A zauna ta tarar da Umma da alamu ta gama nata karatun ne tana adduoi kamar kullum so zama tayi kusa da ita tare da bude hannuwan ta ita ma saida Umma ta gama sanann suka shafa a tare,juyowa Umma tayi tare da kallon ta inda take ta sake wa Umman murmushi sanann ta mika mata hannu,suka yi musabaha kamar yanda suka saba kafin tace

"Hajiya Umma an tashi lafiya?Ina kwana ya jiki jiki kuma"dan kwade kan ta Umma tayi sanann tace "duk lokaci guda kuma wa ni kadai,lafiya klau Alhamdulilah Sabeehatun Umma ya kika tashi?Da fatan dai yunwa bata hana ki bacci ba jiya?"

Saida ta dan zame tare da kwantawa jikin Umman sanann tace "lafiya kalau na kwana na tashi Umma ta,da adduoin ki jiki na babu abinda zai same ni sai abun da Allah ya so"

Kan ta Umma ta shafa sanann tace "Masha Allah Auta na ubangiji ya cigaba da iya mana,tare da rufa mana asiri duniya da lahira,Allah ubangiji yayi miki albarka sannan ya kare ki daga dukkan sharri,yanda kike kula tare da tattali na ubangiji ko bayan raina ya kula mun da ke da zuriar ki baki guda,Allah kuma ya baki miji na gari in wanke ki in kai ki dakin ki"ta kare tana murmushi.

"Ameen thuma Ameen Umma ta,in sha Allah ba za ki mutu yanzu ba sai nayi kudi na zamo babban mutum a kasar nan,sai na kai ki Makka da Madina,Umma in sha Allah sai na siya miki gida da Motoci,sanann na dinka miki Super da laces masu mugun tsada,harda gold duk zan siya miki in nayi kudi,Allah ya kara miki lafiya da tsahon kwana in jiya da ke dadi kamar yanda kike wahala gurin ganin kin inganta rayuwa ta Umma ta🥺"ta kare tana jin hawaye na kokarin zubo mata ba karamin tausayi da kaunar Mahaifiyar ta ba,bata da burin da ya wuce a rayuwa ta zamo wata don kawai ta jiyar da Mahaifiyar ta dadi,tana son ganin ta jiyar da Mahaifiyar ta dadi da mata da yawa suke sha,tana son ta sanya tufafi masu tsada kamar yanda manyan mata ke sanya wa,tana son ta ga ta je Makka ta kaita kasashen waje,bata da fata da buri da ya wuce Allah ya amsa mata tayi arziki ko don ta jiyar da Mahaifiyar ta dadi.

"Ameen Ameen Uwata ubangiji ya amsa Allah ya amsa ya baki budi me Albaraka ya tsare ki da cin haramun,Allah ya sa duk abinda kika taba ya zamo akwai budi a ciki da Albarka,ya kuma kara tsare mun ke mutuncin ki da kuma imanin ki"

"Ameen thuma Ameen Umma ta, ta kare tana lafewa a jikin ta, "daga ni ni kam mutum kamar kuliya sai shegen son jikin tsiya,tashi ki je kiyi wanka,sai a zo a nemi abun da za a karya da shi kuma"

Baki ta dan turo "kai Umma ki dan bari na dan ji dumin ki mana"ture ta Umma tayi "Ke matsa mun dumin me wanda tun kina ciki kike sha,maza tashi ki juye ruwan zafin cikin flask kiyi wanka,bari na shiga na karbo miki dan wake shi kam ai kina so ko?"Umma ta kare tana mike wa,itama tashi Sabeehan tayi har ta kai kofa kuma sai ta dawo

"Yauwa Umma na mance akwai abunda nake son fada miki" a bakin gado Umma ta zauna sannnan tace "ba dai wani abu aka ce ku siya ba ko ku kawo a makarantar na ku"ta kare a raunane,a kasa gurin kafafuwan ta ta zauna sannan ta daura kan ta akan cinyar ta kafin tace

"Umma jiya da dare wani ya kira ni", da sauri Umman tace "wanann wani me saa ne da ya sace zuciyar ki har kike bani labarin shi"ta kare tana dariya don yau ne rana ta farko da Sabeeha tace da ita wani na miji ya kira ta.

"Kai Umma daga na ce miki an kira ni shike nan kuma sai ya zamo soyayya,Umma ke da Zuhra kullum dai maganar ku daya yasin"kan ta Umma ta kwade "gidan ku to don Allah in ba Auran nan kuka yi ba za mu kwada ku mu cinye ne,Wlhy Sabeeha kika cika mun ciki sadakar ki zan bada"dariya duk suka sanya kafin tace "Haba Umman Sabeehatu ke ma Allan na san wasa kike sadaka sai kace wata dankalin Hausa"

"Za ki ga wasa ni tashi maza ki fada mun yanda kuka yi da yaron Allah sa ba yar hali kike yi masa ba don na san hali", "Umma!!Umma to kwantar da hankalin ki ba ma saurayi ko soyayya bane,yau dai da alamun kaji za mu ci da lemun kwalba a gidan nan"ta kare tana tafa hannu kamar wata yar yarinya.

 A SIMPLE DARE (WASA DA SO)Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu