" kinsan Allah idan kika ga na barki kin tafi salin Alin ba tare da na ci ubanki ba sabida yaudarar da kikamin wlh sai kin saka duk cikon da kikayi agabana naga yanda kike yi"

Meera zuba mishi ido kawai tayi tana kallonsa hawaye nata tsiyayya a idonta sai ayau taji ta tsani barikin da take yi sai ayau tayi nadamar halin da ta jefa kanta ji wani irin wulakanci da Adnan yake mata har dasu Mari

Adnan kuwa d'akin yaje ya kulle yace idan bata saka acucin ba sai dai su kwana ahaka ya fara soka mata Ashar

Meera ganin babu sarki sai Allah ta sunkuya ta zazzago da kayan da take ciko dasu tafara sawa cikin kwarewa

Adnan kuwa kur ya mata da ido yana bala'in mamakin yanda ta sake kayan cikon cikin kwarewa bra d'in ba k'aramin ciko tayi masa ba kaf'in ya taso yayi tuntsin tuntsin kamar gaske

Cikin minti biyar Meera ta dawo mace mai shape sosai ta sunkuya ta d'auki mayafinta still tana sharce hawaye
Cikin muryar Kuka tace "yanzu zan iya tafiya"?

Adnan dak'yar ya rufe bakinsa dan mamaki yace " Amma Allah ya isanmu wlh Ashe ahaka kuke cutar maza har nafara tausayin namijin da tsautsayi zai kai shi yace zai Aureki kinsan Allah baki isa kici dubu biyar d'in Dana baki jiya a banza ba na d'auka ke mace Ce Ashe fuskar mata gareki jikin na maza dan wlh ko ni nan nafiki mazaunai kirjina idan na had'eshi waje d'aya zai ma fi naki banda wahalar dani da kikayi ma jiya na ringa. Kai kawayenki gida maza  kafin na kirga biyar ki bani kudina dana baki jiya

Tunda ya fara magana Meera kukan data ke ya tsaya cak ta kura mishi ido tana mai balain mamakin Rashin mutuncin da yake kuma shirin yi mata

Adnan mik'ewa yayi ya d'auki Jakarta ta tafi da gudu zata k'arba tana "haba dan Allah mai nayi maka haka kake min irin wanan wulakancin da cin mutunci"?

Adnan tureta yayi ya fito da kud'in Jakarta harda sababbin kud'in da aka lik'a awajen bikin jiya ya kirga dubu biyar acikin kud'in kuma da alama dama iya kudinsa ne ajakarta sai 'yan chanjin kud'in likin

Meera wani mugun kuka ta fashe dashi dan gabad'aya kud'in jakarta dubu takwas ne cikon dubu goma take nema sai gashi ya kwashe kud'in daya bata

" Allah ya isa tsakanina dakai Wlh ba zan tab'a yafe maka ba abinda kayimin sai anyiwa 'yarka insha Allah

Adnan kuwa dariya kawai yake yi yana saka kayansa sai daya gama sakawa yace "na barki lafiya aji tsoron Allah a daina a cuci ya za'ayi banci nanun ba nanun ya cini hauka ake yau ma sai nayi mugun mafarki sakamakon wanan bushashen jikin naki Dana kalla nima Allah ya isa ban yafe miki ba sakamakon rashin baccin da ban samu ba jiya 'yar iska Mara mutunci idan kinga dama kitafi idan baki ga dama ba kiyi ta zama ni kinga tafiyata"

Meera da zagi da tsinuwa ta bishi har ya fice daga d'akin ita kuwa ta zube a k'asa tana mai cigaba da kuka.


B'angaren Zara kuwa wunin ranar tunanin Adnan ta ringa yi babu abinda take hangowa sai irin Sexy look d'in da yaringa binta dashi da murmushinsa mai sanyaya zuciya tunanin Adnan ya taimaka wajen rage mata zafi da rad'ad'in dukan da  Ameer ya mata kamshin turaren Adnan dake cikin hankicin da ya bata take ta shak'a tana lumshe ido shaidan na ta k'awata mata Dacewarta da Adnan akan Ameer.

Aliya kuwa a daddafe take iya mik'ewa tayi sallah sabida zazzafan zazzabin daya rufeta kanta kamar ya rab'e gida biyu ahaka ta wuni a d'aki ko abinci bata iya d'orawa ba

Wajen k'arfe biyar na Yamma Adnan ya dawo gida musamman dan yaga Zara dan sosai yake jin sha'awar Zara babu abinda ke masa yawo a ido sai surarta da santala santalan cinyarta har wayarsa ya ringa dubawa yaga ko ta kirashi  yasan Ameer sai dare yake dawowa Tara ko goma shiyasa yayi amfani da wanan damar wajen dawowa da Wuri

Mak'otan junaWhere stories live. Discover now