002

7 0 0
                                    

*🌺RANA DUBU...🌺*   
*~A KINGDOM AND ROMANTIC LOVE STORY~*

_STORY AND WRITING BY_
*©️®️JAMEEY*

_M W A_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

_WRITER OF_
*NIDA UWARMIJINA*
*BUDARDIYAR SOYAYYA*
*DA'IMAN ABADAN E. T. C*

_21/9/2023_

002

Shekarun KAZAUWAFA ALIYU da KAZAUWAFA ABDULLAHI biyu a duniya FAUZAJ BILKISU ta haihu itama ta haifo mace aka saka mata sunan Jalila,maimakon murna Allah ya bata haihuwa itama sai ta boye ta sha kukanta dan ba haka take so ba,ita namiji take son haihuwa wanda zai gaji ZAUFAJ LAMIDO dan tana kan bakarka na yanda ta kasance FAUZAJ ta farko to dole ɗan ta zai zama ZAUFAJ, murmushin yaƙe kawai take ma masu zuwa tayata murnar haihuwa dan shekararta goma da aure sannan ta haihu...bayan suna ta cigaba da ga in da ta tsaya ita da hadimanta amintaitun dan tsaye take taga bayan su KAZAUWAFA dan ta saka ma ranta sai dai kowa ya rasa ba zata zuba ido ba tana ji tana gani a maida ta banza a masarauta bayan itace aka fara aura..suma iyayenta ba'a bar su a baya ba wajen neman mata asiri, duba da suma suna da nasu gudurin akan masarautar dan WAIDA (WAZIRI) yace asalin masarautar tasu ce dan kawai basu da ilimin boko a wancan zamanin kakan ZAUFAJ LAMIDO wato ZAUFAJ LAMIDO NA l ya haɗa baki da turawa aka kauce mashi mulki aka maida shi a hannun su LAMIDO,kuma ta hanyar FAUZAJ BILKISU kawai zasu bi mulkinsu ya dawo hannunsu ta ruwan sanyi duk da ko a haka ba zaune suke ba wajen ganin bayan ahalin su ZAUFAJ LAMIDO ta kalƙashin ƙasa.A bangaren FAUZAJ SALAMATU ma ba'a barta a baya ba wajen ganin ta kashe KAZAUWAFA NURANDEEN saboda yanzun shine kawai matsalarta dan tasan idan har ZAUFAJ LAMIDO ya faɗi ya mutu komin daren daɗewa KAZAUWAFA NURANDEEN za'a daura a kan karangar mulki kuma ba zata iya jura ba yanda take yar ZAUFAJ jikar ZAUFAJ to dole kuma ta zama uwar ZAUFAJ sai ta kwafa tahirin da ba'a taɓa kafa shi ba a kasar Mali..ba zata zuba ido ba yar tallakawa tazo ta ringa juyata ba tana ɗaga mata kai dan ta zama uwar ZAUFAJ yanzun ma ya suke ƙare da ita wajen girman kan banza da miskilancin banza ina ga ta waye gari taga ɗan ta ne ZAUFAJ wata ila daga ranar ba zata sake barin su ba suyi wani motsi a masarautar ba.Ita dai FAUZAJ HAJARA ba ruwan ta kullum cikin addu'a take neman tsarin Allah duk da wani lokacin asirin nasu yana dan jefarta amman da ta mike tsaye da addu'a da azkar baya wani tasiri haka ta fama da kishiyoyinta gaba kura baya sayaki ba inda zata je taji dadi sai wajen mijinta hakuri kawai take da kowa bama iya su FAUZAJ SALAMATU ba.Haka rayuwa ta cigaba da tafiya a masarautar dadi ba dadi dan wani irin tungu ake da surkule iri iri..tsoran Allah yayi ma wasu ƙaranci a zuciya dan kuwa su FAUZAJ SALAMATU da FAUZAJ BILKISU tuni suka daina sallah dan bokayensu sun hana su kuma sun daina dan ba sallar bace a gabansu duniya kawai suke nema ido rufe.Bayan shekaru  sun wuce a lokacin KAZAUWAFA NURANDEEN ya kai shekara 20 a duniya ranar da ya cika shekara 20 a ranar ZAUFAJ LAMIDO yayi murabus ya ɗaura KAZAUWAFA NURANDEEN akan karagar mulki dan shi ko aure ma ba'ayi mashi ba, ZAUFAJ LAMIDO yace yana bukatar hutu dan haka zai maida  KAZAUWAFA NURANDEEN akan mulki ya zama ZAUFAJ wannan lamari ba ƙaramin turmutsi ya kawo ba a masarautar dan ba wanda yasan da maganar naɗin ɗan sa,sai da gari ya waye yace ga abun da yake bukata ayi,dan ko shi KAZAUWAFA NURANDEEN bai san da zaman maganar ba dan shi sam mulki baya gaban shi daga shi har Mahaifiyar shi wato FAUZAJ HAJARA,kuma su duka basu san da maganar ba sai a lokacin yace yana son yayi magana akan lamarin yace baya bukata a ɗaura KAZAUWAFA ALIYU Amman bai ga fuska a wajen Baban nashi ba.

