BABI NA BAKWAI

Zacznij od początku
                                    

Ganin mai bawa fulawar gidan ruwa yasa ta ce

"Lafiya kuwa?"

"Lafiya lau Hajiya dama baƙone ya ce a kira ki."

"Baƙo?"

Ta yi tambayar tana kallon wanda ke tsaye gabanta.

"Eh Hajiya."

"To ina zuwa."

Shi ne iyakar abin da Ameesha ta faɗa, mamaki sosai ya rufeta, ita ai bata yi magana da wani akan ya zo gidan su ba 'To waye wannan?' Ta yi wa kanta tambayar da babu amsa.

Bedroom ɗin Ummiee ta nufa, don ko takan Haidar bata yi ba, akan sallaya ta samu Ummiee, zama ta yi gabanta tare da riƙo hannunta ta ce

"Ummi kin ji wai wani ya zo nema na?"

Shafa Addu'ar Ummiee ta yi ta ce "To ya baki tafi ba?”

"To ni ai Ummi ban san shi ba, kuma ai da na san da zuwan shi zai kira wayata."

Ameesha ta yi maganar ranta a ɗan ba ce.

"Haba Ummin Abba ba'a haka, tashi ki ɗauko hijab ki, ki je kiga ko waye daga nan ki haɗa masa abin sha kin ji ko?"

Ɗaga kai Meesha ta yi, badon ranta ya so ba, amma tunda Ummiee ta bata dama bari ta je, ji take kamar ba ita ba, tunda take bata taɓa zuwa harabar gidan su da suna nan tsayuwa da wani ba.

Amma yau gashi wani ya tako har gidansu, tana jinjinawa ko waye wannan da ƙoƙari. Ko ruwa bata ɗauka ba, ta nufi wajen dama jikinta fes yake, fuskar ta shafe yake da powder.

Cikin nutsuwa ta ke tafiyar, jikinta ko'ina iska ke kaɗa ta, tun daga nesa ta soma shaƙar daddar turarensa, tsaye yake ya jingina bayan sa jikin motar, waya ce a hannunsa da alama waya yake, can nesa da shi ta tsaya, tana kallon sa.

Bai san ta iso ba har sai da ya ji ƙamshin turarenta ya cika wajen, a hankali cikin nutsuwa ya juyo da fuskar sa zuwa gareta, fuskar nan tashi ɗauke da murmushi

"Barka da zuwa Gimbiya sarautar mata."

Shi ne abin da ya faɗa, yana kallon Ameesha, ɗan taɓe baki ta yi cikin jin kai ta ce

"Bawan Allah ban gane ka ba, daga ina kuma wajen wa ka zo? "

Murmushin dai ya kuma yi ya ce

"Haba Ameesha baki dai gane ni ba, da farko dai sunana *Najeeb Mansur* ɗan Alhaji Mansur abokin Abban ki."

Zaro ido ta yi cike da mamaki ta ce

"oh! Sannu da zuwa Ya Najeeb ya Alhaji da Momi? "

Ameesha ta tambaya fuskar ta ba yabo ba fallasa.

"Lafiya lau Ameesha, na san zaki yi mamakin gani na a gidanku ko? To wannan ba'a bin mamaki ba ne domin kuwa mai son ɗan tsuntsu shi ke binsa da jifa, gaskiyar magana dai na zo maki da wata magana ne mai muhimmanci, sai dai tunda baki san da zuwa na ba, ina son ki ba ni lokacin da zan dawo mu tattauna."

Kallon sa take tunda ya soma magana, Najeeb dai kyakkyawa ne son kowa ƙin wanda ya rasa, da ganinsa kasan da nutsuwa a tattare da shi, sannan kalaman da ya yi amfani da su wajen yi mata magana sun yi mata daɗi. Amma sai ta basar ta ce

"No ni kam ba ni da wani time, don kullum ina school yau ma ka yi sa'a ne ka iskoni a gidan."

"Haba Princess Meesha ki taimaka, matuƙar baki ba ni dama na fayyace maki abin da ke raina ba, tom zan iya shiga wani hali, ki yi haƙuri ki ba ni dama domin Allah."

Da muryar tausayi ya ƙarasa maganar.

Yadda ya yi maganar har ya kusan bata dariya ya yi, amma sai tayi saurin fuskewa ta ce

"Kana iya dawowa nan da two weeks."

Zaro ido ya yi a ɗan firgice ya ce

" Haba Princess ina laifin two days, wallahi two weeks ya min yawa."

Ta gaji da jin maganar, tana son komawa cikin gida don haka ta ce

"To one week ya yi? Don ina da test a school, a cikin week ɗin nan."

"Allah Ya kai mu amma ba haka naso ba, sai dai kuma tunda Princess ce ta zaɓa ba ni da yadda zan yi."

Har ta kama hanya zata tafi ya ce

"Princess baki ba ni phone number ɗin ki ba please ki ba ni?”

Wayarsa ta amsa tasa masa numbers ɗinta sannan ta wuce. Shi kuma a nashi ɓangaren wani nannauyan ajiyar zuciya ya sauke, da ya gama da wannan, don yasan tunda ya samu number ɗinta ya yi mai wuya.

Maimakon ya yi farinciki da ya samu ta ɗan amince da shi, sai takaici ya rufe shi, don yasan abin da zai aikata ba abin kirki bane, tunda yaudara ce zai yi, takaici sosai da tausayin ta suka rufe shi.

A gefe ɗaya kuma yana yaba kyaunta da nutsuwarta, tabbas da a ce ba shi da Rufaida tofa zai iya aurenta, sai dai shi yanzu Rufaida kawai yake kallo a matsayin mace.

Ko da yake jan motar haka ya yi ta tunanin abin da zai aikata, Allah ya sani umurni zai cika ba yin kansa bane.

*********************************

Zama ya yi kusa da Nanne ya ce (o jod'i haa kombii Nanne! owi

"Nannena da alama yau dai kina tare da farinciki?" ("Nanne aam ko fe'i hande banta ad'on seyi? ")

"Sosai kuwa Asmad tunda burina ya kusa cika." ( "sosai mid'on seye gam heje aam badake hubugo Asmad." )

Dariya ya yi wanda ya kuma fito da asalin kyaun shi ya ce ( o jali ha wad'ega mako beddi wartugo dendenta owi)

"Nannena kenan, hala Saudiyya zaki kuma zuwa? " (" Nannena aam d'oo kaam makka na alorata? ")

"A'a ba Saudiyya ba ne mafarkina na son Asmad ɗina ya yi aure shi yake shirin tabbata." (' a'a na maka sam miyahata koid'ol aam on badake wartugo gonga Asmad aam badake bangugo. ")

"Kai Nannena yo ni da ko budurwa ba ni da ita kike maganar aure?" ("Kai Nanne aam min mowala ko berajo awolwinta hala banga?")

"Ai uba nagari tuni ya samar maka da mata 'yar kirki."( "ai dottijo gonga hebani maa debbo jabdubo")

"Nanne kina nufin Bobbo ya samar mini mata? Oh! Shet." ( "Tani wiaam bobbo aam subani aam debbo? Or toskiyam")

Asmad ya yi maganar cikin wani irin yanayi. (Asmad wi'ika der mettam beram)

"Eh ya zaɓar maka kuma mata yar kirki, wacce kai kanka zakayi Alfahari." (" E of subani Maa debbo kand'o bema to'o larima ko an alarima saito a mani moo")

Nanne ta yi maganar cikin kwantar da hankali. (Nanne wii banjin don wallina moo hakkilo.)

"Wacce mai sa'ar Bobbo ya zaɓa mata ni a matsayin mijinta na aure? " (" mard'o sa'a to be bobbo subani aam?")

"Aneesa!"

Nanne ta faɗa babu shamaki. (Nanne not moo)

Wani irin zabura Asmad ya yi bakin sa na rawa ya ce "What...?" (Asmad haftii hunduko mako don wama owi "d'ume..?")

Yar Mutan Rano

SANGARTA COMPLETEOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz