Tsaki Beel ya ja sannan yace "Adda Leemah kina ta baiwa banzan nan shawara abun da zai fi komai baki haushi FIK kamar tsoron yarinyar yake,ita ba kowa ba ba kuma yar kowa ba fa,and abun takaicin ko phone number din ta baya da"da sauri FIK ya katse shi don har da farko ya tsorata don Wlhy ya dau Beel fada wa Leemah zai yi kan fake relationship yake son yi da Sabeeha.


"Soul sis rabu da Beel na rasa why ya tsani Baiwar Allahn nan"dan kallon shi tayi sannan tace "da gaske ne tsoron ta kake ji?And wai ko phone number din ta baka da shi?"

A hankali yace "ni fa ba tsoron ta nake ji ba kawai yarinyar ce akwai cika ido,duk sanda na tashi don tunkaran ta sai na ji na kasa,and be rasa hadi da rashin kula maza da bata yi,Soul sis ko sau daya ba a taba ji ko an gan ta da na miji suna zance ba kullum tana tare da kawar ta ko mata ma ba shiga harkan su take ba balle maza,zan iya ce miki babu me contact din ta duk makarantar to taya zan samu?"

Dariya ta fashe da shi harda tafa hannu sanann tace "wonder shall never end!!My lord you are so great Wlhy wai yau FIK ne is in love ikon Allah,kai charm charm daman zan ga irin ranar nan,Awnnn my little cute brother is in love"ta kare tana Jan kumatun shi cike da farin ciki don daga ganin yanda ya damu yake bata labari ta tabbatar ba karamin so da kauna yake yi wa wanann budurwar tashi da ko sunan ta be fada mata ba.

Hannun ta ya zame daga face din shi "can you stop this pls am nor more a kid yanzu in su Rayyan suka fito ai sa mun dariya"ya kare yana hade rai,Dan dariya ta kuma sanann tace "finally yaron Mommah ya girma hankali ya zo gwama kayi ka shawo kan ta mu aurar da kai ko ka bar mana gari yayi sakat,but seriously ban dau akwai wanda zai tsorata shugaban Rocket gang ba"ta kare tana kunshe dariyar ta,hakan ne ya hasala shi tare da mike wa ya kalli su Beel "guys let's get going"

Da sauri ta riko hannun shi sanin da tayi sarai fushi yayi "zo abun ka Autan Mommah,ai ba mu gama magana ba za ka tafi", "yo Ai gani nayi kina neman bata mun rai don na zo gidan ki"ya kare yana hade rai,kai ta girgiza sannan tace "to sorry koma ka zauna ka ga irin zuciya da fushin da na gama maka magana kan dole ka rabu da su in ba haka ba matsala za kuyi ta samu da ita yarinyar,maganar number kuma ya ci ace by now ka samo number din ta coz sending cards and flowers kadai ba shine zai sanya ta so ka kamar yanda kake son ta ba,yana da kyau ta san wa ke tura mata sanann ta wayar ce za ka yi kokarin gina fadan ka tare da koyar mata yanda za ta so ka ta kaunace ka,and a iya tunani na tunda ka ce ba kowa take kula wa ba banda kawar ta,to dole through kawar ce za ka sami contact din ta,ka gane ai?"kai FAIZAAN ya gyada mata inda abun ku da yar uwa ta zauna wanann ranar har kusan yamma koya wa FIK dabarun da zai bi ya samu kan Sabeeha, tare da koya masa yanda Sabeeha za ta so shi take ,inda su Beel bakin ciki kamar ya kashe su,don suna da zuwa joint amman ya kashe musu,Wlhy da sun san abunda zai kawo su ke nan da ba su biyo shi ba,don to sun san sarai wanann bata lokaci ne tunda ba wai soyayyar gaske bane,inda shi kuwa ya nutsu sai aukin gyada kai za ka rantse da Allah a class yake yana daukan karatu,cikin zuciyar shi ko dadi kashe ni don kan shi da farko kusan kullewa yayi,and ya rasa ta yanda zai samu number din ta daman,don sam be kawo tunanin zuwa gurin Zuhra ba,saida ta tabbatar ta sanar da shi duk wasu abubuwan da ya dace sanann ya rungume ta tare da mata kiss a goshi,dariya tayi tare da ture shi

"Kai dai charm charm zan ga sanda za ka girma,make sure dai na ji feedback me dadi,and ya ci a kawo mun wanann in law din nawa na gan ta in bata kyauta na wahalar mun da kai da tayi,tare da breaking record don ita ce mace na farko da na fara jin kace kana so,duk da ma baka fada mun sunan ta ba"

Dan dariya yayi sanann yace "kar ki ji komai Soul sis zan kawo miki Barbie doll har gida ki gan ta"baki ta bude tana dariya "ah lalle dole na fada wa Mom ta fara shiri yaron ta ya samu mata"ta kare tana shiga daki, "aa Soul sis ba haka muka yi da ke ba,dadin abun kin san makomar me karya promise"daga dakin ta sa dariya sannan tayi shouting "ba dai ni kake hada wa da Ayatu Munafikun ba"be kai ga bata amsa ba ta fito,side hugging din shi tayi sanann ta shafa kan shi "kar ka ji komai yaron Mommah ba wanda zai ji maganar nan,it's our little secret so ba damuwa and in sha Allah zan taya ka da addua Allah ya sa ka shawo kan ta da wuri,make sure kayi duk abinda na fada maka and let's stay in touch in case akwai abunda ya shige maka duhu,my regard to Mom and Dad in ka koma gida"hugging din ta back yayi sanann ya ce "kar ki ji komai Soul sis ki ce da Little Monkeys din ki na tafi"kan shi ta kwade a lokacin da ya bude kofar mota sanann tace "thank god Monkeys din nan kamannin Fav uncle din su suka yi"ta kare tana dariya sanann ta mika wa Jawad rapper yan dubu dubu guda 3

 A SIMPLE DARE (WASA DA SO)Where stories live. Discover now