Bada jimawa ba kuwa sak'o ya kuma shigowa, d'auka tayi ta karanta
   _"Tudun Wada layin farko gida na biyu yana kallon masallaci"._
    "Good" ta fad'a a bayyane,
    "Insha Allahu zan taimaketa, zanyi shiru bazan fad'awa Umar ba har sai na tabbatar da gaskiyar al'amarin sannan in sanar dashi, shima kuma nasan bakin k'ok'arinshi zai taimaketa idan ya tabbatar da maganar".

      K'arfe hud'u daidai suka tashi aiki,
   A cikin mota Umar yace "nikam na rasa menene tsakanina da Barrister Sa'eed, kwata_kwata baya k'aunata, ko a hanya na had'u dashi na bashi hannu mu gaisa baya amsa, na rasa dalilin hakan".

    "Hmm! Ka rasa dalili fa kace honey, ga dalili k'arara a bayyane,
     Ko ka manta shari'arka ta farko dashi kayi winning? Kuma tun daga nan na kula yake neman shari'ar da zakuyi dashi amma ba'a sameta ba, a tunanina dalilin jin haushinka kenan da yake,
    Kumafa na samu labarin tunda yake a rayuwarshi kaine mutum na farko daya fara kadashi a shari'ah, kuma har yanzu ba'a samu wani ba",
     "Ehh hakane kam, amma ni sai naga kamar duk wannan bai isa yasashi jin haushina ba, ki duba kiga tun lokacin da akayi shari'ar, kusan shekaru goma kenan fa k'ilama anfi, me zai sashi ya rik'e wannan abun? Kuma in banda abunshi ma yanda yake babban barrister wanda duk fad'in k'asar nan an sanshi yayi suna me zaisa ya ringa jin haushina ni d'an k'aramin barrister?".
     "Hmm! Kai kaga haka honey, ai kuwa yanzu idan baka take mashi baya ba to k'iris ya rage ka take bayanshi, yanda yayi suna kaima d'in haka kayi, duk inda ka shiga Barrister Umar Mohd ake fad'i, kaga kuwa ka godewa Allah",
    "Kema kinyi magana Wifey, Allah dai ya k'ara bamu ikon cin halaliyarmu, Allah ya karemu daga cin kud'in cin hanci da rashawa, burinmu a kullum muga mun taimaki mai buk'atar taimako, bama fatan mu tauye gaskiya akan k'arya kawai saboda kud'i ko wata k'awa ta duniya".

     Da wannan firar suka isa gida, da sauri kuwa Haladu ya wage masu gate suka shige da motarsu, cike da soyayya suka fito hannunsu mak'ale da juna,
     Jin k'arar motarsu yasa da gudu Hafsa ta fito tana fad'in "oyoyo oyoyo" ta rungumesu su biyun,
     "Oyoyo Hafsa" Umar ya fad'a bayan ya saki Sultana ya d'auki Hafsa.

      Shigarsu ciki suka samu Haydar da Safiyya sunata wasa abunsu cike da so da k'auna,
      Ganinsu da Haydar yayi yasa ya daina wasan yazo yama iyayenshi oyoyo,
     "Momy yau Safiyya bataje ta d'aukoni School da wuri ba duk saida aka watse aka barni sannan tazo" Hafsa ta fad'a tare da tunzuro baki ita a dole mai fushi.

    "Hafsa me naji kin fad'a?" Sultana ta tambayeta,
    Saurin dafe bakinta tayi tare da fad'in "Aunty Safiyya bataje ta d'aukoni da wuri ba har aka watse aka barni ni kad'ai a School".

    "Au! Kin gyara kenan? Kuma ma ban hanaki kawo min k'arar Safiyya ba? Na hanaki ko ban hanaki ba?" Ta had'a hannayenta biyu ta zare mata ido,
     "Kin hanani momy" Hafsa ta fad'a hawaye na shirin fito mata.

    "To mesa zaki kawo min k'ararta? Sa'arkice ita?  Waya fad'a miki ana kawo babba k'ara?",
     "Babu" ta fad'a bayan hawaye sun fito mata,
     "Ki bata hak'uri",
Juyawa tayi ga Safiyya bayan tayi kneel down ta had'e hannayenta biyu tace "sorry Aunty Safiyya",
    Cike da so da k'auna Safiyya ta jawota ta d'ora kan cinyarta ta rungumeta,
    "Babu komai Hafsa nima ki yafe min kinji? Keke napep ce tamin wahalar samu saida nayi trekking har bakin roundabout sannan na samu".

    "Kema duk laifinki ne ai, dan me zaki tsaya kinama yarinya k'arama kamar Hafsa wai bayanin abunda yasa bakije d'aukarata da wuri ba? Saisa take rainaki wallahi" Sultana ta fad'a dan ta tsani taga k'arami ya raina babba.
     "Babu komai Momy, Hafsa nada biyayya sosai wallahi, yanzu ma nasan fushi tayi ne saboda babu dad'i a watse abar yaro shi kad'ai a School",
     "Kudai kuka sani, akwai abinci ne?",
     "Ehh akwai Momy" Safiyya ta fad'a tare da nufar Kitchen.

    Dama ta riga da ta zuba a food flasks, d'aukowa kawai tayi takai dining,
      D'aki Sultana ta shiga ta kira Umar akan yazo suci abinci,
       "Wanka nake sonyi ne saboda yau na gaji sosai, idan nayi wankan sai in samu d'an k'arfi_k'arfi a jikina",
     "Ehh hakan yayi, nima kaga sai muyi tare dan bakai kad'ai keson samun k'arfin ba" tayi murmushi bayan ta gama maganar.

     "Wifey na ta kaina, ina sonki sosai" ya fad'a k'wayar idonshi akan idonta cike da soyayya,
     "Hmm! Honey ni ba sonka nake ba k'aunarka nake, saboda kasan shi so yana raguwa watan wata rana, amma k'auna bata tab'a raguwa duk tsanani duk wahala",
    "Hakane wfey, ki kud'ura a ranki *ina tare dake* komai rintsi komai wuya",
      "Nima *ina tare dakai* honey na" ta fad'a bayan sun kama hanyar shiga toilet,
     Nidai Amrah gudowa nayi saboda abun yana shirin fin k'arfi na, amma fa ina bakin toilet ina jiran fitowarsu saboda ina son yanayin soyayyar wannan ma'auratan dan ina son in koya nima.

    Sun jima a cikin toilet d'in kafin su fito, Hafsa zaryarta biyu tana nemansu amma bata gansu ba,
   Dan haka ta koma ta fad'awa Safiyya cewa Abba da Momy'nta sun b'ata,
   Dariya kawai Safiyya tayi dan tasan dalilin rashin fitowar tasu.

       Da fitowarsu kuwa mai ta shafa mashi shima kuma ya shafa mata, k'anana kaya ta fiddo mashi blue jeans sai white T-shirt a jikinta an rubuta *"YOU ARE MINE"* da kalar royal blue,
    Itama k'ananan kayan ta fiddo, three qurter ne blue itama sai 'yar polo shirt white da logo na polo royal blue bayanta itama an rubuta *"YOU ARE MINE TOO".*
    Sosai sukayi masifar kyau, nidai "perfect couple" kawai bakina ke furtawa.
    Mak'ale da juna suka fita kamar ba sune suka aje kamar Hafsa ba.
    Kai tsaye dining suka nufa inda suka fara feeding junansu duk da idon Safiyya da Hafsa baisa sunji ko kad'an d'in kunya sun daina ba,
     Koda yake ai a soyayya babu kunya, idan kuwa aka saka kunya to bazaku tab'a jin dad'in rayuwarku ba, wannan haka yake.

Princess Amrah😘
NWA

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