21

773 41 5
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

     by maman shureim
            🌺sad-nas🌺

©Pure Momment Of Life Writers
        _We don't just entertain and educates,we also touch the hearts of the readers💐_




Page 21
I'm so sorry Sis Mubee,i hope you will forgive me my love" ya fad'a cikin muryan kuka.
"Na yafe maka koma menene Ya Atif,amma please kaje gunsu Abba ka sanar dasu cewa ka maidani Ya Atif wlh ina sonka."
"Sis Mubee kiyi hak'uri,bakimin laifin komaiba wlh,please ki dena kuka bana jin dad'in ganinki a hakan nizan tafi."
Rungumesa tayi gam tana ta faman magiya. Muryan Farhan sukaji daga bayansu yana tsaye rai a b'ace.
"Sis Mubee" a hankali ta juyo tana kallonshi babu alaman wasa a fuskarshi dan haka ta tsaya kallonshi amma tana rik'e da Atif.
"Wuce ki koma ciki" ya fad'a mata batare daya kalleta ba.
Cikin sanyin jiki ta kalli Atif shima ita yake kallo sannan ta wuce da gudu zuwa parlour'n Abba inda ta zube a jikin Ummanta tana cigaba da kukan.
  "Atif me haka ka aikata,yanzu dan Allah kai kana ganin ka kyauta wa Abba kenan? Tunda ka fita ya kasa cewa komai wlh yana zaune ne kawai shuru,a ganina koda menene a tsakaninka da Sis Mubee bai kamata kayi haka ba wlh,me yake damunka ne Atif?"
"Kazo a gabansu ka bata takarda me hakan yake nufi,baka ganin girmansu Abban kenan kodai kai kana ganin hakan shine daidai agunka?"
"Atif kayi kuskure wlh,wani laifi Sis Mubee zata maka wanda baka iya jurewa koka kawo k'aranta a gida amma shine zaka sake ta?"
"Imma kuma ba laifinta bane,a kaddara cewa kana da dalili mai k'arfi na sakin Sis Mubee,inaga bai kamata kazo har gaban su Abba ba kafin ka saketa."
"Atif kana da brothers manya wanda zaka iya yin shawara dasu,me yasa baza kaje tagun d'aya daga cikin brothers nakaba ka bada takardan  in yaso su sesu kawowa Abba su mishi bayani inaga aida hakan kayi daya fi sauk'i akan irin wannan abu dakayi babu dad'i wlh."
"Atif dukda dai niba d'an'uwanka na jini bane kuma dukkanmu victims ne akan soyayyar Sis Mubee amma wlh ban tab'a fatan ka saketa ba,dan nasan duk wani kulawa dazan yiwa Sis Mubee kaima zakayi fiye danima tunda tun asali kana sonta sosai,shiyasa nake ganin kayi kuskure akan abinda kayi,yana dakyau ka sake tunani akan abinda ka aikata,Abba fa Mahaifinka ne hakan yasa nake ganin baka kyautaba kwata-kwata."

