Ko kallon inda Mahaifin nasa yake beyi ba,haka yafara takawa rungume da ita saida yakaita mota  yabude mata tashiga ta zauna yarufe motan sannan yaxo yasami Faisal da Barrista Anwar da Janar ɗan Musa mahaifinsu Faisal sai Alh sunusi dama wasu da dake tsaye awajen suna ma Alh badamasin barta da Arziki,su Alhajj sunusi sunde shiga tsawun masu yimasa barkar ne amma zuciyar nan tasu tayi baƙi ƙirin dan bakin ciki  yanzun ma sun tsaya wajen ne gudun mutane su zargi wanibu akan,duba da yanda suke da Alhajin  amma Allah Allah suke su var wajen su kira Alkali da Barrista suji wai meyakawo canjin lokaci ɗaya su suna ganin sun gama komai inde haka ne akwai sauran aiki a gaban su.

Kalle shi tsawon shekaru da dama ya zauna ana juyashi saboda yariga ya damƙa musu yaruwar sa a hannun su sai yanda sukai da ita,baya da kataɓus sai abunda su sukace.

"Ammi ki dena faɗan haka ba kyau kinga hankalin mutane yafara yowa kanmu muje gida idan mun zauna sai muyi magana gyada masa kanta tayi shiya jata a mota saida yabude mata tashiga ta zauna ya rufo murfin motan sannan yaxo suka gaida dasu Barrista Anwar da Janar ɗan Musa mahaifin Faisal yana cewa dasu su haɗu a gida ko kallon inda Mahaifin sa yake tsaye beyi ba,shima din beyi tsamman zeyi masa  magana ba dan sanin halin sa da zuciyar sa.

Dukan su mota suka shiga suka dunguma zuwa gida Alhaji badamasi,Janar ɗan Musa yana nashi motar driven sa soja sanya da kakinsa yake jansa sai Barrista Anwar da shima yake tasa motan sai Alhaji badamasi dayake nashi motar shima drivern sane yake jansa Ammi kuwa tana tare da Ahmad a nashi motan,Barrista Anwar ne yakira Faisal ta waya yake sanar masa da su haɗa a gidan su Ahmad yanzu suma suna kan hanyarsu ta zuwa"lafiya de Barrista kode shari'ar batayi daɗi bane?Faisal ɗin ya tambaya duka a tare dan shi besamu shigowa Kotun ba saboda wani aiki dayashi masa kai.

"Lafiya amma ba lau ba Faisal dan wallahi shari'a kwata kwata batayi mana daɗi ba,saide kasan ance duk abunda Allah be ɓatashi ba baze taɓa ɓaci ba,badan Allah ba da yau saide kaji wani labarin tsabanin wannan ɗin.

"Allah mun gode maka Faisal ɗin yarinƙa cewa sai kuma yasake cewa naji kace mu haɗu gidan su Ahmad din lafiya de ko?ko Ahmad din yashigo ne?"eh yashigo dan Allah kazo karka ɓata lokaci dan yanzu haka muma can muka nufa harda Daddy ɗinka"Ok gani nan zuwa ya amsa masa da haka yana kashe wayan.

Tafiyane suke kowanne cikin su da abunda yake sakawa a ranshi,shi kansa Alhaji badamasin zuciyarsa tana masa rawa gami da hukuncin daya ɗaukama kansa na yin shiru baze faɗi sunan kowa cikin wayanda sune suka sakashi cikin wannan halin dayake ciki ba, dan ma sunan sa ɗaya yake neman ɓaci ta sanadin su,anƴa yama Matar sa abun so da kaunar sa adalcin kowa?anƴa yama ɗansa abun alfarin sa adalci kuwa?dalilin wannan abun ne yasaka yaran sa mata ke zaune a gida basa zuwa Makaranta saboda gudun tsangwama da suke fuskanta a can makarantar tasu,ɗan sa yake gudun sa,amma sufa dasuka sakashi a wannan hali?suna can zaune da matayen su da yaran su lafiya cikin farin ciki da walwala ko ze cigaba dayin shirun ne dan kare rayukan iyalan sa kaman yanda yafaɗa musu tun farko,idan yayi hakan yamusu iyalin sa adalci kuwa? tunda bayason yarasasu ko yasaka rayuwarsu cikin haɗari.

