"Auta kuyi da jiki dai mu samu mu kammala don ku samu ku kwanta kar gobe ku makara gurin zuwa makaranta"Umma ta fadi tana kallon su.

"Wlh Umma kin san yankan ilokan nan shi ke ci mun rai in banda haka da tuni mun gama,shi neman na halak wahala gare shi,Umma a hakan ma sai ki ga duk bayan wahalar nan ribar fa duk bata kai ta kawo ba"Sabeeha ta kare tana turo baki gaba,domin har ga Allah ta soma gajiya da sana'ar kayan madaran nan don ribar nata duk be kai ya kawo ba,ga yanda ake kara kudin abubuwa kullum na Allah in talaka be kai zuciyar shi nesa ba neman kudi gagarar shi za ta yi nan gaba wlhy.

Murmushi Umman tayi don ta san za a yi haka,sanann ta kalli Zuhra tace "ki fada wa kawar taki ta taba ganin inda mutum ya zamo wani ba tare da hakuri da jajircewa gurin neman na halak din sa ba?", "Kyalle ta Umma Wlhy magana kawai take nema ita da Allah ma ke son ta ta samu jarin ke nan,ince ni nan so nake na fara business din amman jari ya gagara haduwa,Wlhy in ta sa wasa sai na kwace ni na cigaba da yi"harara ta maka mata sanann tace "Umma kin ga ki daina sako Zuhra wlhh bata cika hankali ba fa"

"Eh Umma amman a rashin hankalin nawa da take fada ai na iya danne zuciya ta in an mun abu na boye fushi na ba wai don an watsa mun ruwa in tafi in je in wanke fuskan dan mutane da Mari tare da fada mishi maganganu ba" da sauri ta zaro ido tare da kiran sunan ta "Zuhra!!!"domin sam bata yi expecting abinda za ta fada ke nan ba,sam ta rasa me yasa Zuhra bata da hankali Wlhy,nan suka gama yi da ita kar ta bari Umma ta ji abinda ya faru ranar Friday a school tsakanin ta da Rocket gang amman saboda yawon magana saida ta fada.

"Auta wa kika mara?"shine tambayar da Umma tayi mata kai tsaye babu almaun wasa kuma a fuskan ta,saida ta maka wa Zuhra harara sannan ta turo baki gaba tace "Umma kar ki biye wa Zuhra"katse ta Umma tayi da fadin "ba wasa nake ba wa kika mara a makaranta ranar jumma'a kuma kika fada wa maganganu?"ganin tayi shiru tare da yin kasa da idanu ne ya  sanya ta kallon Zuhra tace "fada mun abinda ya faru Zuhra ina jin ki"kamar me jira kuwa nan ta kwashe labarin komai ta sanar wa Umma, sanann ta kare da fada wa Umma su waye yan Rocket Gang sannan kuma ta sanar da ita kan tsoro ne daman ya hana ta komawa Hostel ya sanya ta biyo Sabeeha tun ranar Friday din.

Ajiyar zuciya Umma ta sauke don rasa ma abin cewa tayi,sam ta rasa gane ina Sabeeha ta samo irin wanann banzan zuciyar da fushi kamar wata kuturwa,sam ita kam ba haka take ba,tana dai da fada amman bata da zafin hali da kuma bakin zuciya irin haka,haka ma Margayi Abban su,shi kam ma hayaniyar ce baki daya ba yi da shi,balle kuma Nawwara da ita ma ta koma ga Allah ita kam ma har cewa ake wai hakurin ta yayi yawa,sam za ta iya cewa Sabeeha ce ta fito daban gurin banzan zuciya da saurin fushin nan,saisa ba karamin fama ta ci da ita ba kafin ta samu ta daina tanka wa yan cikin gida in sun yi mata magana,don saida ta gwada mata bacin ran ta kafin ta daina,saidai in ta ga idanun Umman baya gurin to bata barin su in sun yi mata.

Ganin Umman tayi shiru bata ce komai bane ya sanya a sanyaye ta dago ta kalli Umman karaf suka
hada ido ashe tun tuni ita take kallo,duk sai ta ji kuma kunya ya kamata,da sauri ta maida kan ta kasa tana me aiyana irin dukan da za ta yi wa Zuhra in sun shiga daki,sam a rayuwa in akwai abinda ta tsana to fushin Umman ta ne,domin daga sanda tayi fushi da ita to hankalin ta in ya fi dubu sai ya fi na kowa tashi, domin Umma ita ce Uwa kuma Uban ta,so ko kusa bata kaunar ganin ta bata mata rai.

Cikin siririyar muryan ta tace "Umma kiyi hakuri ba zan sake ba"ta kare kamar za tayi kuka,dan kallon ta Umma tayi sannan tace "Sabeeha ni kam ina za ki kai wanann irin zuciya da saurin fushi irin naki?Daman abun da ya faru ke nan na tambaye ki kika ce da ni wai ke da Hajiya ne kuka samu sabani?Me yasa kika mun karya?"dan kallon Umma tayi tare da yin narai narai da idanu sanann tace "Umma tunani nayi in na fada miki abunda ya faru ran ki zai baci kiyi mun fada"

Dan dariyar takaici Umma tayi sanann tace "Au ashe ma ke da kan ki kin san abinda kika yi be dace ba,eh na ji an yi miki ba daidai ba amman me ya sa baki bi shawarar Zuhra kun yi tahowar ku gida?Babu malamai ne makarantar naku da ba za ki kai kara ba in ma ba za ki iya hakuri ba,tunda Zuhra tace da ni ba a sanin shi ya watsa maki ruwa ba,miye na Marin to??Akan me ya sa za ki zage su bayan kin mare shi,ban hana  ki zagin mutane ba?Ko kin mance Allah ke shiryar da bayin sa,ke ce miki aka yi rawa kika yi wa Ubangiji yayi ki me hankali da nutsuwa har kike iya tantance daidai da ba daidai ba"

 A SIMPLE DARE (WASA DA SO)Where stories live. Discover now