part 18/21

2.3K 60 1
                                    

[8/9, 2:11 PM] Ummey Zee Abakson: 💫 *Noorul Huda*💫

18.....

Murya can kasa yace "And you can't become one koh?" Wani kallo tayi masa ta gefen ido tace "as in?" Shiru yayi bai ce komai ba, can yayi murmushi yace "Gaya min me ya burge ki a Christianity!" Ta girgixa kai tace "I don't want to talk about that now!" Bai sake ce mata komai ba har suka iso layinsu, tace "Kayi dropping dina kawai in karasa da kafa" bai tanka ta ba ya isa har gate dinsu ya tsaya snn ya juya yana kallonta, ta bude motar ta fita hade da daga masa hannu, dauke idonsa yyi ya ja motor ya bar wajen, ta bi sa da kallo har yayi nisa snn ta juya ta shiga cikin gida. Mumy ce xaune parlor da wata bakuwa, ta durkusa ta gaishesu xa ta wuce Mumy tace "Ina bible din naki?" Shiru tayi tana kallonta, lkci daya ta tuna ta bar shi a motar Abuturrab, rasa abinda xata ce tayi, uwar ta watsa mata wani kallo tace "Ba kya ji ne?" Wayar Mumyn ne ya dau kara ta dau wayar tare da dagawa, Bakuwarta da ke xaune ta kalli Samantha tace "Tashi kije" mikewa Samantha tayi da sauri ta bar wajen don in har Mumy ta ci gaba da tambayar xata iya fadi mata gaskiyar daga inda take. Karfe tara saura tana xaune da Mathematics gabanta tana solving don Tuesday suke da maths, gaba daya ta kasa ci gaba don ta manta calculation din, bude kofar dakin aka yi Mumy ta shigo tace "Daughter xan tafi church yanxu akwai prayer da muke yi ma wata...." Da sauri Samantha tace "Yaushe xa ki dawo Mumy" Mumy tace "At dawn, Blessing na nan ai, take care of ur self" daga haka ta juya ta fita, Samantha tayi tagumi, it's always church ta fadi a xuciyarta, shi kuma Abba alwayz politics..... Tabe baki tayi ta ci gaba da kallon math din gabanta, Abuturrab ne ya fado mata ta Kalli agogo, dai dai nn ta ji fitar motar Mumy, mikewa tayi sai kuma ta kalli jikinta ta ga 'yar rigar bacci ne iya gwiwa, ta bude press ta fiddo da kimono mai d'an kauri ta daura kan kayan ta dau veil ta rufe kanta snn ta dau textbook dinta da note book tare da pen sai calc, a hankali ta bude kofar ta ta fita ta leka dakin da mai aikinsu take taga har ta kwanta, a hankali ta sauka kasa ta nufi kofa taga a rufe, ta bude ta fita, sai da ta ganta kofar gida gabanta ya shiga faduwa, tafiya take da sauri da sauri har ta iso kofar gidansu Abuturrab, ta tsaya kusa da gate kamar munafuka, tura gate din tayi ta ji a bude ma yake, ta tura a hankali ta shiga sannan ta rufe, da sauri ta nufi balcony tana lekan parlon ta gansa xaune a kan carpet yana danna laptop yyi backing kofar, cikin dubara ta murda kofar yanda baxai ji ba sbda k'aran Tv, tana shiga parlorn bata rufe kofar ba cikin sanda ta nufesa, ta durkushe bayansa tayi wani k'ara, juyowa yayi da sauri lkci daya ya jawota jikinsa ya matse ta, xaro ido tayi, ya buga goshinsa da nata yana wani murmushi yace "See you! Tun da kika bude gate naji shigowar ki malama" boye fuskarta tayi tace "Ohhh," ya dago kanta yace "yan gidanku sun tafi church kenan" kwace kanta take son yi yaki saketa kamar xata yi kuka tace "Pls ka sake ni mana" kallon kafarta