"Amin." Bobbo ya yi maganar cikin jin daɗi.

"Yawwa har na manta Aneesa fa sun kusa komawa makaranta, don haka zata koma gida."

"Yaushe zata koma ɗin?"

"Ranar Asabar zata koma."

"To Allah Ya kai mu."

"Bobbo ya miƙe tare da faɗin bari na leƙa wajen masu aikin gidan can."

A tare suka fita zuwa falon, suna shiga shi ma Asmad na fitowa daga bedroom ɗinsa, sauri yake yi don dama har ya fita mantawa ya yi shi ne ya dawo.

"Bobbo barka da rana. "

Asmad ya faɗa cike da ladabi.

"Barkammu dai Asmad har ka dawo ne?"

Bobbo ya amsa cike da kulawa.

"Eh amma yanzu zan koma, dama na ɗan yi mantuwa ne."

Asmad ya ƙarasa maganar yana nufa hanyar waje. Da fatar alheri iyayensa suka bi shi.

*******

Najeeb ne a ɓangarensa, ya na faman aikin kai kawo gaba ɗaya kansa ya kulle ya rasa tunani ɗaya da zai yi. " shi damuwarsa Rufaida shin taya zata ɗauki maganar in har ta samu labari?"

Ya yi wa kansa tambayar da ba shi da amsa, zuciyar sa ta ce " Kawai ka yiwa mahaifinka biyayya  tunda umurni ya baka."

Najeeb dai ya kasance ɗane mai biyayya sam baya tsallake maganar mahaifansa, don haka da sauri ya nufi toilet, wanka ya yo kana ya shirya cikin ƙananan kaya wanda suka amshi jikinsa, ya feshe jikinsa da turare mai sanyi ƙamshi, key na motarsa ya ɗauka sannan ya yi waje."

Sai da ya isa ɓangaren mahaifiyarsa, bayan ya gaidata sannan ya nufi parking space.

Tunda ya tada motar ya ke tunanin ta ina zai fara ne? Shi dai bai taɓa zuwa wajen wata budurwa da sunan soyayya ba sai Rufaida, to yau gashi da rana tsaka Abban sa ya ɗaura masa aiki, babban matsalar ma ita ce bashi ya ga yarinyar ya ce yana so ba, da a ce shi ya ganta yana so to da da sauƙi, amma wannan umurnin da wuya in za'a ci nasara.

Rasa inda zai nufa ya yi don haka kawai sai ya tsayar da shawarar zuwa makarantar su.

Bai zame koina ba sai makarantar su Ameesha, don yana tunanin tana school ɗin, tunda yanzu sha ɗaya ne na safe, parking ya yi a kusa da kofar makarantar yana jiran ganin fitowar Ameesha.

Najeeb na zaman jiran ganin Ameesha, ita kuwa tana Asbitin da take Practical, suna zaune a ƙarƙashin wata itaciyar mangwaro hira suke ta sha da ƙawayenta.

Hira suke yi hankali kwance, ita da Meena ce sai wasu 'yan class ɗin su biyu, ɗaya daga cikin wacce suke zaune ta kalle su gaba ɗaya ta ce kun san mene ne? Ta ci gaba ni fa wallahi Dr ɗan fullo burgeni da zai soni wallahi da na more..."

Tun kan ta kai ƙarshen maganar ta yi saurin katseta, ta hanyar cewa “Ai ko kina da aiki wannan mara mutunci ne zaki wani ce kina son sa?  Taf lallai da babban aiki a gaban ki."

"Kai Meesha ke dai naga alamar ba zaku sha inuwa ɗaya da Dr ɗan fullo ba, kodayaushe aka yi maganarsa sai ki soma wani haƙiƙance wa."

Salmah ce ta yi maganar, a ɗan hasale, ɗaya daga cikin wacce suke zaune a wajen.

"Allah ya baku haƙuri, ni fa ba ni da matsala, amma na faɗa maki gaskiya tun wuri ki cire shi a ranki kar ya zame maki wata wahalar, ni shi yasa nake alfahari da kaina domin kuwa Allah bai doro min san maza ba ko kaɗan."

Hango Dr ɗan fullo ta yi yana parking motarsa, ta ja wani dogon tsaki wanda yasa duk suka mai da hankalinsu kanta

"Meesha lafiya kike tsaki?"

"Wancen ɗan rainin hankali ne kalleshi fa, yadda yake wani tafiya yana taƙama, gaskiya Dr bai haɗu ba."

Dariyar rainin hankali kawai Meena ta yi, don tasan Meesha faɗa kawai ta yi, ko mara ido ya shafa Dr ɗan fullo yasan, haɗaɗɗen guy ne, ballantana kuma masu ido matashi mai jini ajika, gashi  kuma billion naira.

"Tashi mu je kawai tunda yau bamu da lacca, mu je gida daga nan ma zan biya na gaida Ummi."

Meena ta ƙarasa maganar tana miƙewa, su dai sauran shiru suka yi suna mamakin yadda Ameesha take raina Dr ɗan fullo.

Najeeb dai na zaune a ƙofar school har sha biyu da rabi, bai ga alamar wata Ameesha zata fito ba, don haka sai kawai ya ja motarsa da niyyar anjima zai kai mata ziyara gidansu.

************************************

Bobbo ya gyara zama tare da mai da hankalinsa kan Nanne dake zaune kusa da shi.

"Yawwa kina jina ko mun gama komai da Alhaji Bashir, sannan su Baffa ma sun shiga maganar, komai an yi na yadda auren zai tafi babu gargada."

Nanne ta dubi maigidan nata, cikin sakin fuska da kulawa ta ce

"Ma Sha Allah Ubangiji Ya tabbatar da Alhairi, sai dai har yanzu baka sanar da ni wacce ka zaɓawa Asmad ɗin a matsayin matar aure ba."

Duk da ta ji ya ambaci sunan Alhaji Bashir, wanda shi ɗin Yaya ne a wajenta, kuma mahaifin ga Aneesa, amma tana son gasgata ko hasashenta ya zama gaskiya.

"Yanzu za ki sani kuma zaki yi farin ciki da zaɓina ba kowa ba ce illa... "

Yar Mutan Rano

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now