Dan kallon ta Sabeeha tayi tana yaba kyan hali da hakuri irin ta Mahaifiyar ta kafin ta sauke ajiyar zuciya tace "Umma kiyi hakuri don Allah,nayi laifi da kike kira ban tsaya na saurare ki ba Wlhy raina ke bace lokacin,haba Umma mutanan nan ke ce kadai ke kaunar su amman Wlhy su kam babu kaunar mu ko tausayin mu a tattare da su,Umma yau shekaru na nawa a duniya?Kwayan shinkafa sun taba bada wa saboda a dafa wa Marainiya in na ci za su samu lada?Umma ciyar da Marainiya lada gare shi kamar yanda taimakon Bazawara ko matar da ta rasa mijin ta ko kuma miskiniya aka ce kamar mutum ne da yayi Jahadi sabida Allah,ladan da duk wanda ya ciyar da mutanan da na lissafo zai samu,cikin akwai wanda ya taba kwadayin samun wannan ladan?Umma a ma bar maganar lada wanann daman sai me rabo da tsoron Lahirar sa ya damu da wannan matsiya na na Diyar dan uwan su da ya mutu ya bari,ke kuma na Matar dan uwan su da ya mutu ya bari da yara ba mu cancanci taimako a gurin su ba?Umma ko daidai da ruwan sha akwai wanda ya taba ba mu ko ya tambayi hanyar da muke samu?banda ma kananun dauke dauken da ake mana duk mun yi shiru,sanann Umma yanzu Allah yayi mun samu ace a raba da su saboda su suka fi kowa son abun duniya mu kuma ba mu san dadin namu ba ko?Wlh Umma ko kaffara ba zan yi ba Hajiya fada take babu wani raba wa da za ta yi ita kadai ta so cinye wa da ita da yaran ta"hannu Umma ta daga mata sannan tace

"Wuce ki je ki sa kaya kar sanyi ya shige ki Auta na ga alamun ba za ki fahimci abunda nake nufi ba"ta kare a raunane,kwabe fuska Sabeeha tayi sanann tace "shike nan Umma kiyi hakuri na fahimta Wlhy kuma na san tunanin ki be wuce mun samu tsabani da Hajiya ba ko?To kwantar da hankalin ki Umma ta ko da na je cikin kwanciyar hankali tare da kwantar da kai na roke ta ta dawo mana da kayan mu,saisa ba ki ma ji ihun murya ta ko mata ba,and Umma na yarda tunda in an ba su hankalin ki zai fi kwanciya in na shirya zan zo a zuba wa kowa,amamn Wlhy Umma banda Hajiya Ladi da Maman Latifa su kam wlh ba za a ba su ba tunda kallon karuwa suke mun"ta kare tana shige war ta daki ba tare da tsayawa jin me Umman za ta ce ba,sam ta rasa gane sanyin hali irin na Mahifaiyar ta bata san wani irin hakuri da sanyin zuciya Allah ya bata ba,wasu kan ce ta cika tsoro wasu su ce tana da zurfi ciki tare da kokarin hadiye abu a ranta,wasu su ce ba ta son damuwa da hayaniya ce wasu har haushin sanyin halin nata ma suke ji,wanda a ciki kuwa harda Sabeehar don tashin ta haka Umman ta raine ta ta so ta tashi da sanyin hali tare da hakuri irin nata amman kowa da irin yanda Allah yayi shi,and matan gidan su ne suka kara contributing na rashin hakuri da rashin kunya da suke cewa tana da shi,don tunda ta mallaki hankalin ta ta san me ke mata ciwo ta daina raga wa ko wace mata a cikin gidan,Hajiya Ladi ne ma take jin shakkar ta to yanzu kam ma ta bar ji bata ki su bugu ba Wlhy,don ba karamin kai ta wuya suke yi ba.

Da kallo Umma ta bi bayan ta sannan ta girgiza kai,har gobe tana shan mamakin irin zafin ran Sabeeha bata san a yaushe ta koma me tsiwa haka,duk da bata bi bayan ta ta gan abunda ya faru ba amman sarai ta san ba rokon nata tayi ba kamar yanda ta fada mata,don ta san halin Hajiya Ladi sarai ko kafafuwan ta Sabeeha za ta kama don roko wlhy ba za ta dawo da kayan abincin nan ba don babu wanda ya isa sanya tayi haka ba wanda ya isa hana ta,abunda take so shi take yi,kai ta kuma girgiza wa sanann a fili ta ce "Allah ya kyauta ya kuma shirya mun ke Auta"daga haka ta fara shiga da kayan abincin.

Cikin nustuwa Sabeeha ta zauna tare da shafa mai a jikin ta,tana yi tana sakar wa kan ta murmushi,haka kawai ta ke jin dadi da nutsuwar maganganun da ta fada wa Hajiya Ladi,saida ta gama shafa man sanann ta taje gashin kan ta tare da sanya ribbon ta parka shi a tsakiya sanann ta nannade tare da yin donut da shi,brush ta dauka tare da gyara gashin gaban kanta da ya kwanta luf luf da su abun sha'awa tare da sajen ta,sanann ta aje tare da kallon kan ta,yau daya ta ji tana sha'awar yin kwalliya wa face din ta,she just want to look her absolute best,so tsincan kan ta tayi da daukan powder tare da fara shafawa a face din ta,take kuwa ya kara fito da sirrin kyan ta,ba za ta tuna yaushe ne rabon ta da shafa wa fuskan ta powder ba hakan ne ya sanya ta kura wa kan ta ido sai take ji kamar ta goge duk da yayi matukar yi mata kyau,jin ringing din wayan ta ne ya sanya ta aje kwallin da ta dauka za ta shafa tare da mike wa ta dauko wayar,ganin shine ke kira saida ta saki murmushi domin yanzu ta gama zancen shi a ran ta,dauka tayi tare da sanya wayar a speaker sanann ta koma ta zauna.

 A SIMPLE DARE (WASA DA SO)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora