Faisal ne yakira shi yana daga wayan yace"ɗan rainin hankali ai sai kazo kadaukeni a airport.

Makullin mota kawai ya zira jiki ba kwari yatafi ɗaukoshi koda ya isa airport ɗin Faisal jirginsu ya jima da sauka yana zaune yana karanta jarida yasame shi fuska ba walwala yana isa gareshi hannu kawai yamika masa sukai musabaha,ya daukar masa jaka batare da yakuma tamka ba,shima Faisal bedamu da sai ya tanƙan ba yabiyo shi a baya har zuwa inda ya faka motar ya bude back site yasaka masa jaka kafin ma ya zagayo yashiga ciki har Faisal yashiga ya zauna yana ƴan danne danne wayan sa,saiAhmad yatada motar sannan yace"mu je gidan naku akwai abunda b
Nakeson dubawa kafin ka kaini masauki,yanda yake jan motan shi ze shedama ransa a ɓace yake saida sukai tafiya mai nisa sannan ya ɗan kalli Faisal da gefen ido yace"Broo ina cikin tashin hankali gami da ɗauke Eashow da akai wallahi bansa inda zan saka raina inji daɗi ba itace mahaɗan rayuwata inda ba ita bani itace wacce zuciyata ta aminta zata rayu da ita,bansan yaushe na fara sonta ba saide kawai jina nayi tsumdum cikin tabkin begenta nayi nitso cikin kogin sonta da kaunan ta,ban taɓa yin nadama Auren wucin gadi danace ba sai yau broo bansan ko zata yarda ta zauna dani ta amsheni matsayin mijinta uban ƴaƴan ta ba,saide inajin a raina matukar Eashow ta juyan baya zaku iya ras...rufe masa baki da Faisal yayi ne ya hanashi karasa abunda ke ranshi.

Daidai sanda suka isa bakin get din tangamemen wani gida daya wadatu da shukan fulawowi masu shegun kyau mabambanta launuka,tun daga bakin get din Faisal yasoma bin gidan da kallo gidane na gani na faɗa gini kaman baza'a mutu ba.

Maigadi yabude masa ƙofa kaman yanda yasaba yashiga da motan ciki yayi parkin sannan suka fito tare da Faisal zuwa yayi kaman ɗazu ze fara wannan zuban nasa Ahmad yabarshi yayi gaba juyawa yayi da nufin komawa bakin get din Faisal yace dashi"aikin ka yana kyau Malam Barau saurin juyawo Baba maigadi yayi yana kallon sa da mamakin ambatan sunan sa da Faisal din yayi"saide ban shede ka ba Yaro?yace da yana zazzaro ido irin ta mara gaskiya.

Takowa Faisal yashiga yi a hankali yayin da zuciyar Baba maigadi kaman tayi bundiga ta faso kirjin sa yakeji,daura hannun sa a ƙafadan sa yayi suka shiga takawa a hankali zuwa bakin get din"har tsawon wani lokaci kadauka kana aiki dasu?a zabure baba maigadi ya juya yana kafe Faisal din da ido dan tambayan tazo masa abazata.

suwaye sukazo suka tafi da ita?kafadamun tun muna mu biyun mu karka bari Ahmad ya waiwaye ka dan baze maka daɗi ba,yanzu haka yana cikin tashin hankaline amma kabari ya tsaye da hankalin shi guɗaya ya waiwaye ka sunan ka Sorry dan baze daga maka ƙafa koda wasa ba, bama kai ba duk wanda yake da hannu cikin wannan abun baze bari ba.

Idan baka taɓa ganinsa a bakin aiki ba nasan ba zaka rasa jin labarin sa ba,idan ya dauki aiki baya  hutuwa harsai yagama,ya kake ganin idan aikin yashafi iyalin sa,tamkar mayunwacin zaki daya kwana da yunwa ya kake tunanin gamuwarsa da namun daji.

Take jikin wanda aka kira da Malam Barau ya dauki ɓari take wani irin zuba ya shiga karyo masa"ina kuka kaimun Mata?suka tsinkayo muryan sa tsaye yake a bayan su ta haɗe fuskan nan tasa kaman hadarin gabas kaman betaɓa yin dariya ba arayuwar sa.

"wallahi Allah na rantse ɗaga masa hannu yayi fuskar nan tashi mutur yace"zaka fadamun ne ta lallami kosai nabi dakai ta inda yadace?"wallahi kafin yakarasa fadan abunda yayi niyar fadin yaji saukan wani bahagon naushi kafin ya ankare yasake kai masa wani a takaice de kusan haukace musu Ahmad yayi tun yana narkan Maigadin nan Faisal yana tsaye ya zuba masa ido hartakai saida ya magantu dakyar de ya iya dakatar dashi daga dukansa dayake,amma fa bawan Allah Malam barau ya daku dan koda Faisal ya karbeshi daga hannun Ahmad din zube musu yayi kaman kayan wanki a wajen,da kyar ya bude bakin sa yace"dan Allah yallaɓai kaimun rai wallahi idan nafaɗi wani abu daya dangance su kasheni zasuyi ina da ƙananun yara dan Allah ka tausayamun.

