"Na haɗu dasune a wata seminar a garin Abuja mun dauki tsawon sati biyu dasu harde nayi ɗan sabo dasu ranan wata laraba da yamma da bazan mance ba bayan mun tashi daga wajen taron suka biyoni har matsaukina a nan suka zomun da bukatar su ta son haɗa hannun dani wajen sarrafa magani dan suma sunaso jaharmu ta arewa ta amfana da su,da farko naƙi amince musu da bukatar da suka zomun da ita sai sukai ta kawomin misalai iri iri suka kuma bini da roƙo da magiya harde na amince zamu fara harkar nan dasu amma ban amince musu saka hannu jari da suke nemi sakawa ba.

Nade amince musun ne amma nace sai nayi tunani da haka na rabu dasu,ban kuma sake bi takan maganan tamu dasu ba,har tafiya ta kamani zuwa ƙasar China inda na dauki wata shida kafin dawowata kaman dama jiran zuwan nawa suke inda suka sake taso da maganan wannan karon ba Sunusi kaɗai bane harma da Alhaji Na Allah dama Alhaji Surajo kai tsaye naki amincewa da tayin nasu,dakyar de na amince shima din dan ganin Alhaji na Allah tare dasu dayake shi na Allah abokina ne tun na yaranta tare mukai makarantar secondary da shi nasan shi.

Saide abunda ni bansani ba,su bata yanda suka zo mun da magana haka yake a gunsu ba suna ha'intata ba tare dani nasani ba,suna amfani da mazubin maganin mu suna safaran miyagun ƙwayoyi saida muka ɗauki a ƙalla wata biyar a haka bani da masaniya kan abunda sukeyi ranan wata litinin da baxan taɓa mancewa da ita ba a rayuwa ta ina zaune a cikin Office ɗina sai ga Manager na yashigo bayan yanemi izinin shigowa na bashi sai da ya zauna saman kugera yana fuskantata niko ganin yaƙi cewa komai na ɗago daga abunda nake na dubeshi ina cewa dashi"Malam Adamu ina fatan lafiya kashigo bakace komai.

Saida yasauke gauro numfashi sannan ya ajiyemun mazubin Roba da muke amfani dashi wajen zuba capsule na kalli Roban sai kuma na ɗago kai ina kallon sa dan neman karin bayani.

"Ka gafarce Alhaji ka dauki wannan Roban ka duba da kanka shin da sanin ka ake wannan ta'asar a wannan Company ko rufa rufa sukai maka?

Bangane abunda kake magana a kai ba malam Adamu nace dashi turamun Roban yayi zuwa gabana yace dani kaide ka ɗauki wannan abun kagani.

Ba karamin kaɗuwa nayi ba da abunda na gani ɗin,ɗaukan Roban nayi na nufi guest house ɗin Alhaji na Allah inda nayi sa'an samun su su duka a waje da zuwana nawurga musu Roban ina cewa dasu dama abunda kuke aikatawa kenan a Company na bansani dama kunsan irin abunda kuke aikatawa shine kukaimun rufa rufa kuna cin dunduniya ta batare da nasani na ba.

To wallahi ƙaranku zanyi kuma daga yanzu na sauke ƙwantiragin dake tsakanina daku,basu tankamun ba saida nakai  aya sannan suka kalleni cikin halin ko in kula da rashin damuwa a saman fuskokin su suka shiga mun dariya sannan Alhaji na Allah ya kalleni yace"yanzu kai Badamasi saboda wannan ɗan abun katashi hankalinka ai na ɗaukama ranace ta ɓaci mana da rashin damu saman fuskansa yake magana yakara da cewa yanzu de zauna zamuyi magana dakai.

Zama nayi ina huci bayan na ɗauki Roban nasaka aljuhuna saboda kafa hujja in bukatar hakan ya tashi,ruwa mai sanyi Alhaji Surajo yabani cikin glass cup ina shan ruwan bansake sanin inda kaina yake ba saide tashi nayi na ganni kwance a wani ɗaki saman gado ba tufafin komai a jikina,yana kaiwa nan da maganan sai ya fashe da matsanancin kuka kaman wani karamin. yaro da jin yanda yake kukan kai kasan abunda yafaru da shi yaƙuna masaa marai ainun kuma ba abune mai daɗin faɗa ba,,ruwa Janar ɗan musa dake zaune kusa dashi ya mike masa karba yayi ba tare da ya musaba yasha"na gode yace yana sharan hawayen sa"ko zamu ɗage zaman zuwa wani lokaci na ga kaman kana bukatar hutu"cewar Janar"No wannan shine lokaci daya dace ya fada mana komai dan musami bakin zaren inji Ahmad dayake tsaye tun sanda Baban nashi yasoma magana,murmushin karfin hali Alhaji badamasi yayi sannan yace"ai ko baka ce ba nima din bazan saken barin ku cikin duhu ba,nasan Ammin ka tajima tana zargina da aikata ba daidai ba.

*******
Tana nan turƙushe saman gwiwarta kaman mai neman gafara tajima ahaka kafin ta lallaɓa tsunmar rayuwarta tashiga ɗaki koda tashiga ɗakin ma rasa abunyi tayi takasa taɓuƙa komai wa kanta ashe dama kowa yasan Aurwn wucin gadi Ahmad ɗin yayi da ita,ta tabbata bmara hankali tanama mutanen nan kallon Biri suka ashe kallon ayaba suke mata,ashe shiyasa Hajia Mami ta nace sai takoma zama cikin ƴan aikin gidan ashe da dalilin ta nayin haka ashe shiyasa Fauza ke mata wani gani gani ashe da abunda suke kullawa,ina kallon kaina ina da wayo ashe wayon banzan gareni dana bari yarabani da budurcina ƙimata yarabani da masoyina na gaskiya ashe ashe haka tayi ta magana ita kaɗai a ɗaki bayan fitan Alhajin daga ɓangaren su.

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now