page 5

5.2K 368 10
                                    

*M🅰K'OT🅰N JUN🅰*

*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*  *P.M.L*

         *Written by*

         💅💅💅    *SADNAF*💅💅💅

*Follow me on wattpad @ Sadnaf*

*page 5*

Ameer a Palo ya tarar da Zara tana shafawa tab'on jikinta mai daga ita sai towel Dan bata Dade da fitowa daga wanka ba

Tunda taji karar motar Ameer ta d'aura fuskarta sosai babu alamar faraa a tare da ita

Ameer sallama ya k'ara yi akaro na biyu still bata amsa ba dama yasan zaa rina ko da ba fad'a suka yi ba bata wani damu ta amsa Sallama ba

Ledojin hannunsa ya ajiye yace cikin sanyin murya y "Sannu da gida"

Kamar yanda yayi tunanin bazata kula shin ba ko haka akayi Dan ko d'aga kanta batayi ta kalleshi ba ballantana ta kalli inda ya ke

Kusa da ita ya zauna ya tankwashe k'afarsa ya ruk'o hannunta

Wani irin fusge hannunta tayi tare da sakar masa harara tana "don't u dere touch me Ameer na tsaneka wlh namijin da bai San darajar Mace ba shi yake d'aga hannu ya daketa bazan iya zama da namijin da zai ringa jibgata ba dan haka ka bani takardata kawai na tafi gidanmu"

Tace tana k'ara watsa mishi mugun kallo

Ameer murmushi yayi Dan ko kad'an baiji haushin maganganunta ba he deserve more dan this dan sai a yanzu yaga yanda ya farfasa mata jiki

Cikin Sanyi murya yafara magana

"Zara am sorry pls I know what I did was wrong bai kamata na dakeki ba Amma Zara kinsan idan raina ya b'aci bana iya controlling d'in kaina

Zara kinsan halina ina da bala'in kishi   mai yasa zaki fita da sleeping dress har gidan mak'otanmu shi kuma babu kunya babu tsoron Allah ya tsaya yana kare miki kallo Zara dan Allah haka kika ga matarsa ta nayi meyesa bazaki yi koyi da halinta ba

wlh har
yau bansan kamanin matarsa ba sabida yanda take lullub'e jikinta

Zara idan bana sanki babu yanda za'ayi nayi kishinki islamically ma is not right kifita ahaka kina matsayin matar Aure karki manta ko ina na jikin mace Al-aura ce banda fuskarta tafin kafarta da tafin hannayenta am really hurt Dana ganki agaban Adnan atsaye ahaka

Zara ban hanaki kiyi shigar da ranki keso ba wlh Zara ko tsirara ne ma kiyi matsawar dagani sai ke ni zaki yiwa adon nagani naji dadi kisamu lada

  ina rok'onki kiji tsoron Allah ki kiyaye dokokin Aure da martab'arsa ki ringa tsare mutuncin kanki ki ringa tayani kishin kanki pls insha Allah zan miki duk abinda kikeso matsawar bai fi k'arfina ba ki ringa koyi da mak'ociyarki pls she is very decent ga kunya wlh ban tab'a ganin fuskarta ba kullum kanta a sunkuye kuma"

Shiru yayi sakamakon wani mugun kallo da Zara ta watsa mishi tace "OK kana nufin am not decent and banida kunya idan hakane mai zai hana kaje ka aureta ni ka sakeni inje in Auri Wanda ya dace dani dan gaskiya bazan b'oye maka ba wlh ina bala'in Dana sanin Aurenka ka takura min ka hanani sakewa ban tab'a ganin  ranar data fito ta fad'i batare da kayimin fad'a ba agidanan kullum cikin yimin fad'a kake ban  tab'a yin Abu nayi dai-dai ba

Ameer katseta yayi da " ina miki fad'ane cos u are  not doing the Right thing Zara babu yanda za'ayi na hau yi miki fad'a kawai ba tare da dalili ba

idan kikayi ba dai-dai ba ban nusar dake naganar dake ba mai amfanina amatsayina na mijinki ke kinfiso na zuba miki ido kawai ki ringa abinda ranki keso yanzu duba Sallar daya zama obligatory akanki  bakya San kiyi  sai kin ga dama

Mak'otan junaHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin