★★

Da gudu ta shigo cikin gida sai haki take ta boye bayan UMMATI tana boye fuskarta sai sauke numfashi take da sauri da saur,i ajiye tsintsiyar hannunta UMMATI tayi tana maido da yarinyar gabanta tana cewa."Wa kuma kika takulo mana faɗa yau *AMATULLAH*.?" Turo baki gaba wanda aka kira da Ammatullah tayi sai kuma ta faɗa cikin ɗakin tana banka kofar ta rufe sai kuma ta ruga cikin bedroom tana boyewa bayan mirror sai haki take tana cinno baki ita ɗaya a ɗaki...Da Sallama suka shigo cikin gida riƙe da hannun wani yaro yana kuka ga jini duk ya wanke mashi fuska,ansa sallamarsu Ummati tayi tana salati tana cewa."Inalillahi wa'innalaihirajiun ni UMMATI yau naga abun da ya isheni bai ishi Allah ba, daman tsiyar da yarinyar nan ta kulla kenan,shiyasa ta shigo gidan nan a bujajen kamar wanda tayi gudun ceton rai.?" Cikin ɓacin rai yarinyar da ta kawo yaron take cewa.."gaskiya UMMATI idan har bakuyi ma AMATULLAH faɗa ba a cikin unguwar nan to kuyi kuka da kanku dan duk abin da ya faru da ita itace ta jama kanta ba wani ba, dan haka tun wuri kuyi ma yarinyar nan faɗa ya yaro yana cikin wasan shi daga yar'gardama ta shiga tsakaninsu sai ta fasa mashi kai ai ba dadi."Ita UMMATI tun da Afra ta fara maganar take kallonta tana mamakin yanda yarinyar take ƙoƙarin zaginta akan ƙaninta..Amman ai ba laifin ta bane daman ance ɗan kuka shike ja ma uwarshi jefa, kuma tasan halin AMATULLAH ba jin magana take ba da ace tana jin magana da ko kofar gida aka ce ta fita ba zata fita ba, furzar da numfashi tayi tana cewa."Dan Allah Afra kuyi hakuri tabbas ba'a kyauta maku ba kuma daga yau hakan ba zata sake faruwa ba in shaa Allah." Murguɗa baki AFRA tayi tana cewa"Sau kuna cewa hakan ba zata sake faruwa ba idan har Yarinyar can ta bugu yaran mutane?nidai gaskiya wannan ƙaran ba hakuri zanyi ba sai dai ansan yanda za'ayi dan ko sisi nan bani da ita, kuma Mama bata nan balle har ta bada kudin da za'a kai shi chemist ayi mashi wani abu kuma dai kinga yanda jininshi ke zuba karda ya ƙara case ya koma babba." Cewar Afra sai wani harare harare take tana juya ido kirirs take jira ta fara aunama Ummati zagi dan a wuya take..ita dai Ummati bata da ko sisi dan tun da ta tashi yau bata yi ido hutu da kudi ba ko Naira biyar bata maganinta balle kuma tasan a ƙarance ta ba Afra Naira 500 da zasuje chemist din Iliya ayi mashi dressing din wajen.Girgiza kai Ummati tayi tana sauke ajiyar zuciya a jere dan rasa abu da zata ce ma Afra tayi ta rasa ta ina zata fara da wannan masifar, ita dai har ta fara gajiya da halin AMATULLAH bata san ya zatayi ma yarinyar ba,yarinyar ce ba mai hanata sai Yayanta shine idan har ya ajiye ƙara yace karda ta ƙeta rashi ba zata ƙeta rashi ba har sai idan yace ta wuce kuwa kuma baya nan yana makaranta da yake scholarship ya samu yana cairo yana karatun psychology,tun da ya ƙetare ya bar ƙasar ya tafi cairo AMATULLAH bata sake jin maganar kowa ba suma kan su hakuri suke da ita.

Kamo hannun yaron tayi tana cewa.."shikenan Afra gashi Malam baya nan yana gona bai kai da dawowa ba,bari na wanko mashi fuskar a sama wajen gishiri a samu jinin ya tsaya, kafin Malan ya dawo sai ya bada kudin da zaku je chemist din ni nan wallahi Afra ban maganin ko tasi ai da tuni na bada dan ayi mashi dressing din wajen kiyi hakuri." Ita dai Afra bata ce komai sai ɗaga kai take tana hurawa,tafiya da yaron Ummati tayi ta wanke mashi kan cikin ikon Allah jinin ya daina zuba dan gishirin ta sama wajen ta dawo dashi tana shiga wani ɗaki ta ɗako tabarma ta baja masu tana cewa.."Ga waje ki zauna Afra tsayuwar ba dadi karda ƙafafunki suyi sanyi kuma..nan da dan anjima Malan zai shigo sai a kai shi chemist din a bashi magani." Hararar gefen ido Afra tayi mata tana magana ƙasa ƙasa tana cewa.."ai ko kwana zai yi ba inda zani ina nan zai dawo ya taddani, dan wallahi bata rotsa banza ba sai kudinku sunyi kuka,wata ila idan kun ga ana maku haka kunyi mata faɗa ta daina duk iskancin da take a unguwar nan tun da kudinku sun fara kuka dan ba wani kudi ne da ku ba balle." Girgiza kai kawai Ummati tayi tana cewa.."Allah ya ƙara baki hakuri Afra ai laifi akayi maki komai zakiyi ita ta janyo mamu Allah ya shirya mana dai." Ƙara kwabe baki kawai Afra tayi tana mai dauke kan ta ta maida gefe ,itama Ummati ida haɗa gawayin tayi ta ɗaura tukunya dan yi masu abincin dare,Amman ita kaɗai tasan irin bugun da zatayi ma Amatullah a yau dan ta gaji da rigimar da take janyo mata ina dalili shekara 10 ace har yanzu bata bar wasan banza da wofi ba a unguwa, aikuwa anyi na karshe indai ita ce ta haife ta.

RANA DUBUWhere stories live. Discover now