PROLOGUE

710 94 22
                                    

A cikin idanunshi suke ganin tafasar da zuciyarshi take yi. Sai dai basu cire rai da samuwar abun da suke bukata ba.
Hannunta Marwa da ke wata irin karkarwa ta mika ta kama na Mahfouz, a hankali ta silale ta duka a saman gwiwoyinshi ta na fadin

"Na san ba ta san komai ba dangane da mu. Na san ba mu taso tare da jin dadinta ba. Ba mu san wane kalar farin ciki 'ya'yaye ke ji a duk sadda suka kalli mahaifiyarsu ba. Ba mu san wata irin ni'ima suke ji ba a lokacin da suka sauke nauyinta da ya rataya a wuyansu... amma, Yaa Mahfouz ba za mu taba canja sunanta ba. Ba za mu taba tsaga jikinmu, mu zubar da jininta da ke yawo a cikin namu ba. Ka gane mana."

Kallonta ya yi, yana ganin yadda idanunta suka zurma cike da tashin hankali. Ba kanshi yake ji ba, su yake tausayawa da yadda suke shirin yarda da ita bayan tsayin wannan shekarun.
Su yake tausayawa da yadda suke kokarin raba soyayyar da suka gina a tsakaninsu tare da matar da ba ta san komai dangane da rayuwarsu ba. Matar da ba ta san ya akai suka kawo inda suke a lokacin ba.

Mikewa ya yi yana kallonsu, hannunshi ya sa ya na cakuda gashin kanshi, ba su san yadda rayuwa ke yi mishi yadda take bukata ba. Ba su san iyakar lokutan da ya tsallake rijiya da baya duk dan ya faranta musu ba. Sai dai zai musu yadda suke so, zai takura kanshi, matsawar hakan zai ba da farin ciki a kasan nasu zukatan.

"Ku yi duk yadda kuke so. Ina nufin duk abun da kuka tabbatar zai faranta muku zuciya."

Ya fada yana sanya hannunshi a aljihun wandon chinos dinshi, ya juya da wani irin nauyi a kafafunshi, sai dai ya na jin yadda idanuwansu ke tashi a komai na jikin halittarshi. Suna saka shi yana jin tamkar bai yi musu adalci ba. Tamkar akwai wani abu da suka rasa a cikin kulawar da ya shafe rayuwarshi yana baiwa dukkansu.

***
"Ka na zaton ina kaunarshi ne?"

Ta bukata da idanunta wanda duhun bakin cikin ya gusar da hasken annurinsu.

"Me ya sa ba za ki sanar da su abun da ke tsakaninmu ba? Me ya sa za ki cutar da mu?"

Ya maida mata tambayar yana kafe ta da nashi idanuwan masu matukar tasiri a Kanta. Suna sanya ta ganin gagarumin gi6in da za ta yi wa duniyarta. Dan kuwa ba ta hango wata doguwar rayuwa ba tare da Ashir Baba Sulaiman a cikinta ba.
Kauda fuskarta ta yi tana fadin

"Saboda zan iya sadaukar da komai na gare ta. Lokacina. Kaina. Da duk abun da na tara a duniyata. Daga ciki har da soyayyarka Yaa Ashir!"

Ta ja hancinta da take jin ya toshe mata, muryarta ta karye da wani irin rauni kafun a hankali ta karashe da fadin

"..Ba zan iya zaunawa ina kallon su Hanaan suna kokowa da rayuwa ba.
Ba zan iya daukar ciwon da ganinsu a wulakance zai ajje a kasan zuciyata ba. Ka gane mana.."

"But za mu iya daukarsu 'Isaah! Za mu kula da su. Ni da ke. Mu ba su duk wani jin dadin da kike tunanin rabawa tare da su a rayuwa."

"Ta ya kake ganin hakan mai yiwuwa ne? Ta ina hakan za ta fara ma? Kai da kanka kasan labari ne hakan, Yaa Ashir. Ba abin da zai yiwu ba ne, ka gane mana."

Murmushi ya saki a tsakanin hawayen da ya ji sun sauko sun wanke kuncinshi. Murmushi mai ciwon da yake jin zafinshi har a kasan zuciya.

"Na gane. Na fahimta. Domin ni ba mai kudi ne ba. Saboda ba ni da kudin da zan taimaki rayuwar da kike son yi zuwa nan gaba!"

***
"Ban san me nike ji ta dalilinki ba. Ban taba sanin akwai wata soyayya bayan ta yan uwan da suka kasance duniyata ba. A gaba daya rayuwata, ban san akwai irin abun da ke yawo a kasan zuciyata ba sai da na dora kallona a fuskarki..."

Ya tallabi kanshi da yake sarawa tamkar zai tsage mishi, ya runtse idanuwanshi yana jin yadda zuciyarshi ke dokawa da duk karfin da gangar jikinshi ya bata. A hankali ya ci gaba da fadin

"Ke ce komai na Ruqayya AbdulJabbar! Ke kika canja rayuwata. A kanki na fara sanin dadin kallon da launin kore ke da shi. A kanki na fara sanin akwai wasu kaloli da mata ke so a duniya, bayan baki da na san Safaa da Marwa suna kauna. Da ke na fara raba soyayyar dokunan da na bude idanuwana da shi...Me yasa... me yasa za ki yi mini haka? Me yasa kika zabi ki hukunta ni ta wannan bangaren?"

Hawayenta a wannan karon kara gudu suke a saman kuncinta. Zuciyarta da komai na jikin halittarta wata irin jijjigawa suke suna tuna mata girman laifukan da ta aikata. Idanunta ta runtse, tana tuna yadda Miqdaad Baba Sulaiman ya sallama mata duniyarshi. Sai dai kuma shine silar komai. Shine babban dalilin da ya sa suka tsinci kansu a tsakiyar komai da suke ciki...

________________

Okay... Ka da sunan ya sa ku yi tsammanin zallar soyayya za ku samu a ciki.

Ka da sunan ya ba ku wani tabbaci na ba zai taba zuciyoyinmu ni da ku ba.

Sunan wani jigo ne na yadda kaddara ta hau kan rayuwar malabartan ta yi shimfidarta ta kwanta ba tare da sanin ranar da za ta kama gabanta ba.

Labarin zai dora zuciyoyinmu a wani tsauni mai mugun tsawo. Wanda za mu hau tare da ni da ku da malabartan mu fado, mu ji mu na son mu kara komawa dan ganin yadda labarin zai warware kanshi.

GURBIN SO... a fiction based on a true life event.






#LotsOfLove
#GurbinSo
#Daban ne
Lubbatu Maitafsir🌸💦

GURBIN SOWhere stories live. Discover now