Ajiyar zuciya aka sauke daga cikin wayar har tana iya juyo wa sannnan cikin muryan damuwa tace "Goofy angel wai don Allah tun safe ina kika shiga ne ??I have been trying to reach you amman baki daukan wayar ki,kina lafiya dai ina?"ai bata san sanda ta fashe da kuka ba,a rude Zuhra tace "Hello can you hear me?talk to me,me ke damun ki,where are you fada mun?"ta fada duk a rude domin a duniya in akwai wace ta tsana ta gani cikin damuwa to Goofy angel din tane,don sun dade sosai tare zan
iya cewa ma kusan tare suka taso don tun yarinta suke kawance,sanadiyar su iyayen su mata ma suke kawance da juna,don a yanzu kam ma sun wuci kawaye sun koma yan uwa,don in ka gan su in ba farin sani kayi musu ba ba za ka ce ba yan uwa bane,coz har dan kamanni da juna suke,duk da ta fi Zuhran haske amman kun san ance wata shakuwar na sanya a fara kamanni da juna.

  "Ina ta gurin gate don Allah ki zo,and ki zo mun da babban hijab"daga haka ta kashe wayar,ba tare da bata lokaci ba kuwa Zuhra ta dauko big Hijab kamar yanda ta ce sanann ta fara tafiya ita kadai har ta iso guraren gate din,can ta hango bayan ta ya sanya ta nufi inda  ta ke zaune ita kadai hankalin ta tashe,domin rashin ganin ta a class yau ba karamin tayar mata da hankali yayi ba,don ita ce ma ta tashe ta kan tayi sallan asuba da wuri tayi wanka ta shirya,kar ma ta tsaya karya wa za ta taho musu da Dan wake,duk dan su samu su zauna a gaba sannan suyi submitting din assignment din Malam Jibril, duk zaton wlhy za ta zo theater din su ta samu ta riga ta zuwa,sai gashi ya gama ya fita babu ita babu labari,ta kira wayar ta ya kai sau 10 bata samun ta.

  "Wai Goofy angel me ya faru ne na ga kin zauna ke kadai a nan?kin san yanda kika tayar mun da hankali kuwa"ta kare tana bin ta da kallo,a hankali ta dago face din ta da ya baci da laka ta zuba su akan kawar nata cikin muryan kuka tace "Zuhra Malam Jibril har ya karbi assignment din ko?"

"Lord of Mercy  SABEEHA me ya samu fuska da jikin ki haka?"ta tambaye ta tana me zaro idanu, "hmm Wlhy Goofy angel wani dan iskan me mota ne ya wanke ni da ruwan laka,ya sanya tun dazu na zauna nan ban iya zuwa aji ba,kuma Wlhy Allah ya isa na ba zan yafe mishi sanya wa da yayi na rasa assignment din nan ba"ta kare tana hawaye.

"Ya isa haka yanzu dai wanke face din ki da ruwan cikin basket din nan,sai ki sanya Hijab din mu je hostel na baki kaya ki canza in ya so daga baya ma san ya za muyi da Mal Jabril duk ba zai gagara ba,shi kuma dan duniyar da ya watsa miki ruwan nan idon Zuhra idon shi domin babu me taba mun goofy angel dita ya kwana lafiya"nan ta wanke face din nata tare da sanya hijab din,Zuhra ta karbi basket din sanann suka shiga takowa zuwa hotel,inda ta shiga dan jan ta da hira ko wai zata yi cheering din ta up ganin yanda ranta duk ya gama baci.

Ko da suka isa hostel din straight black skirt da white top ta dauka daga akwatin Zuhran ta sanya,domin Zuhran na da daki a hostel ta kan zauna jifa jifa ko kuma ta koma gida,da tare suka so zaman hostel din ko dan samun saukin kashe kudin abun hawa,sai kuma ta fasa domin ganin za ta bar Umma ita kadai babu me rike mata aiki,don Umman su Zuhra kam akwai su kannan Zuhra da yayun ta za su na taya ta,inda ita kuma Umman ta su biyu kacal
ta haifa,daga ita sai ya yar ta Nawwara wace yanzu bata duniyar Allah ya amshi abun shi,dake kusan yanayin jikin nasu daya ne da Zuhran ya sanya kayan ya zauna mata daram,black hijab ta zira wanda ya kai mata har kasa kuwa sannan Zuhra ta ce ta bar mata kayan da ta cire gurin ta za ta wanke mata su,cikin jin dadi kuwa tace "za mu koma class ne?Ko mu zauna mu cinye Dan waken mu tukun na",dan dariya Zuhra tayi sanann tace "Dan waken mu?Dan wake na dai,yanzu dai taho mu je kar a shiga babu mu,kin ga kuma in an gama classes yau za mu je gurin Mal Jibril dole akan issue din assignment din ki",goshi Sabeeha ta dafe sanann tace "Goofy angel ni fa yau Wlhy in na koma gida ban ci wa wanda ya watsa mun ruwa mutunci ba yasin ina ji sai nayi zazzabi"dariya Zuhra ta fashe da shi sanann tace "Goofy wannan masifa taki ta soma yin yawa fa,yanzu dai wuce mu tafi,in kika je garin cin mutunci kika hadu da wanda ya fi mu kin ga ya ci uban mu ai ko"harara ta watsa wa Zuhran don ta rasa sam me yasa Zuhran ta fiye tsoro,a haka suka jero har zuwa ajin nasu,inda kuwa ba su dade da shiga ba Malamar da za ta dauke su ta shigo,nan aji yayi tsit aka shiga daukan karatu,sune basu samu kan su ba sai around 2,a gajiye duk suka fito,wasu mutane na raina wa course din Food and Nutrition ne ba tare da sanin dumbin wahala da wuyar da ke cikin ta ba,karatu dai duk wanda kace za ka yi shi to babu me sauki saidai ace wani ya fi wani wahala ,Allah ya saukaka kuma ya yassare mana baki daya kawai.

 A SIMPLE DARE (WASA DA SO)Where stories live. Discover now