chapter 1

7 3 0
                                        

Ina tsaye a bakin titi INA jiran adaidaita sahu. Ina ta kallon motocin da suke wucewa.
Da naga farar mota sai na bita da kallo ina tunanin zan ga imran aciki bcos amina ta fada min a farar mota ta ganshi last month.
Sai kuma can nayi tunanin idan ma na ganshi me zanyi. Bazai taba kulani ba saboda abinda nayi mishi. Duk da dai ba laifina bane gaba daya amma ya kamata na jajirce akanmu fiye da yadda nayi.
"Allah yasa Na qara ganinshi" na fada a fili. Wayyo imran! don Allah ka dawo wajen Zahran ka.
Ina cikin wannan tunani sai ga mai adaidaita ya tsaya a gabana. "Malama INA zakije" yace. sannan na dawo daga zurfin tunanin da na tafi nace "Hausawa zaka kaini pls". Yace hau. Na hau ya ja mota sai hausawa.
Nazo shiga gida sai naji alamar ana kallona, nayi ta waiwaye banga kowa Ba, na juya zan shiga gida kenan sai najiyo Amina Na qwala min kira " Zahra!". Na juya da murmushina na jirata ta qaraso. Amina tace "daga ina kike Zahra?" Nace "wlh naje na karbo SIWES letter Ne". Tace " oh! Sai yau? Mashiririciya" nayi dariya muka shige cikin Gida. Nace "Dan tayani don Allah nayi Sauri na dora girki. Muka shiga kitchen muka Dora abinci. Sai Amina tace kinsan kuwa yau wa ye ya Mana lecture?" Nace "aa sai kin fadamin." Tace "shikenan kawai" nace wlh sai kin fadamin. Tace "imran" tare da quramin idon tanason ganin reaction dina. Sai na dake Nace "haba?" amma gabana faduwa yake kawai. Tace "wlh, kuma tayi dadi, ya iya bayani, bakiga yanda yanmata suke zancenshi Ba." Nace" don Allah ki dena min zancen shi. He is past to me". Tace "to Allah ya baki haquri" Nace " Ameen". Muka gama girkin, na zuba Mana mukaci. Na zuba wa khadija da Khalifa. Amina tace zata tafi, na raka ta har qofar gida dayake a bayan layinmu suke. Tayi tayi na shiga gidansu naqi. Saboda idan na shiga bazata bari na fito Ba. Mukayi sallama na kama hanya na koma Gida.
Kamar koda yaushe yanzu ma sai da naji kamar ana kallona. Na juya banga kowa Ba, na cigaba da tafiya da sauri kaina a kasa har na Isa Gida.

-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*

Ina ta shiri cikin sauri, don 9:00 nake da lecture kuma na kusa makara, na duba agogon dake hannu na naga 8:30, kuma 30 minutes ce take kaini BUK. Bana so in shiga an riga an fara saboda kana shiga sai idon kowa yayo kanka har lecturer, gashi kuma na tsani kallo.
"Bazaki tsaya ki karya Ba" Umma tace da taga ina saka takalmi. Nace "Umma wlh na makara" tace "Ai maganinki, tun yaushe nake tashinki kikace sai kin qara 10 minute, amma Ba ke kika tashi ba sai bayan 30 minutes. To kudin mota fa?" Nace " Ai jiya 1k kika bani kuma ban baki chanji Ba" tace " to Allah ya kiyaye" nace "ameen".

Ina fita na hau taxi ta kaini qofar Buk oldsite. Na hau bus ta kaini newsite. Ina ta sauri don tafiyar da nisa zuwa lecture hall din.
Ina zuwa na tarar da wasu a bakin hall din nace " ya na ganku a waje? Yau kuma malam Ahmad din hanaku shiga yakeyi?" Sukace "ke wani sabon lecturer ne, mal Ahmad ya tafi karatu. Ance wannan bashida mutunci shine muke tsoron shiga karya yagamu" nace " nidai bari na gwada sa'ata", sai kawai na sa kai na shiga, banfi taku goma da shigaba, naji yace "ke" na juya mukayi ido hudu da Imran, na zare ido saboda mamakin ganin Imran, shima kallo ya bini dashi sai kuma ya kauda kai " don't you ever enter my class late again" ya fada cikin muryar fada da american accent dinshi da nakeso.
Na qarasa Hawa steps din gwiwa a sanyaye. Na rasa me yasa nakejin mutuwar jiki duk sanda naganshi. Ni dai haka ya qare lecture tashi ban fahimci komai ba, don nikam banda kallonshi da sauraron wannan cool muryar tashi ba abinda nakeyi.
Shi kuma ko kallon side dina bayayi. Kawai sai jinai yace "so we can call it a day" Yan class din suka rude da "thank u sir".
Mun fito ni da wasu classmates dina ana hirar lecturer Imran, sai wata fadila take cewa " amma dai Zahra kin auna arziki da be koraki waje ba" murmushi yaqe kawai nayi nai musu sallama na yi hanyar lecture hall dinsu Amina.
Na kirata a waya bata dauka ba tayi min text tana lecture.
Sai nayi hanyar gate don hawa mota. Babu taxi sai bus. Ni kuma bana son kokawar hawa bus dinnan. Sai nayi gefe ina jira wata tazo sai na Hau. Sai na ga wata hadaddiyar Benz ta tsaya a gefe na.
Na matsa a zatona parking zatayi. Sai naga ta qara matsowa, nayi qoqarin ganin wake ciki ta tinted glasses din amma na kasa. Sai naji anyi horn, na rasa me zanyi. Sai akayi winding glass kasa, wa Zan gani? Imran ne ya sha kunu ko kallon barina bayayi, yace" shiga Mu tafi"
ba shiri na shiga kaina a qasa. Sai da ya kaini qofar Gida yayi parking na fita a sanyaye na rufe kofar, yaja motar ina cikin mishi godia. Bai ko tsaya na qarasa ba.

Naabot mo na ang dulo ng mga na-publish na parte.

⏰ Huling update: Aug 05, 2023 ⏰

Idagdag ang kuwentong ito sa iyong Library para ma-notify tungkol sa mga bagong parte!

Labarin ZuciyaTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon