“Ku dai Gaskiya ce baku so, ni kuma dole sai na faɗa."

“Ki rike gaskiyar ki bamu so ɗin.”

“Yawwa Abba ina son duk lokacin da kuka haɗu, karka saurara masa ka nuna masa ni ɗin 'yar gatan ka ce.”

“An gama Uwata maza je ki ɗaki ki ɗan watsa ruwa ko za ki ji sanyi.”

“To Abba sai na yi sallah zan fito, don a hanyata ta dawowa na ji an kira.”

“A fito lafiya ɗiyar Abba.”

Murmushi Ummiee ta yi, don wannan halin na Ameesha kaɗai ke burgeta, duk abin da take yi da zarar ta ji an kira sallah, bata bari lokaci ya wuce ta, kusa da Ummiee ta matsa tana cewa

“Ummiee yau me kika dafa mana ne?”

“Tuwon shinkafa ne miyar wake.”

“Wowww! Ummiee kin yi abin da nake son ci.”

Da fa kanta Ummiee ta yi ta ce, “To ga can a dining komai is ready.”

“Ok bari na fito.” Ameesha ta yi maganar ya yin da take taka matakalar benan don hayewa sama.

Farin ciki ne ya kama Alhaji Taheer mahaifin Ameesha ganin yadda suka yi magana cikin walwala da farin ciki.

Shigarta bedroom ɗin ke da wuya sai ta wurgar da Jakkarta dake hannunta (hand bag) tare da cire gyalen da ta yafa, kai tsaye toilet ta nufa ta sakarwa kanta ruwan sanyi, ƙila ko ta samu sassaucin abin da take ji a zuciyarta, ta jima sosai sannan ta fito bayan ta ɗauro alwala, zanen da take sallah ta ɗauko tare da hijjab ɗinta sannan ta tayar da sallar.

Bayan ta idar da sallar, ta shirya cikin wani wando da riga wanda suka yi mata matuƙar kyau, wandon pencil ne kalar pink, rigar kuma body top ne kalar white, sun amshi jikinta, ta yi pakin kanta da ribbon kalar wandon ta, tsaf ta feshe jikinta da turaruka masu ƙamshi.

Masha Allah, Gaskiya Allah ya yi halitta don Ameesha kam babu inda Allah ya rage ta, ta fannin halatta kyakkyawa ce wato (First Class) ajin farko, gata doguwa, bata da ƙiba ko kaɗan, amma fa akwai ta da hips and braest, komai cif.

********************************

Cikin ƙwarewa yake driven motar, fuskar sa ɗauke da wani special smile, haka kawai in ya tuna yarinyar sai ya ji zuciyar sa fes! Sai dai wani ɓangaren na zuciyarsa tana fama da raɗaɗi tare da dana sanin marin da ya mata. A fili ya furta, “Shi is very Beautiful Girl, duk wanda ya samu wannan budurwa a matsayin matar aure babu shakka ya gama morewa a duniya.”

Wayarsa ce ta soma ruri a lamar tana neman agaji, da sauri ya ɗauki wayar ganin mai kiran ya sa shi sakin murmushi, picking ya yi tare da karawa a kunne, “Hello Allah hokke sabbugo Nannena, mid'o a nyalli jam, noi sare?” (“Allah ya baki tsawon rai Nannena, fatan kina lafiya ya gida?”)

“Jamni tawon Asmad mid'o yela wala billare fere kam...” (“Lafiya lau Asmad fatan kai ma baka da matsala?”)

“A'a Nanne wala ko d'ume, jottama mid'o lawol Wartugo sare.” (“A'a Nanne babu matsalar komai, yanzu haka ina hanyata ta dawowa gida”)

“Allah wadde jam amma a hakkilina lawol anani naa barkantejo...”  (“Allah ya dawo min da kai lafiya amma ka kula da kyau ka ji ɗan Albarka.”)

Murmushi ya yi lokacin da ya kammala waya da mahaifiyar na shi, yana jin farin cikin yadda Nannensa ke ba shi kulaww, cikin mintina ƙalilan ya iso unguwarsu, a bakin wani makeken get ya tsaya, horn ya yi cikin sauri maigadin ya wangale masa get ɗin, wowww! Ma Sha Allah, gida ne babba ginin zamani, kai da ganin gidan kasan an kashe kuɗi, da ka shigo gidan da ɗakin maigadi zaka soma karo, gefen dama kuma, wani ɗan ɗakine aka gina da alama na generator ne, sai wasu flowers da aka daddasa masu kyau, su suka kuma sa gidan ya haɗu, gefe guda kuma parking space ne, motoci jere a ciki masu dan banzan kyau.

Sai mutum ya yi dan tafiya kafin ya ida sa shiga ainihin cikin gidan. A parking space ya faka motar shi, sannan ya fito tare da ɗaukan laidar da ya yi sayayya a Shahad ɗin, ƙofar babban falon gidan ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, wata kyakkyawar mace wacce ba zata wuce shekaru 40 zuwa 42 ba zaune cikin haɗaɗɗen  falon, babban falo ne wanda aka ƙawata shi da wasu manya-manyan kujeru  na alfarma, ga wani carpet mai shegen kyau wanda ya fito da ainahin kyaun falon, kalarsa da kujerun ɗaya, wato brown color, haka ma labulen, babban Plasma TV ne manne a bangon falon.

Kallo ɗaya za ka yi wa matar ka san bafulatana ce, fara ce fuskar ta ƙunshe da annuri, mace ce mai riƙo da Addini don hannunta riƙe yake da wani littafin Addu'o'i tana karantawa, jin sallamar dan nata ya sa ta yi saurin d'agowa fuska d'auke da murmushi ta amsa masa sallamar.

Inda take zaune ya ƙarasa, zama ya yi kusa da kafarta tare da lanƙwashe ƙafarsa, ya soma gaidata, shafa kansa ta yi tana faɗin, “Ja66ama Asmad, awartii Jam...” (“Barka da zuwa Asmad ka dawo lafiya?”)

“Jamni tawon Nanne, sai welo minanata...” (“Lafiya Lau Nanne sai dai ina jin matuƙar yunwa.”)

“Ta damu mitimmini nyamdu...” (“Karka damu akwai abinci, ban daɗe da gamawa ba.”)

“Yawwa Nanne 6ewaddina aam sudu aam, hiddeko mi wurta yiwugo...” (“Yawwa Nanne a kawo min bedroom dina yanzu, kafin na fito wanka.”)

“To ha ladidi waddine...” (“Ba ri Ladidi ta kawo maka”.)

“A'a Nanne miyid'a 6ingel d'o nastimi sudu aam, toi aneesa ko'o huwata, hokku moo ne o wadda...” ( "a'a Nanne ban son wannan Yarinyar tana shigar min bedroom, ki dai baa Aneesa ita aikin me take yi?”)

“To yahu hami hokka aneesa man waddine...” (“To je ka Aneesa zata kawo maka.”)

"Yawwa Nanne hanju wad'i miyid'i Ma...” (“Yawwa Nanne shi ya sa nake ƙara sonki.”)

Asmad ya yi maganar yana miƙa mata, ɗaya daga cikin ledar da ya shigo da shi, amsa ta yi tare da sanya masa Albarka, shi kuma ya fita tare da nufa ɓangarensa.

SANGARTA COMPLETEDove le storie prendono vita. Scoprilo ora