yanxu kuma nasan xae iya cewa kina gidansu shi yasa na dauke ki, am at risk Samha but i don't care in har ina tare da ke, i love you... I can do anything for your love" hannu yasa ya share hawayen da ke idonta yace "Kar ki damu Allah yana tare da mu!" Sunkuyar da kai tayi bata ce komai ba, ya ci gaba da tukin, a wani atm ya tsaya yace yana xuwa snn ya fita, sae da ya fara duba nawa ne a account din Small Mum din tasa snn yayi withdraw din dubu hamsin, kamar ance ya waiga yaga motar sojoji na kokarin shan cornern gun bank din, da sauri ya koma ya labe jikin Atm din, ta gefen ido yake kallon motan gabansa yayi mugun faduwa ganin abokin Abbansa da ya fito daga gaban motar, sojoji hudu ma suka sauka daga baya, kamar kiftawan ido ya taho a 160 ya shige cikin mota yayi wani reverse bae damu da harbin da suka fara ba, ko kallon titi bai yi ba ko mota na xuwa ya hau titin ya ja motar a guje, Samantha da duk ta gama rikicewa ta dinga kwala ihu a cikin motor, ta madubi ya ga sojojin sun biyo sa a tasu motar da gudu, ya yo waje da ido yace "Kan bala'i" sae ka rantse tashi sama xae yi tsabar yanda yake gudu don ma titin bbu wasu motoci, samantha dake ta rusa kuka sae cewa take don Allah doctor ka tsaya, don Allah ka tsaya, Bai ko kalleta ba bare ya san me take cewa, hankalinsa ya gama tashi ganin sun kusa tadda su a lokacin kuma suna wajajen court road, bai damu da traffic da ya nuna masa green ba ya wani sha kwana da gudu har ya kusa karo da wata mota ya kauce mata ya ci gaba da gudunsa, traffic din nan ne ya taimaka suka samu distance tsakaninsa da soldiers din, sosai ya ga karfin halin samantha don yasan da wata ce da tuni ta suma, har ya hau titin unguwa Uku bai sassauta gudun da yake ba, a can baya sosai yake hango motar soldiers din, bai son ya shiga wani layi su tadda traffic shi yasa ya gwammace yayi ta gudu a express, hankalinsa ya tashi ganin man motan yayi kasa sosai, yana fara fita outskirt din kano yaga da nisa fa sosai tsakaninsu ya ja ya tsaya ya cire makullin motar ya fito da sauri, har lkcn kudin da yayi withdraw da atm card na aljihunsa, ya xaga ya bude inda take ya fito da ita, wani hanya kamar gona ya ja ta suka bi da gudu, daji ya dinga gani sosai a gaba amma hakan bae sa ya dakata ba, ita ko sai kuka take tana cewa "Baxan iya ba Doctor ka tsaya plss" a haka ya ja ta suka shiga dajin, bai damu da thorns din ciki da dogayen ciyayi ba ga uban duhu suka dinga ratsawa a haka,  tafiya sosai suka yi a ciki ya ga kamar numfashinta na neman daukewa tsabar gajiya don jan ta kawae yake, rikota yayi da sauri ya nemi karkashin wani bishiya ya xaunar da ita yana kallonta bnda kyallin idonta bbu wani haske da yake gani a dajin, ta rike duk hannunsa biyu da kyar tace "Ruwa xan sha doctor!" Maida numfashi ya dinga yi yana kallonta, can ya runtse ido ya dinga maimaita innalillahi wa inna ilaihi raji'un a xuciyarsa, bude idon yyi ya dafe kansa, ta xame hannunta daga nasa ta fashe da kuka, mikewa yayi yana dube duben inda xai samo mata ruwa yaji ya yi kick din abu, da sauri ya duk'a yana laluba meye wnn yaga kettle ne, da ruwa amma ba da yawa ba a ciki, dagawa yayi duk da bai san ruwan meye ba ya kai baki ya sha yaji dai ruwa ne sai dai da jin sa a baki kasan ba wani mai kyau bane, ya hadiya da kyar snn ya kai mata baki, karba tayi ta sha gaba daya, ya ajiye butan, ta rike hannunsa gam cikin rawan Murya tace "Am afraid doctor, tsoro nake ji" xaunawa yyi gefenta ya jawota jikinsa murya can kasa yace "Don't be, am here to protect you, am with you" shiru tayi tayi lamo a jikinsa wanda hakan yasa ya dinga jin bugun xuciyarta, sun kusan minti talatin a haka taji ya kankameta, ta d'ago da sauri, taga idonsa a runtse, a hankali ya bude yana kallon kasa murya can kasa taji yace "Ant, i think it's an ant" kalle kallen kasan ita ma take, xaro ido tayi tayi wani uban ihu da sai da ko ina ya amsa, sai a snn ya ga me ta gani, wato kunama shi ba babba ba shi ba karami ba, ya toshe bakinta ya sa kafa yayi smashing dinsa, ko ina na jikinta rawa yake ta dinga cewa it's a scorpion, ya kai bakinsa kunnenta yace "Shhhh na fa kashe shi..." Jin baxata yi shiru ba ya lumshe ido ya rungumeta gam, tayi lamo jikinsa, a hankali ya xame dankwalin kanta ya daura a gun da kunaman ya harbesa, ba a dau lkci ba bacci ya dauketa.

*Haske writers assoasso*📚✍🏻

💫Noorul Huda💫Where stories live. Discover now