"Umma Wlhy baki san halin shi bane wlhh kaf makarantar mu ba wanda be san su ba,don suna da kudi sai suke ga komai suka yi daidai ne,Umma shine wanda ya watsa mun ruwa kuma don nayi magana ya nemi dake mun duwawu na,shine ni kuwa na wanka mishi mari,Zuhra da kan ta tace ba mutanan kirki bane,sanann babu wnada ya isa ya taba su ba su rama ba"ta kare tana bata rai.

"Har yanzu kin ga ya rama?"ta ji Umma ta jefo mata tambayar,kai ta girgiza a hankali alamun a'a,kafin Umma ta daura da fadin "kin ga hakan ya nuna mutum na iya canzawa a ko wani lokaci in Allah ya so,zaki ga me aikata aikin yan wuta ma Allah ya shirya shi gab zai mutu ya koma aikata na Alkhairi ya mutu ya kuma shiga Aljanna to miye Allah baya yi?Sannan kar ki manta yaron nan Dan masu kudi ne tare da connection kika dalla masa mari a tsakiyar makaranta amman ya dawo yana bin ki tare da neman yafiyar ki,inda yana da nufin cutar da ke zai miki irin hidimar da yayi da ke da ni ne?"ganin tayi shiru ne ya sanya Umma cewa "ki tashi ki je kiyi alola ki kwanta kina da makaranta gobe kin kuma ce da ni kuna shirye shirye ko kun ma fara text yake ko test"dan dariya tayi tare da mikewa tace "test ake cewa Umma saida safe"har ta kai kofa ta ji Umman ta kira sunan ta,hakan ya sanya ta ja ta tsaya

"Sabeeha a kullum ina so ki sani rayuwar duniya karamin guri ne,sanann Allah yayi mantuwa don Samar wa yan adam sauki a duk sanda suke cikin damuwa kamar yanda yayi hawaye da dariya,shi rike mutum a rai ba halin musulmin kwarai bane,sanann duk Musulmi an san shi da tausayi yafiya tare da maida damuwar wanin shi nashi,sanann yawan fushi da fada ba shine karfi ba iyakan me karfi shine wanda ya iya mallakan zuciyar shi a yayin da yayi fushi Hadisi ne guda,ina me rokon ki da ki sassauta wa zuciyar ki tare da koya wa kan ki hakuri da yafiya tare da manta abu in ya same ki,Ubangiji ya tashe mu lafiya Allah kuma yayi miki Albaraka"ta kare tana mike wa tare da karkade gadon ta don kwanciya bacci,jiki a sanyaye Sabeeha ta je tare da yin alola sanann ta shige daki inda tayi kuri ita kadai tare da zuba wa guri guda ido tunanuka da yawa na kai kawo a cikin ran ta,jikin ta yayi sanyi sosai da maganganun da Umma ta fada mata,saidai ta rasa me ya sanya take jin tsantsan haushin FIK,sam babu karya ko cutar wa a cikin maganganun Mahaifiyar nata amman bata jin abunda Faizaan yake nema zai samu a tattare da ita,ba shi ba a rayuwa bata jin akwai na mijin da za ta fada soyayyar shi,ta tsani maza!!Haka zalika ta tsani soyayya balle kuma aure,kan ta ya kulle don Haka kawai ta kasa yarda da FIK ko da na second guda,ta rasa me ya sanya Umma aminta da shi tare da yarda da shi lokaci guda haka?haka tayi ta juye juye ita kadai tana tunani inda za ta bullo wa matsalan FAIZAAN tun kan ya hada ta da Mahaifiyar ta kamar yanda ya hada ta da kawar ta don ganin take taken shi ke nan,sam babu Alkhairi a tattare da shi haka jikin ta ke bata,tunda suke basu taba fada da Zuhra ba saida ya shigo rayuwar ta,sanann yanzu yana son hada ta da Mahaifiyar ta abinda kuma ba zai taba yuwa ke nan ba,haka wannan Daren tayi ta tunani ka har bacci ya dauke ta tana ganin irin kiran da yake tayi mata inda taki dauka don ba karamin haushi ya kara bata ba yau.

******************************

Sallama tayi wa Umma cikin sauri ta fice daga gidan domin yau za su fara C.A so tana son isa da wuri,inda ko ba karamin kyau tayi ba don sanye take cikin wata gown din Atampa yellow da sky blue a jikin atampan inda aka mata dinkin gown me dogon hannu,duk da ba wani style aka sanya wa rigar ba amman ba karamin kyau yayi mata ba,don ya mugun zama mata a jiki,face din ta fayau kamar kullum banda kwalli da man lebe da ta sanya wanda sai sheki yake yi kuwa babu komai a face din nata,sai ta murza daurin ture inda ya kafu kuwa a kan ta gashin da ta parka ta daure da ribbon sai daurin ya zauna mata daram a kai,madaidaiciyar sky blue veil ta yafa a kan ta sai ta fito kamar wata sabuwar amarya Masha Allah da takalmin ta ma sky blue flat shoe,cikin sa'a kuwa ta samu abun hawa inda suka yi ciniki sai makaranta.


A bakin ajin su ta hadu da Zuhra inda ko ba a fada mata ba jiran ta take yi,rungume ta Sabeeha tayi sanann tace "good morning goofy angel,saura kadan in ce a aje ni a hostel na dauka baki fito ba ai"dan dariya Zuhran tayi sanann tace

 A SIMPLE DARE (WASA DA SO)Where stories live. Discover now