yayi don kimonon ya d'age daga kasa yace "Baki sa kaya ba knn.." Bai kai karshe ba ya dage kimonon, sai ga long legs dinta a waje, ta wani hade rai tana kkrin kwace kanta tace "What's this" ya buda ido yace "Ohh sorry, i never knew you were naked" wani kallo ta watsa masa tace "Am not naked" ya fashe da dariya, ta samu ta kwace kanta ta mike ta dau litattafenta ta nufi kofa, ya tashi da sauri ya isa gun kofar ya rufe, kallonsa take kamar xata yi kuka, ya langwabar da kai yace "Wasa fa nake" tace "Yeah na sani, bude min kofa in wuce" yace "Nooo baby i was only joking" bata ankara ba sai ji tayi ya wani sureta ta runtse ido tace "Doctor....." Kan kujera ya direta yace "Ki hakura plss" da sauri tace "Nayiii" ya ja hancinta yace "Troublesome girl" kallonsa kawai take, ya hura mata iska ta rufe idon da sauri yana murmushi yace "Irin wnn kallo" turo baki tayi tace "I brought my mathematics, put me through pls" daga haka ta bude textbook din tana nuna masa ya karba, k'asa ya sauka ta bi sa, nan ya shiga nuna mata solution din question din, sai kusan goma suka gama, mikewa tayi tace "Ka raka ni plss dare yayi" yace "Spend the night here tunda dare yayi" ta hade rai tace "No, why shud i??" kamo hannunta yayi ya tsare ta da ido yace "Cinye ki xan yi idan kin kwana?" Kallon manyan idanuwan nasa take, murya can ciki yace "Plss dear" a hankali kamar xata yi kuka tace "but it's not decent, it's not proper....." Da sauri yace "Naga dare yayi ne fa..." Xata yi magana yayi mata wani kallo ta kasa cewa komai tana kallonsa, sake hannunta yayi ya nufi kofa ya bude yace "Alryt, you can go sai da safe" ta sauke idonta kasa, ya karasa kujera ya xauna, kallonsa tayi snn ta nufi inda yake ta durkusa tace "Ohk am sorry, i will spend the nyt here sai in tafi da sassafe kamin mumy ta dawo" yace "No, am not forcing, kar ki fara wani tunani fah, you can go...." Hade rai tayi tace "Toh am not going" ya shafa beard dinsa hade da tabe baki yace "Da wani katon idonta a wajen, i guess her thought will be like what is this guy up to da yake son in kwana yau" xaro ido tayi ya fixgota kusa da shi yana murmushi yana kallon kwayar idonta yace "ko ba
Haka ba? Babu abinda xan maki har sai ran da Allah ya mallaka min ke a matsayin matata" buda ido tayi tana kallonsa tace "Matar ka kuma" ya kai fuskarsa dab da nata yace "Ko baxa ki iya aurena ba" xaro ido tayi da mamaki xata yi magana ya rufe bakinta yana murmushi yace "Yesss" daga haka ya mike ya fita ya rufe gate snn ya dawo ciki ya rufe kofa ta bi sa da kallo har ya xauna yace "Za kiyi wanka?" Ta girgixa kai yace "Alryt shiga ki gyara inda xa ki kwana ni parlor xan kwanta before then bari inyi wanka" binsa tayi da ido har ya shiga dakin sai kuma ta bi bayansa, taga har ya shige bathroom, kallon gadon tayi taga it's tidy except from the bedsheet wanda hakan ya nuna alaman yayi bacci a kai, ta karasa ta shiga gyarawa tana gamawa ta dau wayarsa dake gaban mirror ta fara game, har ya fito bata sani ba, sai jin kamshi me dadi hade da ruwa da ya diga a jikinta, da sauri ta dago suka ci karo, ta mike tace "Ohhh