Tunda Farhan ya fara magana Atif baice komaiba in banda dana sani dayake ta faman yi azuciyar sa.
Shi kanshi se a yanzu da Farhan ya fahimtar dashi kafin ya gane kuskuren sa,dama gurin Yaya Musty yaje ayi komai ta hannusa da hakan zaifi,kuma Abba zaisan cewa na mutunta shi sosai. Hannun Farhan ya rik'o tare da cewa "please Farhan kayi k'ok'arin fahimtar da Abba,wlh banyi hakan dan cin mutuncin suba sedan hakan shine dai-dai a nawa fahimtar. Nagode da shawarar ka,amma please ka sanar da Abba cewa Sis Mubee bata min komaiba wlh,bana so ad'au wani mataki akanta wlh bata da laifin komai nine mai laifi pls Farhan kamin wannan taimakon karka bari a cutar da Sis Mubee please?"
Yana kaiwa nan ya wuce cikin motarshi,ya d'ibeta da gudu ya fice yana share k'walla.
Farhan a tsaye yana mamakin irin wannan lamari na Atif. "What is going on?" ya tambayi kanshi.
Muryan Mubinat ya jiyo tana cewa "Dan Allah Umma kiyi hak'uri wlh banyi mishi komaiba."
  Cikin sauri ya wuce cikin parlour'n, Umma ce taketa dukan Mubinat da hannayenta bibbiyu tana cewa "Duk yadda akayi akwai abinda kikayiwa Atif,dan na tabbata haka kawai Atif bazai d'auki wannan tsatstsauran matakiba akanki wlh da akwai wani abu,bazaki gaya minba ko?"
"Wlh Allah babu abinda na mishi Umma ki kirashi ki tambaye shi wlh ban mishi komai ba,wayyo Abba dan Allah kaba Umma hak'uri wlh Abba bazan tab'a muku k'aryaba Allah banma Ya Atif komai ba wlh babu abinda na sani."
Abba yana zaune duk jikinsa yayi sanyi,ita kuwa Umma se dukan Mubinat takeyi babu sassauci. 
Shureim yanata kuka yazo inda Farhan yake  tsaye a jikin bango idanunsa a rufe yana jin irin k'unar da Mubinat takeji. Tunda yaji irin rantsuwan da Mubinat takeyi ya gaskata maganar ta,dan shima shaidane muddin Mubinat bata da gaskiya to bata tab'a yin rantsuwa akan abu,kuma ita kanta Umma tasan da hakan amma gashi yau tak'i sauraron ta,shima kuma Abba baice musu komai ba.
Shureim ne ya katseshi da cewa "Ya Farhan dan Allah kaje ka karb'i Sis Mubee a hannu Umma,tanata dukanta sosai baka gani ne?"
Kuka sosai Shureim yakeyi idanunsa har sunyi ja,shi kanshi Farhan baiji dad'in hakan ba,se kuma ya tuna da kalaman Atif na cewa karya bari a hukunta Mubee dan bata da laifi,da sauri ya d'auka wayarsa ya kira number'n Atif domin ya sanar dashi amma is switch off,hakan yasa yaje har inda Umma take dukan Mubinat yana magana cikin sanyin murya maiban  tausayi
"Umma please stop beating her like that,you know that she won't lie to you please Umma ?"
"Let me Farhan,ai d'an yau ba'a shaidarsa,duk yadda akayi akwai abinda tayiwa Atif nidai ban yadda ba,domin haka kawai Atif bazai tab'a d'aukan wannan mataki mai zafi hakaba akan ta."
"Haba Umma yanzu idan zanyiwa wasu k'arya se in had'a harda ke? Kar Allah ya nunamin wannan rana Umma,wlh kin wuce komai aguna dan Allah kiyi hak'uri" Cewar Mubinat.
"Tome ya had'aku dashi? Indai ba k'arya kike minba haka kawai zai sake kine Mubinat?"
"Wlh Umma nima tambayar da nake masa kenan dana bishi waje d'azu bayan fitansa,amma wlh bai bani amsaba kuma na gama dukkan tunanina babu aminda ya hadamuma bare ince ko dalilin kenan wlh Umma."
"Mubinat sefa kin gayamin yau,ai ruwa baya tsami banza"
"Please Umma kiyi hak'uri wlh kamar Atif yasan abinda zai faru kenan yacemin kar in bari a  hukunta Sis Mubee saboda bata da laifin komai dan Allah Umma ki k'yaleta haka."
Kunya Umma taji yadda Farhan yaketa had'ata da Allah,shiyasa ta k'yaleta tare da barin parlour'n gaba d'aya.
Tausayin Mubinat ya kamashi sosai harma da Abba da yake zaune kamar ruwa ta cinyesa.
Shureim ya matso kusa da ita yana goge hawayen sa yana cewa "Sis Mubee kiyi hak'uri ki dena kuka"
Rungume k'anin nata tayi sunata kuka,shi kanshi Abba sedaya tausaya musu ganin yadda ta rungume Shureim a jikinta.
Bayan ta share k'wallan ne seta zo gaban Abba ta durk'usa "Dan Allah Abba kayi hak'uri,wlh Allah Abba nidai banyiwa Ya Atif komai ba,kuma bansan dalilin wannan sakin daya min ba,dan Allah Abba kabawa Umma hak'uri bana so tayi fushi dani."
"Bakomai Mamana tashi Ku shiga ciki."
"Nagode Abba" ta fad'a tana mai cigaba da hawaye suka wuce ita da Shureim.
Abba ya kalli Farhan da yake ta binsu Mubinat da kallo,shi kanshi yasan har gobe Farhan yana k'aunar Mubinat kodan irin wannan kallo da yaga Farhan yana binta dashi na tausayawa.
"Farhan shin Atif ya gaya maka wani abune game da Mamana?"
"A'a Abba,baice komai ba,yadai tabbatar min da cewa babu laifinta ko kad'an akan hakan."
"To Amma abin da d'aurewan kai,a sanin dana yiwa Atif gaskiya bazai tab'a yiwa Mamana haka ba,lallai akwai babban dalili mai k'arfi dayasa ya aikata hakan."
  "Hakane Abba,dan Allah kayiwa Umma magana,tad'an sassauta mata."
"Ba damuwa Farhan,dukda dai nasan halin Mamana amma yana da kyau a sake tuntub'an ta daga baya,wata k'ila itama baza'a rasa abinda ta mishi ba."
"To Abba,insha Allah zanyi magana da ita"
"Allah yayi maka albarka Farhan"
"Ameen Abba nagode" sannan ya fice zuwa shashinsa...

