"Nabeel!!!can you stay out of this pls,haba yanzu fa na gama maka bayani sai kace baka fahimta ko baka gane wa,what else kake son ji daga guri na kuma??Sarai ka sani bana son dogon magana musamman ma wanda zai bata mun rai,haba wani irin abu ne haka magana daya mun yi ta yi ke nan"da sauri Farouq ya ce

"Haba Geee be calming down mana miye haka akan wata banza can za ku tsaya fada a tsakanin ku??Kuna ganin hakan yayi haba"

"Kyalle shi Farouq Ai ba gane wa yake yi ba,sarai ya san abun nan duk saboda mu nake yin sa,I don't think duk duniya akwai wanda ya kaini tsanar yarinyar nan,in kun san yanda nake daure wa in danni heart dina kafin in kira ta sai kun tausaya mun,I'm doing all this for your guys ba wai don kai na kawai ba amman Beel ya kasa fahimta,in har ban yi haka ba a taya za ta saki jiki da ni har ta yarda eh da gasken son ta nake har ita ma ta so ni??Kar fa ku manta wace ce ita manta da ta fito daga middle class family yarinyar akwai Jan class da self respect sannan  uwa uba bata taba soyayya ba in har ban yi haka ba a taya zan janyo attention din ta har ta fada soyyaya da ni?Duk tunanin Beel son yarinyar nake yi wanda mentality ne kawai irin na shi,kai ka sani ko in ce duk kun sani sam bata da qualities din da nake nema tattare da mace,na yi zama cikin turawa da Larabawa duk ban so su ba sai Sabeeha??Wai kake thinking zan fada soyayyar ta??Bata da wayewar da nake nema a gurin mace sanann bata da aji da nake so tattare da mace,In fact Sabeeha bata da ko daya daga cikin abubuwan da nake nema a gurin mace  amman sam ka kasa kwantar da hankalin ka ka fahimci I'm just playing her ne,haba I'm fade up with all this bullshit of yours wallah"ya kare a zafafe yana son barin dakin.

Riko hannun shi Beel yayi tare da dawo da shi ya zauna sanann yace "C'mon dude I'm sorry okay ba wai in fadan haka don na bata maka rai bane,kawai ina jin tsoro ne kar along the line ka fara developing feeling wa ita ya sanya nake fadan haka"

"Beel mark my words ni Faizan babu feelings din Sabeeha da zan yi catching don't you trust me??Ko ka mance Waye ni ne FIK ne fa,haba Ai ya ci ace a wani za ka bada labari na ba wai a baka ba,so worry no more okay I got nothing to do with her,daga 3 months sun cika ka bani watch dina Sabeeha will be out of the picture,kana tunanin wai yarinyar tana burge ni ne??Ko gani kake ni ban tsane ta ba?Beel
She slapped me right on my chic fa and kana tunanin in fara son ta haba wake up guy,ko za ku iya mance wa ku yafe mata ka san na rantse maka I must avenge marin da tayi mun,and tunda nake ko da wasa ba wanda ya taba kai hannu jiki na sai ita and kana tunanin ta daki banza ne,shirya mata nake wlhh sai tayi kuka kukan da bata taba yin irin sa a rayuwar ta ba and bana jin har ta koma ga Allah za ta kuma irin sa,sai na yi breaking din ta down into smaller pieces inda ba za ta iya kallon kan ta a mirror ba ma balle tayi tunanin hado pieces din back ta tayar da kan ta,just watch and see how I will destroy her life,banda abun ka Ai 3 months ya kusa so time will speak ba sai na ce komai ba,ku tashi mu tafi kar a fara party babu mu,in samu mu dawo in kira that Middle class Twat of mine,na samu na kashe shegiya da kalamai masu zafi🥱"ya kare yana saka Expensive Shade din shi a idanu tare da feshe jikin shi da turaruka masu shegen kamshi.

Wata wawiyar dariya duk suka sanya sanann Akram yace "ku ji tsoron Allah guys ku tsoraci FIK,Kai FAIZAAN!!Baby girl din ta ka kake kira Twat??Tunda nake na jima ban ga shege irin ka ba gata Twat ga ta Middle class,abun yayi yawa ai"

Dan dariya yayi sanann yace "Akram to in ba Twat ba me zan kira ta da shi?Ai sunan shine ya dace da ita"dan dariya Jawad yayi sannan yace "Wlhy in badun mun san Waye kai ba babu wanda zai ga yanda kake kashe yarinyar nan da kalamai ya dau ba son ta kake ba,Breakfast har gida fa aka kai mata yau,Wlhy ko Zuma rock ne ya danne heart din ta sai ka shiga mutumi na,na san tana can tana tunanin ka don babu abunda yam mata ke so irin haka Wlhy duk wace ta samu Romantic and caring babe like you to ita kan ta ba za ta san time din da za ta fada son ka ba,shege fada mun a ina ka iya duk wanann abubuwan?"

Kafadan shi ya dan daka sanann yace "tsaya wasa Mommah da Soul sis ke bani course na musamman Ai nima jiki na na bani na kusa shawo kan yar banza wannan cika bakin bana soyayya bana soyayya duk zai kare Ai tunda ta shiga harkan Rocket gang sai mun koya mata hankali,ku zo mu tafi, tayi ta tunani na tun safe sai zuwa anjima zan kira ta in kara birkita mata lissafi,don ma tana da taurin kai Ai da tun day one na samu soyayyar ta,amman ba komai with time da ni take wasan"ya kare yana juya car key din hannun shi,duk dariya suka sanya tare da yi masa shegiyar kirari dake kara wa kan shi girma sanann suka fito daga side din dake mallakin su a gidan su Beel,tare da fadawa mota suka fita a tsiyace,wanann daman a rubuce yake duk gidaje biyar din nan suna da part guda wanda yake mallakin su ne,in sun zo duk nan suke zama.

 A SIMPLE DARE (WASA DA SO)Where stories live. Discover now