1-THE RUN IN

1.8K 59 21
                                        


8 WEEKS BEFORE THE WEDDING

Ozumba Mbadiwe Avenue
VI, Lagos.
MGR HOLDINGS

"Baka wasa da ciniki A.jay, nazo nan dan na saka jari bawai na bada rabin kamfanina ba".

Deen ke fada yana zaune akan daya daga cikin kujerun dake ajiye a matsaikacin parlourn dake office din kuma dai dai wacca ke kallon table dinda A.jay din ke zaune akai a bayan desktop dinda ke dauke da tambarin apple, yana rubutu akan keyboard cike da kwarewa. Hasken rana daya soma disashewa yana haskawa akan dogayen gine gine ya hasko ilahirin ofishin ta jikin manyan manyan gilasan da curtain dinsu fari kal ke a bude.

Batareda ya dago ya kalla Deen ba yace, "Idan bakaso, sai ka barshi"

Deen ya saki y'ar siririyar dariya yana dauke idonsa daga kan fuskar A.jay dake a daure ya tattarre girarsa waje daya kafin ya sake daurasu akan file din dake gabansa yana kara bude shafikan takardun dake ciki. Ya girgiza kai yace

"Kasan bazan barshi haka ba amma kaso arba'in daga sabon project din kamfanina in exchange for funding and logistics, that's steep, kanada tsada da yawa".

A.Jay ya mika hannunsa kan table dinsa mai karancin hayaniya ya dauka takardun dake saman files dinda ke jere cikin tsari yana dubawa.

"It's a fair exchange, zaka samu international access ta hanyata, jiragen ruwa da kuma tsaro, kamfaninka zai amfana, ni kuma zanci riba, it's a win win"

Ya karasa fada lokacin daya kai hannu yana daukar pen na Montblanc daga ma'ajiyarsa ya saka hannu akan takardun.

Deen ya shafa kwantaciyyar sajen dake kan fuskarsa alamar tunani, abunda su duka biyu sun san cewa tuni zuciyarsa ta gama karkata da amincewa yace

"Toh, na amince, amma inada sharadi, banaso wani daga gefenka ya saka hannu idan na samo sababbain masu zuba jari".

Sai alokacin A.jay ya dago da idanuwansa masu zurfi da kuma nisa, nisan da baya bari ka iya karantar abunda ke zuciyarsa ya dora su akan Deen. Ya kallesa na d'an sakanni kafun ya gyada kansa yana buga yatsunsa biyu akan table din ahankali, wani abu daya zame masa jiki a duk lokacin da yake son nuna ikon dayake dashi a kowane lokaci yace

"Done"

Deen ya saki murmushin rashin yarda, yana kara girgiza kansa dan yasan A.jay cikinsa da wajensa kuma ya sani sarai ba hakan ne zai kasance ba. Maganar daya fada kaman ta wuce ta sassanyar iskan da na'urar A.cn dake ofishin ke fitarwa ne. Shi Kansa yasan abunda yake fada bazai ma yiwu ba.

"Kai wannan mutumin akwai keta"

"Ana yawan fada" A.jay ya bashi ansa lokacinda ya mike daga kan kujerar sa yana takawa zuwa ga katuwar shelf din glass dake manne a bangon office din ta hannun dama, cike take taf da littafai na kasuwanci da folders kala kala dake ajiye da tsantsar tsari. Ya mika zara zaran yatsunsa yana ciro folder daya kafun idanunsa su sauka akan wani katon frame din zane dake daukeda fulawowi masu launi kala kala mai haske da annuri. Jar kala, dorawa kamar hasken rana. shudi mai haske kamar sararin sama, kalar danyen haki da dai sauran su. Furanni ne acike a ko'ina a zanen, kamar wani lambu.

Ya kara tamke fuskar nan tasa dan ba karamar rigima sukayi da Deen ba daya siye sa a wata tafiyar kasuwanci da sukayi kasar France kuma dan takaici da tsada sosai ya siyesan kuma bai dire sa ko'ina ba sai office dinsa dan wulakanci. Kalaman Deen suka dawo masa akai lokacin da yace masa bazai saka masa shi a office ba saidai a cire

"Kana bukatar abu mai kala a office dinnan naka marar rai, kamar dai yanda kake bukatar kala a rayuwarka, haske kake bukata da zai ceci zuciyarka daga wannan duhun daka lullube kanka dashi"

AMOOT FEIK ( I die for you ) Bağımlısı olacağınız hikayeler. Şimdi keşfedin