Dan dariya Zuhra tayi tare da yi mata kiss a kumatu inda Sabeeha tayi saurin tureta "matsa dallah don't smash my make up"dariya Zuhra ta kuma sake wa sannan tace "bakauyiya sabida anyi light make up yau shine har ake ture kiss din Zuhra,yayi miki kyau"

Riko ta Sabeeha tayi sanann tace "dallah to in kika bata kwalliyan wanda aka yi domin shi be gani ba fa?"baki bude Zuhra ke kallon Sabeeha kafin tace "enyee yam matan Umma is finally in love 😻 dole ki ce mun haka,Soyayya dadi kawata Allah ya baki FIK mu sha biki"

Cike da jin kunya Sabeeha ta amsa da "Ameen"tana dariya itama Zuhran dariya ta sanya tana matukar ji wa Sabeeha dadi kallon ta Sabeeha tayi a hankali tace "Goofy angel daman haka ake ji in ana son mutum?"

"Bani labarin yanda kike ji?"Zuhra ta tambaya tana zama kusa da ita,dan fari Sabeeha tayi da idanu sanann tace "ni ban ma san me zan ce ko ya zan miki bayani ki fahimta ba,Zuhra Wlhy ko motsi nayi Shi nake tunawa,komai zan yi yana cikin zuciya ta,fuskan shi kuma na idanu na,Zuhra sai ina ji kamar ban da lafiya ko wani abu zai same shi in ba muyi magana ba,I just don't know how?Where?or when?Nayi developing feelings me yawa akan shi,Wlhy ni kai na at times har mamakin kaina nake yi ashe haka daman soyayyan yake?Sai na ji kamar na fada masa sai na kasa,Zuhra zuciya ta sai tayi ta azzalata in kira shi nayi masa magana ashe wai duk son shi nake yi"ta kare tana dariya kamar wata karamar yarinya.

Kallon ta kawai Zuhra ke yi ta ma kasa cewa komai banda gode wa Allah da take ta yi a ranta yau Sabeeha ce da bakin ta yake cewa wai ta kamu da soyayyan wani ashe za ta ga wanann ranar a rayuwar ta,ashe dai mahakurci mawadaci,ta kuma ji dadi da Allah ya sanya wahalar FIK be tashi a banza ba,gashi yanzu da yayi hakuri ta fada son shi,ta sani babu wanda zai kai Sabeeha sa'a da dace in ta samu FIK a matsayin miji,domin she is very sure zai kula da ita fiye da zaton me tunani.

Ganin Zuhran tayi shiru tana ta kallon ta ne ya sanya ta cuno baki tare da snapping fingers din ta a kan face din ta "Hellooo Goofy angel,ina ta magana kin yi shiru,ko dai na fada son da ta yawa ne?Maybe I overreacted ko?"ta kare tana cuno baki.

Kai Zuhra ta girgiza a hankali tace "ko daya my love babu wani overreacting din da kika yi,I'm very sure soyayyan da yake miki ya fi wanda kike masa sau dubu dari biyar,am just so happy for you,I can't wait to see how this your love story will end,after long years of waiting Goofy angel dina is in love dole nayi sadaka,Wlhy ba karamin perfect couples za ku zamo ba,and your babies za suyi masifar kyau,Allah ya tabbatar da Alkhairi a tsakanin ku,and Allah ya sa maganar da zai miki cewa zai yi turowa gida yake son yi a masa tambayar Auran ki,da mun gama exams mu sha biki"Zuhra ta kare da tsantsan farin ciki,inda dariya kawai Sabeeha ke mata ita kan ta ta rasa wani irin farin ciki take ciki,sai take ta cewa Allah ya sa maganar Auran zai mata domin da gaske har cikin zuciyar ta ta kamu da so da kaunar shi wanda ita da kan ta bata san a yaushe ta fara son shi ba,but how she feels at the moment is like she couldn't live without him even if she wanted to, wato ashe ba fault din yanmata bane idan sunce ba za su iya rayuwa ba tare da abinda suke so  ba ashe this is exactly how they feel lallai turawa sunyi gaskia dasukace love is a very strong weapon.

Ringing din wayarta ne ya katse musu hirar da suke yi  number ne tagani kan wayar hakan ya tabbatar mata driver'n FIK ne dauka tayi inda driver cikin ladabi kamar tana ganinsa ya gaisheta sannan ya shaida mata yana waje, jin haka Zuhra cikin sheqiyanci ta sake  feshe ta da turare tana cewa "Kawata kin san  amarya saida turare"kai Sabeeha ta girgiza tace "ke nikam rabu dani sai na dawo" cike da zolaya Zuhra tace "ko dai  nayi rakiya ne? Na kalli yanda sabin shiga a soyayya suke yi"Sabeeha ta galla mata harara tare da cewa "toh in kina wurin taya zan fada masa ina son shi ke dai yi zaman ki Hajiya ta zan baki labari in details"

Baki Zuhra ta turo sanann tace "Allah ya isa ko A in kika cire baki fada mun ba,bari na dauko hijab na raka ki kofar gida to tunda kin ce ba zan biki ba"Sabeeha ba ta tsaya kula ta ba takalmi ta sanya don in tace za ta biye wa Zuhran sai su kwana su tashi don ta ga alamun yau tsiyar Zuhran kan ta ya tashi,saida suka biya dakin Mama inda Sabeeha ta sanar da ita za taje ta dawo,inda Mama tayi mata Allah ya tsare hanya har tana tsokanan ta tayi kyau,yau ranar farko da ta gan ta da kwalliya,dariya Sabeeha tayi tace "kai Mama"inda Maman tace "yoo ai Gaskiya ce kila surikin nawa ne ya zo,to a gaishe shi a kuma dawo da wuri don Allah"da haka suka rabu tana dariya wa Zuhra wai taya Mama tayi saurin gano ta haka,har kofar gida Zuhra ta raka ta inda cike da farin ciki tace

 A SIMPLE DARE (WASA DA SO)Where stories live. Discover now