Atif kuwa tafiya kawai yakeyi,amma hankalinsa a tashe yake.
  Gidan Yaya musty ya wuce kai tsaye. Ya Musty yayi mamakin ganin Atif da sassafe haka,yanayin dayaga Atif kad'ai yasan akwai wani abu.
"Atif lafiya na ganka haka?"
Cikin wata irin murya mai tada hankali Atif yayi magana "Ya Musty na rabu da Sis Mubee"
"What!"
"Wlh Ya Musty"
"Atif what come's over you da har zaka aikata hakan?"
"Wlh sharrin shaid'an ne Ya Musty,please help me talk to Abba banyi hakan dan b'ata musu raiba sedan dalilina."
"What did you mean by that Atif? Ko menene Mubinat zata maka ashe har zaka iya sakinta bazaka kawo k'ara koda gurina bane?"
Cikin k'walla Atif yace "I'm sorry bros"
"Sorry for your self Atif,dan ka riga daka b'ata mana zumunci,ba Abba kad'aiba harta muma ka cucemu,Mubinat is your sister Atif,wannan shine irin son da kake mata? Bazaka iya hak'uri ka jure duk wani abu da zata maka ba?"
"Is not like that Ya Musty... "Enough Atif,ina Mubinat take?"
"Tana gida,na mai da ita gun Abba"
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un,Atif are you that serious? Meya had'aku haka?"
"I'm sorry but I can't tell you bro"
"What did you mean by you can't tell me? Kana nufi haka kawai ka saketa babu wani dalili?"
Shuru Atif yayi ya kasa cewa komai,Ya Musty ya sake cewa "Kayi min magana Atif meya had'aku?"
"I'm sorry bazan iya fad'a ba Ya Musty"
"To shikenan,tunda kai bazaka iya fad'aba bari ni naje na tambayi Mubinat d'in."
Atif yasan yadda Mubinat take tsoron Ya Musty,dan haka yabi Yayan nashi a baya yana cewa "Ya Musty wlh Sis Mubee bata da laifi,laifin nawane ita kanta bata san komaiba game da wannan sakin dana mata please karka mata fad'a."
"Atif,kaidai ka gama yanke naka hukuncin ko,so karma ka biyoni."
Tsaye Atif yake yana bin mortar Yayanshi da kallo harya fice data gidan...

Vote and comment mana

                                  Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAWhere stories live. Discover now