Ɗiyarka Aisha ai surkuwata ce Matar ɗanka Ahmad,ba Daddy Ishaq ba hatta da Alhaji badamasi saida yashiga shock da maganan nata,Janar ɗan Musa baki a buɗe yake kallon Ammi shiko gogon naku ƙasa yayi da kansa cike da jin nauyin mutumin shikan sa Daddy Ishaq yayi mamakin jin wai Aisha tana da Auren wani akanta,ko sanda su Alhaji Sunusi suka saka ayi kidnaping ɗinta duk da tabashi labarta masa yanda suka rayu bayan bashi da barin gida da sukai dama garin baki ɗaya irin yanda Anna tasha wahala akansu da yanda sukayi rabu da Anna hatta da zaman ta A gidan Anty hajja da aiki da take a companyn Ahmad ɗin bata ɓoye masa komai ba,sai na auren ta da Ahmad ɗin.

Gwauron numfashi yasauke yana cewa"ikon Allah yanzu dama wannan shine surikin nawa?amma Mamana bata faɗamun tana da Auren ba ko sanda na haɗu da ita"to ko a sa'in ba a daura musu Auren bane cewar Ammi,sai kuma tace dama kahaɗu da itane kafin sannan?kuma ta gane ka?amma mesaya bata faɗa mana ta ganka ba?"Ma'arufa baki canza ba ko kaɗan a yanda nasanki yawan tambaya to yanzu wanne zan amsa miki daga ciki kin cikani da tambayoyi kamar wata ƴar jarida.

Dariya suka saka"duka zaka amsa"to ni nace karta faɗawa kowa ta ganni ciki kowa harda khadija saboda tana cewa ta ganni dole yaran su bukaci ganina,ni kuma banaso mutane su sani saboda farautar rayuwarta da akeyi,dan a sa'in ruwa ajallo Sunusi da Yaransa suke nemana ya bazasu ko ina,kuma banason saka rayuwarsu cikin hatsari sunyi rayuwa batare da sanin ina raye ba,banaso wani abu yasame su ta dalilina yanzu kinji amma nayi mamaki da bata faɗamin tana da aure ba.

"Inaga kunyar faɗa maka takeyi Daddy Faisal ya amsa masa da cewa haka,shiko Barista Anwar cewa yayi"kunya kamar wata ƴar 80c dariya baki daya akayi banda Alhaji badamasi da kunyar duk ta da baibaye shi wai ɗiyar Ishaq ɗansa Ahmad ke aure kaji ikon Allah aure daya dinga ikirari na wucin gadi ne sai gashi Allah yayi ikon sa akai ashema ƴar ɗan uwane a gareshi Allah ƙadiran alaman yasha yarinƙa kira a ransa.

**********

Tun barin Fauza wajen  koda tashiga ɗaki zama tayi daga bakin gado tana mai tariyo fuskar matar da tagani saide duk yanda taso ta wassafa wannan fuskar bata Annan ta bane ba,nutsuwa tayi tana mai tariyo hoton matar da tagani dakuma tariyo yanayin muryar,tabbas ba Annata bace ko shekara dubu tayi ba taganta bata tsammanin zata iya mantawa da ita balle ƴan wasu watannine ko Mubaraq dayake ƙaramin cikin besa yamance kamannin ta ba balle ita data mallaki hankalin kanta,to ita ko wannan ɗin wacece?
Meyasa zuciyar ta taƙi amince mata da Anna ta gani,wai ma yama'akai mutumin nan yasan da ɓatan Anna,ko bana tare da Mahaifiyata ba wanda yasan inda take kuma ina bukatar ta atare dani?ya'akai ma yasan ta harya iya samo vedion ta yakemun nuni da bata cikin nutsuwar tana bukatar taimakona.

Kode yana bibiyarki ne wata zuciyar ta amsa mata eh bibiyarki yake dan son  sanin komai naki dan cimma wata manufa nashi ta daban,idan ko hakanne lalle akwai aiki a gabana kode nafaɗama Ahmad ne ko shi ze iya ya taimaka mini,to shi Ahmad din kinsan kowaye Alhajin a wajen sa tunda ya daukoki ya ajeki cikin gidan sa ai baki isa yin komai ba saide kawai ki masa biyayya kawai ko baki samu komai ba wajen sanin ko shidin wayene zaki tsira da takardun kadarorin Mahaifinki idan kika samu kika dauka zaki iya guduwa a gidan dan tsiratar da rayuwarki.

Ajiyar zuciyar ta sauke da ta gamsu ɗari bisa ɗari da shawarar da zuciyarta ta bata,saide kuma waze taimakamun dan ganin burin nan nawa yacika waye waye wayeee?

Tawani jaa ye ɗin da karfi "nine wanda ze taimakeki dan ganin kin cika burinki yafaɗa daga bakin ƙofa tsaye yake ya rungumi hannunsa a saman ƙirjinsa ya zuba mata idanun sa masu ƙwarjini,batasan adadin wani lokaci ya ɗauka tsaye a wajen ba,muryan shin kaɗai da taji ya sakata neman ruɗewa.

"Karki ji shakkar faɗamuni damuwarki Eashow baki da kowa a nan sai Ni nimaɗin kusan bani da kowa saike karkiyi la'akari da yanda mukai aure ko abunda auren namu ya ƙunsa,kafin wa'adin sa yacika ina tare dake da daɗi babu daɗi waye shi?yayi tambayan da yakusan sakata ruɗewa.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now