sorry" yace "Uhm ohk" sauke idonta tayi ta mayar ga wayar ya nufi gaban mirror, har ya gama shiryawa bata kalli inda yake ba, sai bayan da ya gama ya dawo ya xauna kusa da ita yace "Kina da paper gobe?" Ta girgixa kai tace "Sae Tuesday" kallon game din da take yayi tayi, can ta mika masa wayar tace "Za kayi amfani da shi?" Ya girgixa kai yace "No, i just want you to tell me a story, may be a bible story, i like them, No! Ko kuma mu ci gaba da wanda nake baki ranan" ta kallesa tace "Toh barin in fara baka sae ka ci mim gaba, wani iri kake so?" yace "ko wanne" ta langwabar da kai tace "Ohk let me tell you the story of Joseph you will like it" yace "Tohm" hawa gadon yayi ya nuna mata kusa da shi ta turo baki tace "Nan ma yayi" yayi murmushi yace "Ohk" shiru tayi sai kuma a hankali ta hau ta dawo kusa da shi, nan ta fara basa story din Joseph according to the new testament of their Holy Bible, jin shirun yayi yawa ta dago tana kallonsa taga idonsa lumshe, murya can kasa tace "Doctor..." taji shiru, tsura ma long lashes dinsa ido tayi snn ta sauke idonta kan cute lips dinsa, bacci yake hankalinsa kwance, murmushi tayi ta gyara masa kansa a hankali snn ta koma can karshen gadon ta kwanta ta juya masa baya, nan da nan ita ma bacci ya dauke ta, can cikin dare ya farka ya mike xaune da sauri ta dalilin hasken dakin don wuta a kunne yake har lkcn kuma dama shi bai saba kwana da wuta ba, ya juya ya kalleta yaga ta dukunkune gu daya tana bacci don sanyi ne sosai a dakin ta dalilin ac da ya kure, sauka yyi daga kan gadon ya shiga toilet ya fito snn ya dauko duvet ya dawo kusa da ita ya lullubata da shi ya durkusa kusa da ita yana kallon kyakkyawan fuskarta, lumshe ido yayi ya kai lips dinsa goshinta snn ya mike ya kashe wutan dakin ya koma inda yake ya kwanta. Da asuba a gefensa ya ganta, ya mike zaune bayan ya karanto addu'ar tashi a bacci, ya kusa minti biyar xaune kafin ya mike ya shiga bayi don yin alwala ya wuce masallaci. Ko da ya dawo daga masallaci bata tashi ba, ya cire bargon jikinta ya ja hancinta, mikewa xaune tayi ya wara mata ido yace "Come and start going kar mumy ta dawo" kallon agogo tayi da sauri ta xaro ido, sai kuma ta mike tsaye ta cire kimonon jikinta ya rage daga ita sai half nighty ta shiga bayi, wanke fuskarta tayi ta wanke bakinta da freshener snn ta fito, xaune ta gansa kan darduma da Al-quran a gabansa, dago kai yayi yana kallonta ta karaso ta duka d'an nesa da shi tace "Good morning" ya wara mata manyan idonsa yace "Good morning Baby, kin tashi lafiya" xaro ido tayi tace "Ni kuma?" mikewa tayi tana murmushi ta dau kimononta ta saka ta tattara books dinta tace "Xan tafi" yace "Toh bari in raka ki" da sauri tace "No thank you" daga haka ta d'aga masa hannu ta nufi kofa ya bi ta da ido har ta fita. Karfe hudu da kusan rabi Abuturrab ya dawo daga gun aiki, wanka yayi ya shirya cikin kananun kaya ya fito, kallo daya yayi ma abincinsa da ke ajiye parlor ya fita, main house ya nufa, ya tadda Mami xaune parlor mai aiki na yi mata gyaran gashi, ya xauna ya gaisheta ta amsa tace "Har ka dawo?" Ya jinginar da kansa jikin kujera yace "Na dawo Mami" tace "Toh ka ci abinci?" Girgixa mata kai yayi yace "Ban ci ba tukun" tace "an kai maka can ai" yace "Na gani!" Mikewa yayi ya wuce sama. Yana dakinsu Ramla ta shigo, ta karaso tana kallonsa ganin ba yanda ta saba ganinsa ba ta xauna gefensa tace "What's wrong with you Aliyu?" Kallonta yayi yace "Nothing Mami" tace "ko dai kana son dawowa nan ne?" Murmushi yayi yace "Not at all" ta tabe baki tace "Toh kai ka sani" Shafa kansa yayi yace "Mami a kan maganan da Yakumbo ta min ranan" shiru tayi tana kallonsa sai kuma tace "Toh ya aka yi" ya langwabar da kai yace "I don't know what to do mum" ta tabe baki tace "yanxu duk yan matan da kake bani mu gaisa a waya ina suke?" Dariya yayi yace "Ohhh Mami na fa ce maki they are my frnds!" Tace "Toh, kana son in maka zabi?" Kallonta yayi da sauri yace "No Mami ni fa ina da warce nake so" tace "Toh kuma shine xa ka taho nan kana damuna" ya marairaice yace "Shawara fa na xo nema Mami" Mami tace "Toh ina jin ka, yar ina ce?" Shiru yayi yana kallonta, tace "Kayi shiru!" Xai yi magana aka bude kofar dakin, Khaleesat da Ilham suka shigo da alamar daga boko suke, mikewa yayi yace "Xa muyi magana anjima Mami" bin sa da kallo tayi, Su ilham suka gaishesa a tare, bai ko kallesu ba ya fice, khaleesat ta tabe baki, Ilham tace "Mami kin ga ya daina amsa gaisuwar mu koh?" Mami tace "ku kuka san me ya hada ku da shi ba ruwana" juyawa khaleesat tayi ta fice ilham ta bi bayanta, suna shiga dakinsu Ilham tace "You know what leesat, mu je mu basa hakuri, he's ignoring us" kamar xata yi kuka ta kare maganar, khaleesat na kokarin cire kayan jikinta tace "Am going no where" Ilham tace "Why?" Wani kallo Khaleesat tayi mata tace "Don ma ba mu gaya ma Mami abinda muka gani ba" ilham tayi shiru tana kallonta. Abuturrab na xaune parlornsa yana kallo a laptop misalin shidda da yan mintuna yaji an bude gate, kallon kofa yayi da sauri, aka turo kofar a hankali ta shigo rike da basket dauke da abinci, sosai abayar jikinta yayi mata kyau, ta karaso parlon ba tare da ta bari sun hada ido ba ganin kallon da yake mata, d'an nesa da shi ta xauna tace "Good evening, i brought you food" wara ido yayi ya mike tana ganin haka ita ma ta mike da sauri tayi hanyar kofa, suka ji an kwankwasa kofar, still tayi tana kallon kofar, kawai gani yayi ta juya da sauri tayi hanyar bedroom, aka bude kofar, ilham ce ta shigo ta tsaya daga bakin kofa tana kallonsa kamar xata yi kuka tace "Ya Abu ni dai kayi hakuri....." Ya hade rai yace "Me ya faru da xan yi hakuri, fitan min a parlor" tace "Plsss am sorry sweet bro" xai yi magana ta karaso ta rungumesa tace "Yayana plss mana" shiru yayi bai ce komai ba, a hankali tace "Kaji" janyeta yyi jikinsa yace "Toh tafi daki ki ba ta hakuri right away" dago kai tayi ta kallesa, sai kuma ta kalli hanyar dakin snn ta tafi, tsaye ta ganta ta juya baya, da sauri ta juyo tana kallon Ilham, Ilham ta karasa kusa da ita tana turo baki tace "Kiyi hakuri, we are sorry for everything...." Shiru samantha tayi tana kallonta ko kiftawa bbu.

💫Noorul Huda💫Where stories live. Discover now