"Ya isa haka kukan bashi fa da amfani Zuhra tunda aikin gama ai ya Riga da ya gama,duk na san komai tunda Ai tare da ke muke cikin gidan nan,kin san kowa da irin fahimtar shi,so kar ki dauki maganganun da ta fada miki ki kai su zuciya har ya dame ki,Sabeeha Aminyar ki ce ko na ce yar uwar ki,yanda kike fadin kina kaunar ta na tabbatar ke ma tana kaunar ki fiye ma da hakan,ke dai shedan ne da bayi son zaman lafiya,abu ne karami amman ya ya hura ya zamo babba don a samu tashin hankali,yanzu dai kiyi hakuri ya sanya tun farko na so da kin sanar mata tunda kin ce mun tun farko bata kaunar yaron,kila da duk hakan be faru ba"

"Mama sabida Allah Sabeeha haka za tayi ta zama ke nan har karshen rayuwar ta ba aure saboda kawai tana tsoron kar abunda ya faru da Adda Nawwara kar ya maimaitu a kan ta?Ashe da ko haka ne nima ko inda maza suke ba zan kalla ba saboda halin Mahaifi na,Mama Wlhy babu abinda nake so a duniyar nan irin in ga Sabeeha tayi Settling down nima zan fi samun kwanciyar hankali,ina tausayin kan mu ina tausaya mata,domin marainiya ce daga ita sai Umman ta,da rayuwar kuncin da take kullum gidan su ba gwamma tayi Auran ta samu yancin kan ta ba,Wlhh Mama FIK ya canza daman abunda ya sanya ta tsane shin matsala suka samu har ta mare shi,Wlhy in kin ga yanda yake rawar kafafuwa akan ta sai kin yi mamaki,sai yanzu na gane harda karyan mutane in suna fadan halaiyan sa,amman rashin kirkin nashi be kai haka ba,ke dai sheda ne zuwan shi gidan nan a sau nawa don kawai na shawo masa kan Sabeeha,Umma ga kyauta ga hakuri Wlhy da wani ne ta mare shi sai yanda karfin shi ya kare,kila sai ya sanya an daure ta tunda dan gidan masu kudi ne na ban mamaki,amman sam be yi hakan ba,wallahi Mama Faizan irin shine ko wace mace ke son samu,daga shigan shi rayuwar Sabeeha farin ciki da walwalan da ya sanya ta har ban san adadi ba,tsakani da Allah Allah da kanshi ya hallici soyayya sanann Aure sunnah din Annabin mu ne amman ke Sabeeha kiyi depriving kan ki wa wanann right din akan me?Ko kundin dokar kasa ma ta bada daman ka so kuma a so ka,amman na rasa gane wanann mentality na Sabeeha"Zuhra ta kare tana Jan hanci.

Dan shiru Mama tayi sanann tace "duk na ji na kuma fahimta kamar dai yanda na fada miki ne shedan ne a tsakanin ku shi daman yana bakin ciki da duk wani aikin Alkhairi,Allah ya ga niyar ki don haka ki yi hakuri ki bar kukan nan haka,ki nutsu hankalin ki ya kwanta itama nata ya kwanta sai kuyi magana na fahimtar juna,na tabbatar itama Sabeehar bacin rai ne amman sarai ta san ba za ki taba iya cutar da ita ba,tashi ki wanko idanun ki kar ki sanya damuwa a ran ki babu kawancen da ba a samun matsala ba ma kawance ba duk zama aka ce ai daman zo mu zauna watarana kuma mu sa'ba do kar ma ki sanya abun a ran ki kin ji ko"kai Zuhra ta gyada tare da mikewa don wanko idanun nata wanda har yanzu ran ta bace yake da maganganun da Sabeeha ta mata,yau ta dauka tana da wanann alfarman a gurin Sabeeha amman wai har ita take kira da Shashasha kawai don ta baiwa FIK number din ta,kai ta girgiza tare da iban ruwa a mo'da ta wanke fuskan nata sanann ta shige dakin ta don har ta ji kan ta ya fara Sara mata,jakar tsarabar da FIK ya kawo a baiwa Sabeehar ta gani aje alamun Sabeehar bata dauka ba ke nan,hakan ne ya sanya ta mike wa tare da sanya hijab ta dau jaka sanann ta fito,dakin Mama ta shiga

"Daga wanko idanu sai kuma na gan ki da Hijabi ina zuwa kuma?"Mama ta tambaya tana yar dariya, "Mama gidan su Sabeeha zan je yanzu in dawo tsarabar da ya kawo zan kai mata,kin ga ba nawa bane tsautsayi kar ya sa Abba ya shigo ya gani"

"Munafuka da Uwar ta uban me ake boye mun ni da gida na don iskanci wai kar a bari na gani"caraf suka jiyo maganar Abba a bayan su,daman Zuhra a sama take hakan ya sanya ta saurin bashi amsa don ta san in tayi shiru Mama ba iya tanka shi za ta yi ba.

"Abba lah ashe ka shigo to sannu da zuwa,kai Abba ba fa komai bane daman sako ne aka bani na baiwa Sabeeha to ta zo ta tafi ta manta da shi shine nace bari na kai mata kar ka gani kayi wa Anty Amarya sha'awar sa ka ga kuma abunda ba na wa ba balle marainiyar wayon nata Mama na balle ace za a kai mata"ta kare tana bude mishi kyakyawar paper bag din.

Idanu yayi saurin zaro wa sakamakon kayan dukiya da ya ci karo da su,wanda be taba ganin irin su ba,bakin shi har na rawa gurin fadin "Zuhra wanann din wai duk na wace ma kika ce?Ko naki ne kin fara yin abun arziki"ya kare yana washe baki tare da kokarin saka hannu don ciro wata kwali da ya gani wanda be san ta mecece ba amman ta tsole idanun shi.

 A SIMPLE DARE (WASA DA SO)Where stories live. Discover now