Hakade shi kaɗai yaringa magana da zuciyan sa har suka isa gida besan sun isa ba saida drivern sa yace"yallaɓa ai mun karaso tun tuni tukun ya ankara ya fito daga cikin motan jiki ba kwari daidai Fadwa da Ummu salma sun fito da gudu jin dirin motoci yasasu fitowa ganin Yayan sune suka fara yimasa Oyoyo suka juya suka gaishe da Janar  da barrista Anwar amma ko kallon inda mahaifinsu yake ba suyi ba suka juya suka shiga ciki.

A falo suka zazzauna Ammi ce ta saka kuka irin mai cin rannan kukane daya tasone tun daga ƙasan zuciyarta yaran suna tayata duk taurin zuciya irin ta Ahmad saida ya zubda ƙwalla shi ba komai yakeyi ma kukan sai dan ƙannen sa da maza ne ma da sauki amma dukkan su matane ya rayuwar su zata kasance? wane mijine ze yarda ya aure su ba tare da ya goranta musu halin Mahaifinsu da duniya take masa kallon maci amanan ƙasa dama al'umma dasuka yarda dashi suka damƙa rayukansu a hannusa suna amfana da ilimi da Allah ya bashi na haɗa magunguna.

Katse masa tunani Janar ɗan Musa yayi sanda ya kalli halin da yaran suke cikin da Mahaifiyar su,juyawa yayi ya kalli Alhaji badamasi daya dukar da kansa ƙasa yakasa ɗagowa ya kallisu,gyaran murya yayi yace"Ka dubi Allah ka kuma kalli halin da iyalan ka suke ciki ka bude baki kayi magana ta yanda zamu sami makami koda ƙanƙanine.

Be ɗago ya kalle shi ba, be kuma amsa masa ba, shiru yamasa still kansa a ƙasa"ba zeyi magana ba saboda yana ganin shirun sa kaman ceton a halin sa zeyi abunda besani ba shine koda kayi shirun ba barin nasu za suyi ba,duk kansu kusan a tare suka zubawa ƙofan shigowa falon ido inda zuke jiyo murya,sanya yake da farin yadi mai shegen kyau yayi shigan manyan kaya kansa sanye da hula damanga dukka ya manyanta amma kyaun nan tasa na nan ga wanda yamasa farin sani mutum ne mai cikan kamala da dattako kusan a tare suka miƙe tsaye nunashi Janar ɗan Musa yayi da yatsa yana cewa"dama baka mutu ba kana raye?

"Wanake gani haka kaman Ishaqu cewar Ammi tana mai bayyana mamakin ta.

"Dama dama kana raye ɗan jarida cewa Alhaji badamasi da dakyar ya iya haɗu maganan yayi ta saboda ɗaukewar da ƴawun bakinsa yayi lokaci ɗaya,Anwar da Ahmad kuwa ƴan kallo suka koma anan suna kallon yanda iyayen nasu.

Murmushin su na manya yayi yana cewa"ban mutu ba ina raye Janar"Amma ina kashiga tsawon wannan lokacin?yasake jeho masa da tambaya"hmm labarine mai tsawo Janar ɗan Musa zamuyi ta data baya.

"Zauna mana Ishaqu zama yayi suma dukan su zaman sukayi,kallo Alhaji badamasi yayi yana cewa dashi"shirun ka baze hanasu ai watar da mugun nufunsa kanku da Iyalinka ba,abu mafi sauki kawai shine kabude bakin ka ka faɗa musu wace alaqa ke tsakanin ka da Alhaji Sunusi dama Alh Shehu Alh Surajo rumbun kunɗi da Na Allah G.G.B....


ALLAH YASA MUDACE

AUREN WUCIN GADIWhere stories live. Discover now