Cikin iko na Allah suka iso asibitin inda Umma ta mika mishi dubu guda ba tare da ta tsaya karban canji ba tayi gaba,me adaidaita yana "Hajiya canjin ki"amman ina Umma tayi gaba,inda Zuhra tace mata suke ta nufa inda kuwa ta tarar da su a tsatsaye ita da Mansoor hankalin su a matukar tashe,idanun Zuhra sun yi luhu luhu tsaban kukan da ta rizga da ganin Umma kuwa ta zo ta rungume ta,tana sakin sabon kuka.

"Ya isa Zuhra bar kukan haka nan,ba ga ni na iso ba,ina ita kawar taki ta farfado?Me ke damun ta ne ma?Me likitoci suka ce?Tana raye ina?"Umma ta kare muryan ta na rawa don daurewa kawai take yi amman kuka take son fashe wa da shi.

Cikin hawaye Zuhra tace "Umma likitan da ya shiga har yanzu be fito ba,ba mu san halin da take ciki ba,Umma tsoro nake kar wani abu ya samu Goofy angel,saida nace mata ta koma gida kar ta shigo makaranta amman taki ji saida ta shigo gashi yanzu abunda ya faru,na sani daman ba za su taba kyalle ta ba,mugaye azzalumai"ta kare tana goge hawayen ta.

Kan Umma ya kulle hakan ya sa ta kalli Zuhra domin bata fahimci inda zancen nata ya dosa ba "kika ce kar ta shigo,su waye ba za su Kyalle ta ba,me ta musu kuma akan me ya sa?Me ma suka yi mata?"shine tambayar da Umma ta jero wa Zuhra ta budi baki da niyar amsa ta ke nan suka ga fitowan Doc hakan ya sanya Zuhra fasa fadan abun da tayi niya inda suka nufe shi da sauri

"Sannu Doc ya jikin nata?Ta farfado kuwa?Hope tana raye babu abunda ya same ta ko?"Zuhra ta kare a raunane kai likitan ya girgiza yana dan murmushi sanann yace "mu je office dina sai na muku bayani,ince yan uwan ta ne ku?"

"Eh likita nice Mahaifiyar ta wanann kuma yar uwar ta ce"kai kawai ya gyada musu tare da yin gaba inda suka mara mishi baya,da sallama suka shiga office din inda ya nuna musu guri tare da cewa su zauna zama suka yi inda har suna hada baki gurin tambayan

"Doc ya jikin nata?Allah ya sa ba wani babban abu ke damun ta ba"dan murmushi yayi sanann yace "ku kwantar da hankalin ku tana raye bata mutu ba,and for now I can say she is out of danger"wata wawiyar ajiyar zuciya suka sauke a tare sanann Umma tace "Alhamdulilah Allah na gode maka,amman likita wai me ke damun ta ne?Lafiya kalau muka yi sallama da ita ta tafi makaranta sai kira na gani wai ta fadi"Umma ta kare tana share hawaye.

Dan shiru Doc yayi sanann yace "ku kwantar da hankalin ku ba wani serious abu ne ya same ta ba actually she panicked and went into a shock state but we shall observe her more when she's conscious don for now kam ba mu ga komai ba,dole a jira sai ta farka sai a gwada a ga ko akwai wani internal injuries"ya kare yana kallon su.

Kallon Zuhra Umma tayi sanann tace "wai me hakan da ya ce yake nufi Zuhra?"dan murmushi Doc yayi sanann yace "Hajiya ina nufin ba wani abu ne ya samu yar ki ba,firgici da tsoro ne ya haura mata wanda yayi sanadiyar suman nata,kila ta ga wani abun da ya bata tsoro wanda bata yi zaton gani ba,ko ta ji abunda ya gigita tane har yayi causing ta samu din,amman bayan nan ban jin akwai wani matsala don ko jinin ta be hau ba kuma be sauka ba so Alhamdulilah babu matsalan Bp,sai mun jira ta farfado sai a mata gwaje gwaje sai mu gani ko akwai raunukan cikin jiki"daga haka yayi musu sallama don yana da duba wasu marasa lafiyan.

Jiki a sanyaye Umma suka fito daga Office din inda suka nufi dakin da Sabeehar ke kwance,shiru Umma tayi tare da zuba mata idanu bakin ta ma yayi nauyi bare ta tambayi miye yayi causing shock ya haura mata?Me kuma ya faru,kallon Sabeehan kawai take yi yanda take sauke ajiyar suna nan zaune a dakin Umman na rike da hannun ta ta farka,inda a zabure ta mike zaune tana ihu tana kuka cikin ihu take fadin

"Inalilhi wa ina ilaihi raju'un Zuhra Wlhy tallahi ba ni ce a video din nan ba,Wayyo Allah na miye na yi da na cancanci haka?Waye ke neman rusa mun rayuwa ya zubar mun da mutunci na,Zuhra in Umma ta gani ya za ta yi,me za ta ce"ita kadai ke ta sumbatu masu taba zuciya tana ihu tana kuka tana salati kamar wata me hauka sabon kamu,inda da sauri Zuhra ta fita tana kuka don kiran likita Umma banda hawaye babu abunda take yi tana tofa mata addua inda suna dawowa numfashin ta na kuma tsaya wa cak,ta kuma sulale wa kan gado sumammiya.

 A SIMPLE DARE (WASA DA SO)Место, где живут истории. Откройте их для себя