Dan dariya Zuhra ta danne sanann tace "dadi na da ke saurin fushi Sabeeha waya ce miki son FIK nake??Kawai dai ce miki nayi na ga me kama da shi ne ya wuce,so why all this long lecture??And ko kaffara ba zan yi ba in na rantse FIK is not that bad as you think kin ki ba wa kan ki daman fahimtan Waye shi ne,amman yana da kirki sosai wlhy"

"Excuse meeee!!!Goofy angel don't tell me is  true abunda nake tunani?Yaushe kika san shi har kike bada shedan kirki akan shi?"ta kare tana tsare ta da idanu.

"Ko na san shi ko ban san shi ba Sabeeha d'an Adam
ne shi,dole yana da good da bad halaye babu yanda za ayi ace Allah ya tara masa mugayen halaye ba tare da kyawawa ko da kadan ne ba,and a labari na ji yana da halin kyauta duk wani me kyauta kuma Ai kin ga alamun mutumin kirki ne,so pls don't just judge a book by it's cover and ki sassauta irin wanann tsanar da kike masa domin bayi da amfani sam,as far as zan iya tunawa mu muka masa laifi amamn shi ya zo yana neman shiri da mu,inda wani ne ko zai yi yawo tsirara kin san sai ya rama marin da kika yi mishi,amman rashin ramawa da be yi ba har yau shiru be kuma yi komai ba shows that he is actually a gentleman!!!!so pls no need of holding grudges anymore ki manta ke ma da abunda ya faru ko ma zauna lafiya mu fahimci juna duka"

"Ke dalla yi mun shiru!!!Sannu nace sannu Zuhra Wlhy abu daya da yake hada ni da ke rashin wayon ki,ko hauka nake ni ce zan zauna har na fahimci waye shi to akan me ma ??Akan wani dalili??Keee ni fa haka kawai yaron be mun ba ko kin manta abinda ya fara hada mu da shi ne???"ta kare tana tsare ta da idanu wa

"Ban manta ba Goofy angel ko da ace labari kika nan ya ci ace na haddace na kasa mantawa balle akan idanu na komai ya faru,I'm just saying kiyi kokarin kyautata masa zato tunda shima Musulmi ne dan uwan ki,yanda kike sallah shima haka yake yi,so why za ki zauna kina ta jin haushin shi tare da tsanar shi?"

Dan shiru Sabeeha tayi don ta ma rasa abun fada saida Zuhran ta riko hannun ta tare da damkewa cikin nata alamun kin ji pls sanann ta iya budan baki tace "can we stop talking about him pls???and can you hear me out pls?Labari nake baki kin katse ni kin shiga na wani can daban so kina iya saurara ta na karasa miki ko kuma nayi tafiya ta yau it's gonna be a busy day for me got a lot to do"ta kare tana hada kan jakar ta don bata ga amfanin zama da Zuhra yau tana mata tadin yaron da take ji duk duniya babu wanda ta tsana irin shi,and ko shakka babu ita ma ta san ya tsane ta,hauka ma ashe take ta saki Jiki da shi,yaron da tarbiyya ma be ishe shi ba,duk da itama har yau in ta tuna da ta mare shi bata bashi hakuri ba,sanann be yi mata komai don ramuwa ba banda haka ma sai taimakon ta da yayi ta yi don ma ta hana shi,jikin ta ya kan yi sanyi tare da jin tsoron ko yana planning something big ne??saisa kullum idanun ta bude suke tana jiran ta ga ta inda zai bullo don a yanda Zuhra take bata labarin su ta san ko ita kanwar uwar shi ce ta mare shi Wlhy sai ya rama,ta rasa me ya shiga kan kawar nata yau har take yabo tare da kare shi haka,banda ta san Zuhran ta mace wa Habeebeey Ai da sai tace son FIK din take yi.

"I'm sorry babe ni ba na fadi haka don na bata miki rai bane,just saying abunda nake gani kamar ya dace ne,ina jin ki"saida ta harare ta sanann tace "wa Ai na gama miki labarin bani karasawa kuma yar iya"ta kare tana hararan ta.

Rungumo ta Zuhra tayi tare da manna mata kiss a kumatu sanann tace "zo mu shirya kawata FIK din banza in dai maganar shi ne baki so am gama daga yau"ta kare tana narai narai da idanu,saida ta kuma maka mata harara sanann tace "Allah ya so ki yau ina cikin farin ciki yasin da nan gani nan bari ba zan karasa miki labarin ba haka zalika ba zan baki ko ficika a cikin kudi na ba eheee"

Dariya Zuhra ta kwashe da shi kafin tace "Ke kin isa!!yasin ba ki isa cin kwandala babu Zuhra ba ke ma kin san ni da ke hanta da blood ne in daya baya nan dayan ma babu shi,kar ki manta ke wata ni Zahra so ni da ke mutu karaba takalmin kaza,maza karasa mun labarin".

Saida ta dan kwade kan ta sannan tace "sai shegen dadin bakin tsiya,ki cigaba da mun iyayi da rawan kai in ina baki labari wataran sai na kama ki na tusa miki pepper a cikin bum bum din ki"

 A SIMPLE DARE (WASA DA SO)Where stories live. Discover now