"Amma sanda ka karɓi aikin ai bakayi tunanin ita wacce kayi musu hanya sukazo suka tafi da ita din itama ɗiyar wasu bace ba,kaman yanda bakason rasa naka yaran ko ɗaya daga cikin su haka ita ma nata iyayen ka kaddara ace yau ɗaya daga cikin yaranka aka nema aka rasa lokaci ɗaya wani hali zaka tsinci kanka ciki?

Shiru Faisal yayi da maganan da yake dan shi Ahmad ji yake kaman xuciyar sa zatayi bindiga saboda fushi shi Faisal ɗinma haushin sa yake ji hanashi dukan mutumin dayayi jiyake kaman ya shaƙeshi harsai yadena numfashi sannan ya barshi.

" kamun rai wallahi kudi suka bani Naira dubu ɗari kasan zuciya ba ƙashine da ita ba,ganin kuɗi haka masu yawa yasani ce musu suzo ranan ita yau za'ayi bikin zagayon ranan haihuwar ɗiyar ta Alhaji shine sukazo kuma akaci sa'a Alhaji ba lafiya kakaishi Asibiti ya kare maganan sa yana ta muzurai na rashin gaskiya.

Zaune yake dafe da kansa da dukkan hannuwan sa kallon sa Dr Jamal yayi yayi ƙasa da murya cikin nuna girmawa gareshi yace"yallaɓai gaskiya kana bukatan hutu sosai rashin bacci da baka samu kwana biyu da dare harma da rana gashi kasaka damuwa sosai a ranka yana neman barazana da ƙwakwalwanka,shi yajawi maka wannan ciwon kan idan baka rage damuwa ba ƙwaƙwalwanka zata iya buwaga zaka iya kamuwa da ciwon ƙwaƙwalwa ako wani irin lokaci so kana da,, bukatan hutu a karan kanka dama ƙwaƙwalwanka baki ɗaya.

"Ya'isa nace ya'isa ya faɗama likitan a fusace sai kuma ya sassauta muryarsa yace inajin kaman hayaniya kaman ana kiran sunana wani lokaci kuma nakanji kunnuwana kaman suna amsa kuwa.

"Kayi hakuri ranka yadaɗe amma gaskiya kana bukatar hutu ko dan saboda lafiyanka, idan kacigaba da taƙurama kanka da yawan tunani da rashin samun wadataccen bacci za'iya samun matsala dan....hannu ya ɗagawa likitan yana cewa"bakomai na gode zaka iya tafiya likitan badan yagama yimasa bayani ba haka ya hakura ya dan bayan da zeyi ya tafi yana sake jaddadama Goga da su kula da shi suyi koƙarin ganin sun dauke masa hankali daga shiga damuwa.

Bayan barin likitan wajen ya jinjina jikin sa da kugera dayake kai yashiga faɗin"bade haukacewa zanyi ba,ina ina be kamata na haukace batare da ganin faɗiwar baƙiyina ba be dace ƙwaƙwalwata ta kamu da ciwon damuwa banga tsoro a cikin idon Sanusi ba,ya Allah ina rokon ka daka aramun tsawon rai naga rugugewar wannan ɓakar alkarya ta azzaluman irin Surajo da Sunusi ba ya rabbi kaƙubutar mun da ƴata dake hannun su yarahman bakarka bama kowani mugu daman ya cutarmun da ita,Allah kasaka ɗauke mun ƴa dasukai yaxamana silar rushewar su Ya Allah yaceci ƴaƴan Al'umma daga zaluncin waƴan nan bayan naka.

ANAN NAKAWO KARSHEN LITTAFI NA ƊAYA,KUYI HAKURI DAJINA SHIRU DA KUKAI TSAWON LOKACI KUNSAN JIKI DA JINI,MASU KIRANA TA WAYA DA MASU YIMUN MAGANA HAKA DUK NAGODE SAI MUN HADU A KASHI NA BIYU KUMA NA KARSHE DAN JIN YA.

Zata kaya tsakanin Daddy Ishaq da Alhji Sunusi.

Shin Anna na haduwa da Daddy Ishaq da yaran ta?

Ahmad nayin nasara wajen samo Aisha kowa ya Auren nasu ze kasance bayan ta ƙubura daga hannun su Allah sunusi,duka kubiyoni a littafi na biyu dan jin karshen labarin taku har kullum.

ZAHRA ALI ABDULLAHI
   

  Alkalami 🖋yafi takobi.⚔

ALLAH YASA MUDACE

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 05 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now