Najeeb kuwa tunda ya ga Ameesha ta datse kiran, yasan da matsala, shi kuma baya son tambaya don haka sai ya fito daga falon bakin da yake, jikin sa a sanyaye yana Addu'a Allah yasa ba shi ya bata mata rai ba.

Koda ta kammala da cin abinci sama ta koma, tana shiga taji karar wayarta, da sauri ta karasa tare da d'auka, suna nan Meena ta gani akan screen din.

" Ya Meesha wai kuwa kinga takardun? "

Ajiyar zuciya ta ja ta ce

"  Eh Meena na gani a asbiti."

" Masha Allah, wallahi tun dazun tunani kawai nake yi fa."

" Ki bari kawai Meena zamu hadu a school akwai labari."

" Allah k'awata? "

"  Allah kuwa."

" Dan fara bani labari mana kin san ni da son jin labari."

" No maganar bata yuwuwa a waya, ki dai bari har mu hadu din zai fi."

"To ai shi kenan." Meena ta fada.

Daga haka sukayi sallama.

*************************
Koda Asmad ya shiga gidan, bangaren sa ya soma shiga ruwa ya watsa sannan ya nufi babban falo, da sallama ya shiga.

Nenne da wata ne kadai suke zaune a falo, amsa masa sallamar su ka yi, ya ida shiga yana fadin

"Nenne barka da yammaci, Adda sannu da zuwa. "

" Yawwa Asmad an dawo? Ya aikin ya kuma masu jiki? "

" Aiki Alhamdulillah! Masu jiki da sauki. "

Zamewa kasa ya yi tare da gaida Addan, cikin sakin fuska ta amsa, bakuwa ce tazo daga adamawa matar Yayar Nennen Asmad, ta zo ne kan maganar bikin Asmad din.

Amsawa ta yi cikin farin ciki ta ce

"  Asmad ango ya shirye shirye? "

Dukar da kai kasa ya yi cikin kunya bai ce komai ba, sai ma tashi da ya yi ya nufi kicin don yana jin yunwa, koda ya dibi abincin bai zauna a falo ba sai bangaren sa da ya nufa,  don gaba d'aya kunyar Nenne da Adda ya ke ji.

Bayan ya kammala cin abinci ne ya koma cikin bedroom din sa, zama ya yi a bakin gadon sa, hannun sa ya kai saman sumarsa ya na shafawa a hankali, a hankali ya furzar da wani irin iska mai zafi, dai dai da soma ringing din wayarsa, juyo da kai ya yi ya dubi wayar sunan da ya gani ne yasa shi dan jan tsaki.

Bai dauki wayar ba sai ci gaba da tunanin sa kawai ya yi, fuskar Ameesha ce ke masa gizo, ya rasa fahimtar yadda ya ke ji game da ita.

****************************

Zaune suke a karkashin wata bashiya,  saurin dago da kai Meena ta yi bayan ta gama jin labarin da Meesha ta ba, baki bude don tsananin mamaki ta ce

"Meesha Dr dan fullo fa kika ce? yaushe  kuka dai dai ta da shi? "

" ki bari kawai amma wallahi jiya nayi matukar mamaki, da ya bani takardun nan, kinsan Allah daga jiya zuwa yau sai naji cikin kashi dari na haushin da nake ji nashi, ashirin da biyar sun fita."

Murmushi Meena ta yi cikin dai mamakin maganar nata ta ce

" Kuma ina maganar rama Mari aka barta? "

" Tana nan sai na rama komai dadewa. "

Taba Meena amsa tare da gyara zama.

"  Amma nifa gani nake kamar gaba kadan zaku zama masoya, musamman yadda kuke hakan alamar soyayya ce."

Harara Meesha ta watsa wa Meena ta ce

" Allah ya kyauta waye zai yi soyayya da wannan mutumin, kema kin san na wu ce da ajinsa."

Dariyar rainin hankali ta yi ta ce

" Lallai Meesha ke Wai kina ganin kin fi Dr dan fullo aji ne?  To wallahi bari kiji duk fa inda kike tunanin sa ya fi haka. "

Tsaki kawai ta yi tare da tashi tsaye.

Itama Meena ganin haka sai ta mike, suka kama hanyar su da yake daman sun riga da sun gama laccan ranar.

Yau dai sauran kwana bakwai bikin su Yaya Jaheed da Yaya Abdul Malik, shirye shiryen bikin ake ta yi kota ina, tuni gidan Alhaji Taheer ya cika da mutane domin wannan shine karon farko da zai fara auraswa, su Ameesha kam babu zama, sai kai komo ake musamman da Ya Abdul din Meena zai aura.

Kudin da Abban ta ya bata kawai don shagalin biki, dubu dari uku ne, a ce warsa baya son ta nemi komai ta rasa har a gama bikin.

Suna kwance a dakin Meena, bayan sun dawo daga shopping don a gajiye suke likis, wayar Ameesha ce ta soma ruri alamar neman agaji dan dago da kai tayi a hankali ta dubi fuskar wayar, Sunan da ta gani ne yasa ta sakin murmushi. Cikin sauri ta dauki wayar

" Hello."

Ta fada cikin sansanyar murya.

Daga bangaren Najeeb din lumshe ido ya yi, cikin jin dadin muryar da ya ratsa masa kunnuwa.

" Baby son ki na neman hallaka ni fa."

Murmushi mai sauti ta yi ta ce

" Kamar yadda naka ke wahalar dani."

"Kina ina ne haka? "

" Gani gidan su Meena."

" OK bari na zo don ina son ganin beauty face naki."

" Allah ya kawo ka lafiya." ta fada tana gyara kwanciya.

"Please Meesha ga number din Dr ki tura masa da text din bikin."

Maganar da Meena ta fada kenan wanda yasa Meesha saurin tashi zaune  wani harara ta watsawa ta ta ce..."

_*Yar Mutan Rano*

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now