Ba shi ba duka yan masarautar masu ikon faɗa aji bai basu wannan damar ba,bama wanda yayi gigin cewa zai yi mashi maganar dan kuwa kowa yasan halin ZAUFAJ LAMIDO NA II bai da wasa ko kaɗan kuma baya daukar raini ko kadan shiyasa kowa ya fara shiri dan 30mn ya basu zasu fara nadin...tafiya akayi da KAZAUWAFA NURANDEEN wani bangare a masarautar dan a shirya mashi kafin lokacin yayi shi kuwa ZAUFAJ LAMIDO bangarenn shi ya koma dan shiryawa daga shigowarshi RAUDELE(JAKKADIYA) tazo akan FAUZAJ SALAMATU tana neman ayi mata iso murmushi kawai yayi yana girgiza kai yace ta shigo koda ta shigo bai kulata ba sai da ya gama shan tea din shi sannan ya kalleta akan ta fadi abun da ya kawo ta dan yana da abun da zaiyi sosai..Sai da ta dan yi jum dan a tsorace take amman ba zatayi shuru ba akan wanann lamarin dan sam KAZAUWAFA NURANDEEN bai canci ya zama ZAUFAJ ba dan KAZAUWAFA ALIYU ya fi shi iya komai ya fi shi sanin mai ye mulki mai ake kira mulki shi da yake jikan ZAUFAJ gaba da baya..shi ko KAZAUWAFA NURANDEEN mai ya sani yaron da ko fada baya zuwa kullun yana wajen uwarshi zaune suna kulla makirci to ba zata zuba ido ba a wanann gaɓar ta gaji da banbancin da ZAUFAJ LAMIDO yake nuna akan yaran ai su ma su KAZAUWAFA ALIYU ai haihuwarsu akayi..Katse mata tunanin ZAUFAJ LAMIDO yayi yana ce mata akan ta fadi abun da ya kawo ta dan ai tasan yau ake naɗin da zata yi mashi zaune bayan tasan lokacin da aka ɗiba ya kusa cika.. cikin salon makirci da yaudara ta kwantar da murya ta fara gaya mashi abinda ya kawo ta ɗaga mata hannu yayi yana nuna mata hanyar fita...tasan halin kayanta sai ta mike tana bashi hakuri ta fita daga dakin girgiza kai kawai yayi bayan ta fita yayi mata addu'ar Allah ya shiryeta..Koda ta fita a bangaren ZAUFAJ LAMIDO ba inda ta zarce sai a bangaren FAUZAJ BILKISU nan suka hadu dan nemo mafita suna cikin haɗawa da kwancewa lokacin ya cika suka shirya suka tafi amman ran su tas dan sun san ba za'a taba yin naɗin ba idan ma anyi to yaron yana yawan kujerar to na zai kwana da rai ba inji bokansu da wannan hope din suka tafi akayi komai da su..sai dai suka zuba ido wajen ganin zaman kujera da Bismillah ya hau kujera aka gama komai ba abun da ya samu sabon ZAUFAJ wato ZAUFAJ NURANDEEN..Tun da akayi wanann naɗin sai komai ya ida jagulewa a cikin Masarautar komai ya lalace dan wanda suke da boyaiyiyar manufa akan mulki sai suka fito a zahiri komai ya jagula ga tsafi ba wanda ba'ayi a cikin Masarautar bama a waje ba..ana cikin wanann tirka tirka ZAUFAJ LAMIDO yace ga garinku nan bayan ya bar ma ZAUFAJ NURANDEEN sirrika masu girman gaske ya kuma tusa mashi son mulkin a rai da kuma kawo sauyi mai girma a masarautar..Bayan mutuwarsa da watanni ZAUFAJ NURANDEEN ya kawo da dokar duk wanda aka kama yana tsafi a cikin Masarautar bama masarauta ba duka nahiyar kasar Mali to hukuncin kisa ne..wanann lamari ya ƙara tado da tarzoma wanda sun ce bai isa ya hana su yin tsafi ba dan tun kaka da kakanni ake yin tsafi abun da suka tashi suka ga anayi kenan.

RANA DUBUحيث تعيش القصص. اكتشف الآن